Ali Usman Umar: Bitar Ɗafi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

BITAR ƊAFI A TASRIFIN HAUSA


Ali Usman Umar
Sashen Harsunan Nijeriya
Jami'ar Tarayya ta Lafia
+234 706 375 8416
alusumshariff@gmail.com


Gabatarwa

Harshen Hausa ɗaya ne daga cikin harsunan gidan Cadi na Yamma, yayin da kakan harsunan gidan Cadi ya kasance daga cikin harsuna ’yan tsatson Afroshiya. Harshen Hausa ya kasance mai halayyar ɗafi a cikin harsuna kumburau (Greenberg 1963). Sannan kuma harshe ne mai sauƙin koyo da saurin mamaya; kamar yadda yake ci gaba da zama harshen sadarwa da na ƙasa a Yammaci da wasu manyan biranen nahiyar Afrika (Schon 1862; Rufa’i 1977; Jaggar 2001).
Masana kimiyyar harshe da tasrifi a ƙirar kalma ta Hausa sun yi amannar cewa ɗafi muhimmin sinadari ne wajen samar da kalmomi mabambanta kuma masu dangantaka da juna, imam ta fuskar kumburi ko tsira ko ninki ko ma a wasu lokutan harɗantawa.
Masana tasrifin Hausa, irin su Bagari (1986) da Jinju (1981) da Bello (1981) da Newman (2000) da Jaggar (2001) Abubakar (2001) Fagge (2004) da Mamman (2011) da Sani (2011) da Al-Hassan (2011a, 2011b) da sauransu, sun haɗu a kan cewa ɗafi ko ɗofane ko liƙi ƙarin harafi ko haruffa ne da ake mannawa/haɗawa da ɓangarori dabandaban na saiwa ko tushe ko kalma don ƙera (samar da) wata sabuwar kalmar da take da kusanci da ta asali. A gefe guda za a yarda cewa dangantakar tsakanin ɗafi da saiwa/tushe, angantaka ce ta jini da tsoka.

Latsa nan ka Juyi Takarda


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub