Ali Usman Umar: Waiwaye Adon Tafiya

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Waiwaye Adon Tafiya: Tsokaci Kan Wasan
Kwaikwayon Hausa Aikatacce da Rubutacce


Ali Usman Umar
Sashen Harsunan Nijeriya
Jami'ar Tarayya ta Lafia
+234 706 375 8416
alusumshariff@gmail.com


Tsakure

Nau’o’in wasan kwaikwayon Hausa aikatacce da rubutacce ba su daɗe ba idan an kwatanta da rubutacciyar waƙa da rubutun zube. Cikin wannan bincike an bi diddigin tarihin samuwar aikatacce da rubutaccen wasan kwaikwayon Hausa. Kamar yadda binciken ya gano an fara samun rubutaccen was an kwaikwayon Hausa tun daga ayyukan Haji Ahmadu Kano (1898) da Rudolf Prietze (1924) ta hanyar amfani da labarum gargajiya da hikiyoyi.Yayin da, a gefe guda, aikatcce kuwa ya fara bayyana a ƙarshen gomiyar shekarar 1930 cikin wasannin da Malam Aminu Kano (1938) ya shisshirya da kuma na Abubakar Tunau (1943) ta hanyar dandamalantar da ƙirƙirarrun wasannin kwaikwayo. Haka kuma wannan takarda ta kawo nau’o’in ruhin aikatacce/rubutaccen wasan kwaikwayo guda tara (9), sannan aka ƙarƙare bitar wannan bincike da hanyoyi guda bakwai (7) waɗanda akan bi wajen samar da wasannin kwaikwayon Hausa.
Fitattun Kalmomi: wasan kwaikwayo, aikatacce, rubutacce, mashiryin wasa, marubucin wasa.

Latsa nan ka Juyi Takarda


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub