Wasan Kwaikwayon Hausa: Tushensa da Kashe-kashensa da kuma
Muhimmancinsa
Ali Usman Umar
Sashen Harsunan Nijeriya
Jami’ar Tarayya da ke Lafia
+234 706 375 8416
alusumshariff@gmail.com
Gabatarwa
Kalmar wasan kwaikwayo ta zo cikin harɗaɗɗen suna wato wasa da kuma kwaikwayo, wanɗanda suka haɗu suka tayar da wasan kwaikwayo. Kalmar wasa, a cewar Ƙamusun Hausa na CNHN (2006:470), na nufin aiwatar da wani abu don raha ko nishaɗi; ko kuma yin wani abu wanda ba gaske ba. Waɗannan ma’anoni da aka ayyana kalmar wasa na da matuƙar tasiri wajen bayyana ma’anar wasan kwaikwayo. Ita kuwa kalmar kwaikwayo, a cewar Ƙamusun Hausa na CNHN (2006:260), na nufin kwatanta yin wani abu da ya taɓa faruwa a zahiri; ko koyon wani abu da wani ya yi, ko yake yi. Saboda haka, idan aka haɗa kalmar ‘wasa’ da ‘kwaikwayo’ sun zama kalma guda ɗauke da ma’ana guda wato wasankwaikwayo. Masana fannin adabin Hausa Malumfashi (1984), Ɗangambo (1984), Ahmed (1985), Umar (1987), Yahaya da wasu (1992), Furniss (1996), Yar’aduwa (2007), da Umar (2014) sun yi bayanai masu gamsarwa a kan wasan kwaikwayo. A dunƙule, za mu iya bayyana wasan kwaikwayo da cewaaiwatar da kamancen halaye ne a wasance cikin raha da nishaɗi don kwatanta yadda wani lamari ya taɓa faruwa ko kuma yadda wani ya taɓa yin sa a zahiri. A nan, manufar wannan takarda ita ce, ta tattauna game da tushen wasan kwaikwayo a wurin Hausawa tare da kawo kashe-kashensa da muhimmancinsa idan aka yi duba da yadda wannan reshen adabi yake a fannin ilimin hikimomin al’ummar Hausawa.
Takarda/Muƙala
- Gudunmmawar Harshe...
- Matsayin Sana'o'i...
- Tasirin Mawaƙan Baka...
- Jiya da Yau...
- Gudunmawar Shafuka..
- Bitar Ma'anar Kalmar 'Hausa' ...
- 'Fathers' and 'Mothers' in Hausa...
- Friendship Requires Visits...
- Indigenous Languages...
- Dialectal Variation...
- Ƙasar Zamfara a Bakin Makaɗan Baka
- Waiwaye...
- Bitar Ɗafi
- Hausa Lexical
- Aspects of Meaning
- Hausa Noun-Based
- Gender and Language Use
- Wasan Kwaikwayon Hausa
- Infixes and Infixation
Kwamfuta
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin