Sarkin Dutse Gwajabo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Amadu Gwajabo 1799 – 1807


Gabatarwa

Sarki Amadu Gwajabo shi ne sarki na ishirin da takwas kuma sarki na ƙarshe a jerin sarakunan Dutse Hausawa. Shi ɗa ne ga sarkin Dutse Zubairu Tsohon Mutum (1737 - 1797). Ya gaji ɗan’uwansa sarkin Dutse Mamman Natatu (1797 – 1799). A zamaninsa Masarautar Dutse ta yi raunin sosai dangane da harkar tsaro.

Lokacin da Fulani masu jihadi suka iso ƙasar Dutse ya yi yunƙurin kare ƙasarsa, amma daga baya ya tsallake ya gudu. Ya fita ta ƙofa ta goma sha biyu inda ya yi hijira zuwa Kila. Bayan isarsa Kila ya turo wakilansa cewa su yi sulhu da dakarun jihadin cewa shi zai yi murabus ya basu mulki ba tare da yaƙi ba amma shi ma kuma za a ƙyale shi da shi da iyalansa. Wannan tayi nasa ya samu karɓuwa a wajen shugaban rundunar Fulani masu jihadi inda aka ƙyale shi ya ƙaura zuwa Jigawar Sarki, garin da bashi da nisa daga garin na Garu wanda yake a wajen ganuwar gari. A wannan gari ya rayu da shi da iyalansa har zuwa ƙarshen rayuwarsa.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub