Sarkin Dutse Habu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Habu Mai Ƙoƙiya 1658 – 1667


Gabatarwa

Sarki Habu Mai Ƙoƙiya shi ne sarkin Dutse na goma sha tara. Shi ɗa ne ga sarkin Dutse Yakubu  Nabukka (1632 – 1643).

A zamaninsa ya samu nasarar ƙulla yarjejeniyar daina yaƙi da kuma shata iyaka tsakaninsa da ƙasar Guddiri daga yamma da shi. Haka nan kuma ya yi yunƙurin samun wannan yarjejeniya tsakaninsa da Masarautar Kano amma abin ya ci tura. Idan muka duba kenan ya yi zamani da sarakunan Kano biyu, akwai na farko Muhammadu Kukuna (1652 – 1660), sai kuma Bawa Ɗan Muhammadu Kukuna (1660 – 1670).

Sarki Habu Mai Ƙoƙiya ya mulki Masarautar Dutse tsawon shekaru tara wanda daga baya ya yi murabus daga mulkin Masarautar Dutse a shekarar 1667 sakamakon matsalar gani da ya samu.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub