Sarkin Dutse Jawandu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Jawandu-Dogo 1584 – 1609


Gabatarwa

Sarki Jawandu-Dogo shi ne sarkin Dutse na goma sha huɗu. Shi ɗa ne ga marigayin sarki Mantau Jarmai. Ya gaji mahaifinsa wajen jarumta, saboda haka bayan hawansa karagar mulki sai ya ci gaba da faɗaɗa masarautar ta Dutse inda shi kuma ya samu nasarar faɗaɗa sashen Kudu da Yamma na masarautar. Garuruwan da suka yarda suka bishi ta hanyar sulhu akwai Madobi, Shimadara, Kuɗai, Malamawa, Ruru, Jaudi, Jidawa, Warwaɗe, Sakwaya, da kuma Fuguma (Fuguma yanzu tana cikin ƙaramar hukumar Takai ta Jahar Kano).

Sarki Jawandu-Dogo ya zamo mutum mai son kaɗaitaka, wannan dalili ne ma ya saka shi barin harkokin tafiyar da mulki a hannun ɗan’uwansa mai suna Barwa Timbale. Ya zamo mafi yawan lokutansa yana kai-komo tsakanin Dutsen Asarki yana hulɗarsa da iskokai. Wannan ta sabauta masa samun matsalar da bama ya iya tantance tsakanin abubuwa na zahiri da shifcin Gizo. Wannan ta sabauta tuɓe shi daga gadon mulki.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub