Hakimin Dutse Muhammad Sanusi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Muhammadu Sanusi Ɗan Bello 1983 – 1995


Gabatarwa

Sarki Muhammadu Sanusi Ɗan Bello Bayallige. An haife shi a watan Nuwamba na shekarar 1913. Ya fito daga zuriyar Sarkin Dutse Sulemanu Ɗan Musa (1849 – 1868). Shi mutumin kirki ne wanda ke son jama’arsa ta samu ci gaba. Ya samu gogewa a harkar sarauta ƙwarai da gaske, kasantuwarsa mutumin da ya fara sarauta tun daga dagaci, ya zama hakimi, sannan daga ƙarshe ya zama sarkin Yanka mai daraja ta ɗaya.

Ya fara shiga harkar mulki a matsayin Makaman Dutse, dagacin Galamawa a shekarar 1937 – 1944. Daga baya aka yi masa Sarkin Yaƙin Dutse kuma Dagacin ‘Yargaba daga 1944 – 1935. Sannan aka sake yi masa Dagacin Gurduɓa a shekarar 1953 – 1981. A shekarar 1981 aka tursasa masa yin murabus bisa umarnin Gwamnan Kano na wancan zamani, marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, wanda ya bayar da umarnin sauke duk wani dagacin da aka san yana marawa jama’iyyar siyasa ta NPN baya.

Bayan ƙarewar wa’adin mulkin gwamnatin marigayi Alhaji Abubakar Rimi, a ranar 31 ga watan Oktoba na shekarar 1983, Sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero (1963 - 2014), ya yi masa naɗin da ya maida shi hakimin Dutse na tara kuma na ƙarshe. Sannan kuma sarki na arba’in a jerin sarakunan Dutse, kuma sarki na goma sha biyu a sarakunan Fulani.

Ya riƙe wannan muƙami na hakimi har zuwa shekarar 1991, shekarar da ta kawo ƙarshen kwan-gaba-kwan-baya da masarautar ta Dutse ta riƙa samu a harkar sarauta. Wanda bayan samar da sabuwar gwamnatin jahar Jigawa da Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ya yi, da kuma saka Dutse a matsayin helikwatar mulkin jahar, sai aka sake ɗaukaka darajar masarautar ta Dutse zuwa masarauta mai daraja ta ɗaya wacce ke da yankunan hakimai guda bakwai da suka haɗa da Dutsen ita kanta, Kiyawa, Birnin-Kudu, Gwaram, Buji, Miga, da Jahun. Sannan kuma Sarki Muhammadu Sanusi ya tashi daga hakimi zuwa Sarki mai daraja ta ɗaya.

Zamaninsa shi ne lokacin da ya ɗora Dutse a tafarkin ci gaba. Aka samu ruwan sha mai inganci, hasken wutar lantarki, manyan tituna, da sauran abubuwan da lissafo su ke da kamar wuya, gurguwa da auren nesa.

Sarki Muhammadu Sanusi ya rasu a ranar 29 ga watan Nuwamba na shekarar 1995, bayan ‘yar gajeruwar rashin lafiya a fadarsa da ke Garu. An kuma binne shi bisa karantarwar addinin Musulunci a gidansa da ke Shuwarin da misalin karfe 3 na yammacin ranar da ya rasu.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub