Sarkin Dutse Salihu II

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Salihu Ɗan Ibrahim II 1893 – 1894


Gabatarwa

Sarki Salihu ɗan Ibrahin II Bajallige, shi ne sarki na talatin da biyar a jerin sarakunan Dutse, sannan kuma sarki na bakwai daga cikin sarakunan Fulani a Dutse. Shi ɗa ne ga Sarki Ibrahim Ɗan Salihu (1868 – 1884). Sabon sarkin Kano Tukur Ɗan Muhammadu Bello (1893 - 1894), shi ya naɗa shi a matsayin sabon sarkin Dutse.

Wannan naɗi na wani sabon sarkin daga zuriyar Jalligawa, ya sake fusata Yalligawa har ta kai ga sun yanke ƙauna daga gidan sarautar Kano. A saboda wannan dalili sai suka yi wa sabon sarki tawaye kamar yadda shi ma sabon sarkin Kanon yake fama da tasa rigimar tawayen daga gidansu; wato ‘ya’yan Abdullahi Ɗan Dabo (1585 – 1882) da suka ƙi yi wa sabon sarki Tukur Ɗan Muhammadu Bello (1893 – 1894) caffa (Northern Nigerian Publishing Company, 1970).

Faruwar wannan al’amari ta kai ga haɗuwar waɗannan masu tawaye guri guda. Wato ‘yan tawayen Kano, da kuma ‘yan tawayen Dutse, da kuma gayyato sarkin Haɗeja Muhammadu da kuma sarkin Gumel Habu da shi Yusufu ya yi dan su taya shi yaƙar sabon sarkin na Kano, amma shi sarkin Haɗeja Muhammadu bai shiga yaƙin ba yana mai cewa, tun da dai Gumel tana ciki, to shi ba zai shiga ba, saboda ba za su haɗu waje guda da Gumel ba (Northern Nigerian Publishing Company, 1970). A garin Takai aka ƙulla yarjejeniyar tallafawa juna wajen yaƙar sarakunan da ke kan karagar mulki tsakanin Yusuf Galadiman Kano da kuma Ibrahim ɗan Musa daga Dutse. Shi kuma Ibrahim Ɗan Musa, shi ya jagoranci wannan runduna.

Bayan da rundunarsu ta haɗaka ta yaƙi Gaya, sai shi Ibrahim Ɗan Musa ya buƙaci da a kaiwa sarkin Dutse Salihu Ɗan Ibrahim II hari. Jin daɗin irin rawar da shi Ibrahim ɗan Musa ya taka a yaƙin Gaya, ta saka shi Galadiman Kano Yusuf ya naɗa Ibrahim Ɗan Musa a matsayin kangararren sarkin Dutse tun kafin a kai ga kammala cin nasara a kan Dutse. An yi wannan naɗi a cikin watan Agusta na shekarar 1894.

Da aka shata dagar ƙarshe a garin Karnaya, sai shi Sarkin Dutse Salihu ɗan Ibrahim II, ya gudu da shi da jama’asa zuwa Haɗejiya gudun hijira da kuma neman taimako. Saboda haka sai sarkin Haɗejiya Muhammadu ya bashi mafaka.

Daga nan kuma sai Ibrahim Ɗan Musa ya zama sabon sarkin Dutse. Wannan sabon sauyi da aka samu na naɗa Ibrahim Bayallige a matsayin sabon sarkin Dutse kuma ya sake rura wutar gabar da ke tsakanin waɗannan gidajen sarauta guda biyu.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub