Tsarin Sauti: Adadin Baƙaƙe

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tsarin Sauti: Adadin Baƙaƙe


Gabatarwa

Akwai baƙaƙen Hausa guda talatin da biyu a fagen Nazarin Sauti a Daidaitacciyar Hausa. Akwai baƙaƙe 24 daga ciki sauƙaƙa, 8 kuma masu aure ko masu goyo. Ga su kamar haka:

Sauƙaƙan Baƙaƙe

 1. /b/ ta cikin baba.
 2. /Φ/ ta cikin fata.
 3. /ɓ/ ta cikin taɓarya.
 4. /m/ ta cikin mama.
 5. /n/ ta cikin nono. Tana kuma da ‘ya’ya guda biyu; /ɲ/ alamar furucin n, wacce take zuwa a cikin hanya da kuma /ŋ/, alamar furucin n, wacce take zuwa a cikin can.
 6. /ʤ/ alamar furuncin j kamar a cikin jaki
 7. /t/ ta cikin tafi.
 8. /d/ ta cikin dodo.
 9. /ɗ/ ta cikin ɗaki.
 10. /l/ ta cikin lalo.
 11. /s/ ta cikin sara.
 12. /z/ ta cikin zaki.
 13. /s’/ ta cikin tsutsa.
 14. /r/ ta cikin rago.
 15. /ɽ/ ko /ȓ/ alama ce ta furucin /r/, kamar a cikin randa.
 16. /ʃ/ alamar furucin sh, kamar a cikin shayi.
 17. /tʃ/ alama ce ta furucin /c/, kamar a cikin caca.
 18. /j/ alamar furucin y kamar a cikin yaro.
 19. /k/ ta cikin kare.
 20. /ƙ/ ta cikin ƙoƙo.
 21. /g/ ta cikin goro.
 22. /w/ ta cikin wasa.
 23. /h/ ta cikin haihuwa.
 24. /Ɂ/ alamar furucin Hamza (‘), wacce take zuwa a cikin ‘ya’ya.

Baƙaƙe Masu Goyo

 1. /kw/ ta cikin kwakwa.
 2. /ƙw/ ta cikin ƙwai.
 3. /gw/ ta cikin agwagwa.
 4. /kj/ alamar furucin /ky/, kamar a cikin kyanwa.
 5. /ƙj/ alamar furucin /ƙy/, kamar a cikin ƙyasbi.
 6. /gj/ alamar furucin /gy/, kamar a cikin gyara.
 7. /Ɂj/ alamar furucin /‘y/, kamar a cikin ‘yanci.
 8. /Φj/ alamar furucin /fy/, kamar a cikin fyaɗe.

Manazarta:


Junaidu I. da ‘Yar’aduwa T.M (Babu Shekara). Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Nigeria.

Sani M.A.Z. (2007). Tsarin Sauti Da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Sani M.A.Z., Muhammad A. Da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Langugae Don Masu Rubuta Jarabawar WASC da SSCE. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M da ‘Yar’aduwa T.M. (2006). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub