Tsarin Sauti: Adadin Wasula

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tsarin Sauti: Adadin Wasula


Gabatarwa

A fagen Nazarin Tsarin Sautin Hausa, akwai adadin wasula guda goma sha uku. Daga cikinsu akwai guda goma gwauraye, waɗanda suka sake kasuwa zuwa dogaye da kuma gajeru duka guda biyar-biyar kamar haka:

Dogayen Wassula

  1. /ii/ kamar a cikin kiifii.
  2. /ee/ kamar a cikin bee.
  3. /aa/ kamar a cikin raa
  4. /oo/ kamar a cikin zoomoo.
  5. /uu/ kamar a cikin guuruu.

Gajerun wassula

  1. /a/ kamar a cikin bara.
  2. /e/ kamar a cikin mace.
  3. /i/ kamar a cikin abinci.
  4. /o/ kamar a cikin kaɗo.
  5. /u/ kamar a cikin huɗu.

Masu Aure

Guda uku ne:

  1. /ai/ kamar a cikin aiki.
  2. /au/ kamar a cikin sauri.
  3. /ui/ kamar a cikin guiwa.

Manazarta:


Junaidu I. da ‘Yar’aduwa T.M (Babu Shekara). Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Nigeria.

Sani M.A.Z. (2007). Tsarin Sauti Da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Sani M.A.Z., Muhammad A. Da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Langugae Don Masu Rubuta Jarabawar WASC da SSCE. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M da ‘Yar’aduwa T.M. (2006). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub