Hausa Al'adu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Al'adun a Ƙasar Hausa


Gabatarwa

Al’ada, kalma ce da aka aro ta daga Larabci aka mayar da ita ‘yar’gida a Hausa. Ma’anarta ita ce sababben abu, wato abin da aka saba da shi kenan. Shi kuwa Farfesa Ɗangambo (1984), cewa ya yi, “Al’ada ita ce abin da aka saba yi yau-da-gobe”.

Wannan rubutu zai duba al’ada ne ta fuskacin bukukuwan Hausawa. Wato idan aka ce al’ada da kuma biki, wasu abubuwa ne da ke cakuةùe da juna. A lokutan gudanar da wasu al’adun ake samu biki yana shigowa ciki. Misali, idan aka yi maganar al’ada a Ƙasar Hausa za a samu aure a ciki, haka nan kuma idan aka yi maganar biki, to za a samu aure a ciki. Kenan, biki ya shiga cikin al’ada. Misali, a lokacin al’adar zanen suna, akan yi biki.

Saboda haka a wannan rubutun idan aka ce al’ada, ana nufin tsura ko zalla ko gundarin abubuwan da aka saba yi a Ƙasar Hausa idan wata hidima ta tashi kamar suna da sauransu.

Al’ada ta shafi kusan dukkanin rayuwar Bahaushe. Idan aka lura sosai da hidindimun da ake yi a Ƙasar Hausa, za a taras cewa kowane ةùaya akwai yadda ake yinsa, da kuma lokacin da ake yinsa, to wannan shi ne al'ada.

Kenan, a taƙaice ana iya cewa, al’ada ita ce abin da aka saba yi yau-da-kullum wajen gudanarwa ko yin abubuwa, kuma ta shafi abubuwan da ake yi yau-da-kullum. A Ƙasar Hausa akwai al’adu iri-iri da suka haةùa da aure, zanen suna, da sauransu.

Manazarta:


ئèangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maةùaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Zarruئ└ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don ئ┐ananan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub