Tsarin Sauti: Harrufa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tsarin Sauti: Adadin Harrufa


Gabatarwa

Dangane da abin da ya shafi sauti, Daidaitacciyar Hausa tana da adadin harrufan da ake amfani da su. Idan kuma aka ce harrufa a nan, to ana nufin haɗakar baƙaƙe da wasula waɗanda kowane ɗaya daga cikinsu ƙwayar sauti ce.

A dunƙule, Hausa tana da harrufa; wato sautuka guda 44, talatin da biyu daga ciki baƙaƙe, goma sha biyu kuma wassula kamar yadda ya zo a Yahaya, Zariya, Gusau da kuma ‘Yar’aduwa (2006).

Amma Sani (2007), ya ce akwai ƙwayoyin sauti a Hausa guda 45, talatin da biyu baƙaƙe, goma sha uku kuma wassula. Ga jerin sautukan baƙaƙen Hausa guda 32. 24 daga ciki sauƙaƙa, 8 kuma masu aure ko masu goyo.

Manazarta:


Junaidu I. da ‘Yar’aduwa T.M (Babu Shekara). Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Nigeria.

Sani M.A.Z. (2007). Tsarin Sauti Da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Sani M.A.Z., Muhammad A. Da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Langugae Don Masu Rubuta Jarabawar WASC da SSCE. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M da ‘Yar’aduwa T.M. (2006). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub