Hausa Kacici-Kacici

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kacici-Kacici


Gabatarwa

Kacici-kacici, reshe ne na sarrafa harshe wanda yara kan yi ta hanyar tambaya da amsa. Amma Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), sun fassara shi a matsayin “shiryayyun tambayoyi ne da kan zo a gajarce na hikima masu ɗaukar fasali ayyananne da ke buƙatar bayar da amsoshi”. Shi kuwa Farfesa Ɗangambo (1984), ya ayyana shi a matsayin nau’in tatsuniya mai tambaya da amsa.

Shi kacici-kacici ana yinsa ne a lokaci ɗaya da tatsuniya wanda wasu kan buɗe hirar da shi, sannan kuma tatsuniyoyi su biyo baya, a wasu lokutan kuma yakan zo a ƙarshe, wanda idan an ɗauki kacici-kacici mai kama da waƙa ne, ana zuwa ƙarshensa kowa sai ya watse.

Wannan nau’i na sarrafa harshe, yana da matuƙar muhimmaci ga yara. Saboda yana taimakawa yara wajen kaifafa tunaninsu. Sannan kuma yana koyawa yara iya magana ta fuskar bayar da amsar da ta dace ga kowace tambaya. Haka nan yana koya wa yara yin tunani kafin yanke hukunci, saboda a wasu lokutan sai an yi nazari kafin a iya bayar da amsar tambayar, inda kuma ba amsa sai a ce an ba da gari. Wato an sallama ba za a iya ba, a nan kuma sai shi mai tambayar ya faɗi amsa, wanda wannan yana koyar da yara sanin duk abin da ya gagari mutum, to za a iya samun mai yi.

Ana yin kacici-kacici ne ta hanyar tambaya da amsa. Mutane biyu, ko fiye da haka ne ke yinsa. Ɗaya na tambaya saura kuma suna amsawa. A duk lokacin da za yi kacici-kacici akan fara tambayar da cewa, Ƙulun ƙulu fita. Wannan kamar ita ce taken kacici-kacici, duk wanda ya ji wannan amo, sai ya nufi gurin, idan kuma ba mai sha'awar wannan wasan ba ne, sai ya kama gabansa.

Nau'ukan Kacici-Kacici

Kacici-kacici iri-iri ne, daga ciki akwai:

Nau’i na farko:

Tambaya:   Ƙulun ƙulu fita.
Amsa:         Gauta
Tambaya:   Ta ƙanda ba ƙashi ba.
Amsa:         Kanwa.
Tambaya:   ‘yan matan gidanmu sun raba mana goro
Amsa:         Kashin awaki.
Tambaya:   Baba na ɗaka gemun na waje.
Amsa:         Hayaƙi.
Tambata:    Daga nesa na jiyo muryar ƙawata.
Amsa:         Ganga
A wannan salo na kacici-kacici, yara sukan taru ne a wani waje, sai kuma a samu mai tambaya ya tsaya daga gefe guda, a bayan mai tambayar sai a samu wata bishiya ko wani abu a ce ita ce gurin sha; kamar tudun mun tsira kenan. To idan ana cikin wannan tambaya ana bayar da amsa, duk wanda ya faɗi wani abu wanda ba amsar tambayar ba ce, sai a rufe shi da duka shi kuma ya ruga da gudu har sai ya je ya taɓa wannan bishiya sannan a ƙyale shi. Wato ya sha kenan.

Nau’i na biyu:

A wannan nau’in kuma za a riƙa ambato sunayen wasu abubuwa ne waɗanda suke da wata siffa, hali, ko ɗabi’a iri ɗaya, sai masu bada amsa sun sakankance sai a sako bare kuma a ciki. Duk sai a yi shiru, to wanda bai san dawar garin ba yana bayar da wannan amsa, sai a haushi da tuma, har sai ya je ya sha tukuna. Misali:
Tambaya:   Bibita da jini
Amsa:         Tanjam
Tambaya:   Akuya da jini
Amsa:         Tanjama
Tambaya:   Jaki da jini
Amsa:         Tanjama
Tambaya:   Mutum da jini
Amsa:         Tanjama
Tambaya:   Doki da jini
Amsa:         Tanjama
Tambaya:   Kaza da jini
Amsa:         Tanjama
Tambaya:   Bishiya da jini
Amsa:         Babu
To a wannan amsa ta ƙarshe duk wanda ya ce tanjam, ya kauce hanya sai duka.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur, Kano – Nigeria.

Yahaya I. Y. (1971). Tatsuniyoyi da Wasanni, Littafi Na Ɗaya. Oxford University Press.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub