Nahawun Hausa: Jimla

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Aikatau


Gabatarwa

Dukkan wata kalma da idan aka ambata ta take nuni zuwa ga faruwar wani aiki, a cikin wani keɓantaccen lokaci, to, sunanta aikatau. Aikatau ajin kalmomi ne mai faɗin gaske. Masana harshen Hausa sun tabbatar da cewa kalmomin aikatau sun fi kowane ajin kalmomin Hausa yawa.

Manufar wannan rubutu ita ce bayyanawa mai karatu ma’anar aikatau, ire-irensa, da kuma lokuta game da aikatau.

Ma’anar Aikatau

Aikatau, su ne kalmomin da ke nuni zuwa ga wani aiki idan aka furta su. wasu kuma suka ce, aikatau su ne kalmomin da ke maganar aiki a cikin jimla. Kalmomi irin su ci, sha, gudu, zama, kiɗa, girki, da sauransun dukkansu aikatau ne.

Misali, Ado ya ci abinci. Laraba ta sha ruwa, sun zauna, yana kiɗa, tana girki, jimloli ne waɗanda ke ɗauke da kalmomin aikatau ɗin da aka ambata a sama.

Rabe-Raben Aikatau

A Hausance, sun karkasa kalmomin aikatau bisa la’akari da aikin da ta ke yi a cikin jimla. Akwai So-Karɓau da kuma Ƙi-Karɓau.

Aikatau So-Karɓau

Shi ne aikin da ke faɗawa kan wani abu. Wato idan aka aikata aikin, za a taras cewa a kan wani abu aka aiwatar da shi. Lura da misalan Ado ya ci abinci, da kuma Laraba ta sha ruwa. Ado da ya aikata aikin ci, sai aikin ya faɗa kan abinci. Wato shi abinci shi aka ci, saboda haka sakamakon aikin a kansa ya ƙare. Haka nan ma Laraba da ta sha ruwa, sai ya zama ruwa shi aka shanye. Saboda haka, ci da sha a nan sun zama aikatau so-karɓau. Ga wasu misalan:

 1. Basiru ya nome gonarsa.
 2. Bala yana karanta littafi.
 3. Gobe zan hau mota.
 4. Jummai takan share ɗakinta.
 5. Mota ta buge kare.

Aikatau Ƙi-Karɓau

Aikatau ƙi-karɓau shi ne aikin da baya faɗawa kan komai a cikin jimla. Lura da waɗannan misalai: Yara suna wasa. Binta tana shara. A cikin waɗannan jimloli mun fahimci cewa yara sun aikata wasa, amma ba wanda aikin ya faɗa a kansa. Haka nana a jimla ta biyu, Binta ta yi shara, amma ba wani abu da ya karɓi wannan sharar. Saboda haka wasa, da kuma shara a nan, sun zama aikatau ƙi-karɓau. Ga wasu misalan:

 1. Ɗanmakaranta ya yi karatu.
 2. Maryam takan yi barci.
 3. Shehu ya gudu.
 4. Ado ya yi wanka.
 5. Zahara za ta yi girki.

Lokuta

Lokuta a nan na nufin lokacin da aka wanzar da aiki a cikinsa, wanda ka iya zama an aikata aikin, ko kuma ana aikatawa, ko kuma za a aikata. Wato kamar a ce ɗazu, da yanzu da an jima. Masana fannin Hausa sun karkasa lokacin aikatau zuwa lokuta guda bakwai:

 1. Shuɗaɗɗen lokaci I.
 2. Shuɗaɗɗen lokaci II.
 3. Sababben lokaci.
 4. Lokacin yanzu I.
 5. Lokacin yanzu II.
 6. Lokaci mai zuwa I.
 7. Lokaci mai zuwa II.

Shuɗaɗɗen lokaci I

Shi ne lokacin da ya riga ya wuce. Wannan lokaci yana nuni da aikin da aka riga aka kammala shi. Wakilan suna na, ka, ya, ta, kin, sun, mun, da kun, su suke gabatarsa. Wato ana gane shi idan ɗaya daga cikin waɗannan kalmomin suka zo a farko, sannan shi kuma aikatau ɗin ya biyo bayansu. Misali:

 1. Na wanke rigata.
 2. Ka ci jarabawa.
 3. Ya sayi sabuwar mota.
 4. Ta gaishe da maras lafiya.
 5. Kin karanta littafi.
 6. Sun ziyarci malaminsu.
 7. Mun ƙarawa junanmu sani.
 8. Kun cika alƙawari.

Shuɗaɗɗen lokaci II

Lokaci ne da yake nuni da faruwar wani aiki a wani lokaci a baya. Kalmomin na, ta, ya, kuka, suka, aka da muka su ke gabatarsa, tare da kalmomin dangantaka, wato mahaɗai; wanda, waɗanda, da kuma wadda. Misali:

 1. Ni ne wanda na zo jiya.
 2. Mariya ce wadda ta sayo maka zuma.
 3. Adamu wanda ya gasa maka nama.
 4. Ku ne waɗanda kuka nome gonar Idi?
 5. Su ne waɗanda suka ci jarabawa.
 6. Su ne waɗanda ka ziyarta bara.
 7. Mu ne waɗanda muka kai masa kayansa.

Sababben Lokaci

Shi ne lokacin da yake nuni ga aikin da aka saba yi. Kalmar kan ce ka bayyana shi. Misali:

 1. Na kan ci ɗanwake da rana.
 2. Ta kan share gidanta da safe.
 3. Na san ka kan faɗi gaskiya.
 4. Mu kan biya kuɗin makaranta shekara-shekara.
 5. Ku kan taimaki Alhaji da aikin gona.
 6. Su kan ziyarci malaminsu.

Lokaci na Gaba I

Shi ne lokacin da yake nuni zuwa ga aikin da ake da tabbacin aiwatar da shi a wani lokaci mai zuwa. Kalmar za ce ke bayyana shi. Misali:

 1. Za na zo gidanku.
 2. Za su je makaranta.
 3. Za ya kwanta barci.
 4. Za mu je kasuwa.
 5. Za su hau mota.

Lokaci na Gaba na II

Shi ne lokacin da ya ke nuni ga aikin da za a aikata a lokaci mai zuwa a gaba, amma akwai kokwanto wajen aikata aikin. Wato za a aikata aikin a gaba amma ba tabbas a cikin yin aikin. Kalmomi masu karin sauti mai faɗowa su ke bayyana shi. Misali:

 1. Na ziyarce ku.
 2. Sa biya kuɗin makaranta.
 3. Ka daina yin haka.
 4. Ma je gurin taron.
 5. Larai ta biya kuɗin katin.

Lokacin da Ake Ciki na I

Lokaci ne da ya ke nuni ga aikin da ake cikin yi. Wato aikin da an riga an fara aiwatar da shi amma ba a kai ga kammala shi ba. Kalmomin ina, kana, tana, kina, suna, kuna, muna, da sauransu, su suke bayyana shi. Misali:

 1. Ina karanta littafi.
 2. Kana rubuta wasiƙa.
 3. Tana karantar da yara.
 4. Suna gyara mota.
 5. Muna tattaunawa.

Lokacin da Ake Ciki na II

Lokaci ne da ya ke nuni zuwa ga aikin da ke tsaka da faruwa, ba a riga an kammala shi ba a lokacin da ake maganar. Kalmar ke, ita take bayyana shi. Misali:

 1. Bala ne yake kaɗa ganga.
 2. Ni nake magana da kai.
 3. Su ne suke damun mu da surutu.
 4. Ita ce take koyar da yara.
 5. Shi ne yake tuƙa motar.

A daidai wannan gaɓar mun fahimci cewa aikatau shi ne dukkan wata kalma da take nuni zuwa ga faruwar wani aiki a cikin jimla. Aikatau kala biyu ne; akwai so-karɓau wanda ake samun aikin da aka aikata ya faɗa kan wani abu, da kuma ƙi-karɓau, wanda shi aikin da aka aiwatar a cikin jimla baya faɗawa kan kan komai. Lokacin da aka gudanar da aiki a cikinsa shi ne a Hausa ake kiransa da lokaci. Akwai lokuta guda bakwai a Hausa wanda kowane ke nuni da faruwar wani aiki a cikinsa.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo da Koyarwa. Irshad Islamic Publication Cetre LTD. 31, Adelabu Street, Surulere, Lagos-Najeriya.

Jinju M.H. (1981). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company Limited.

Sani M.A.Z. (1999). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Sani M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub