Nahawun Hausa: Jimla

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Azuzuwan Kalmomi


Gabatarwa

A fannin nahawun Hausa, an rarraba dukkanin kalmomin Hausa zuwa aji-aji dan samun sauƙin yin hulɗa da kalmomin. Wannan aji-aji da aka yi musu a wasu lokutan ana kiransa da azuzuwan nahawu.

Dukkan wata kalma Bahaushiya, da ma baƙuwar kalmar da aka Hausantar da ita, an sama mata aji daidai da irin aikin da take yi.
Azuzuwan Kalmomi

Akwai saɓani a tsakanin masana fannin Hausa dangane da suna da kuma karkasa wannan darasi na azuzuwan kalmomi. Wasu daga cikinsu sun kira shi da suna Azuzuwan Kalmomi, wasu kuma suka ce da shi Rukunan Nahawu

Masana kamar irin su, Sani, Muhammad da Rabeh (2000); Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa (1992), sun kira shi da Azuzuwan Kalmomi.

A ta ɗaya ɓangaren kuma akwai Sani (1999), da kuma su Zarruƙ, Kafin Hausa, da Al-Hassan (1987), da suka kira shi da sunan Rukunan Nahawu.

To, kenan azuzuwan kalmomi da kuma rukunan nahawu duka abu guda ne; wato Ɗanjuma ne da Ɗanjummai. Dangane da abin da ya shafi wannan rubutu kuwa, mun kira su da suna Azuzuwan Kalmomi.

Rabe-Raben Azuzuwan Kalmomi

Kamar yadda aka faɗa da farko, masana sun saɓa dangane da adadin azuzuwan kalmomin, saboda haka a wannan rubutun sai zaɓo guda shida da mafiya rinjaye suka yi tarayya wajen zayyano su. Ga su kamar haka:

  1. Suna.
  2. Walikin Suna.
  3. Aikatau.
  4. Bayanau.
  5. Siffa.
  6. Mahaɗi.

Azuzuwan Kalmomi shi ne rarraba kalmomin Hausa zuwa aji-aji bisa la’akari da irin aikin da kalmar ke yi. Akwai saɓanin masana dangane da baiwa wannan darasi suna. Sani, Muhammad da Rabeh (2000); Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa (1992), sun kira shi da Azuzuwan Kalmomi. Sani (1999); Zarruƙ, Kafin Hausa, da Al-Hassan (1987), su kuma sun kira shi da suna Rukunan Nahawu. Waɗannan mabambantan sunaye kuma da  masana suka baiwa wannan darasi ba komai ba ne kamar sunaye Ɗanjuma ne da Ɗanjummai. Dangane da abin da ya shafi wannan rubutu kuma, mun yi amfani da sunan Azuzuwan Kalmomi. A cikin wannan ƙunshi na azuzuwan kalmomi kuma mun samu azuzuwa shida da suka haɗa da suna, wakilin suna, aikatau, bayanau, siffa, da mahaɗi.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo da Koyarwa. Irshad Islamic Publication Cetre LTD. 31, Adelabu Street, Surulere, Lagos-Najeriya.

Jinju M.H. (1981). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company Limited.

Sani M.A.Z. (1999). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Sani M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub