Nahawun Hausa: Jimla

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Bayanau


Gabatarwa

Bayanau kalmomi ne da ke yin ƙarin bayani game da aikatau. Wannan bayani da suke yi shi ya ke fito da aikin a fili. Sukan faɗi gurin da aka yi aikin, lokacin da aka yi aiki ko kuma yadda aka yi, ake yi ko za a yi aiki.

Ma’anar Bayanau

Masana suka ce, kalma ce da ke yin ƙarin bayani game da aikatau a cikin jimla. Wato kenan, wannan kalma, ita ce fitilar da take haskaka aikatau a ganshi a fahimce shi.

Rabe-Raben Bayanau

 1. Bayanau na wuri.
 2. Bayanau na lokaci.
 3. Bayanau na yanayi.

Bayanau na Wuri

Shi ne kalmar da ke bayyana gurin da aka aikata aiki, ko za a aikata ko kuma ake aikatawa. Kalmomi irin su nan, can, gefe, gaba, baya, ƙasa, sama, kusa, nesa, daf, gabas, yamma, da sauransu, duk bayanau ne na wuri. Misali:

 1. Yana zaune a kan kujera.
 2. Ta zauna daf da mijinta.
 3. Ya ajiye tamola a ƙasan teburi.
 4. Yana noma a gabas da gari.
 5. Tafi can ka zauna.

Bayanau na Lokaci

Shi ne kalmar da ke yin bayani game da lokacin da aka aikata aiki, ko za a aikata, ko kuma ake aikatawa. Kalmomi irin su jiya, yau, ɗazu, yanzu, gobe, baya, baɗi, dare, rana, safiya, watan mai kamawa, damina, rani, da sauransu, duk bayanau ne na lokaci. Misali:

 1. Habu ya dawo jiya.
 2. Na ji wani ihu cikin dare.
 3. Ai yaron baɗi zai gama karatu.
 4. Ɗazu ya tafi kasuwa.
 5. Noman damina abu ne mai riba.

Bayanau na Yanayi

Shi ne kalmar da ke yin bayani game da yadda aka aikata aiki, ko za a aikata aiki, ko kuma ake aikata aikin. Kalmomi irinsu da sauri, a hankali, a fusace, a gigice, a guje, da sauransu, duk bayanau ne na yanayi. Misali:

 1. Garba ya iya tuƙi a hankali.
 2. Yaron ya wuce da sauri.
 3. A guje yake tafiya.
 4. Shi da yake magana a gigice, ai ba za a fahimci me yake cewa ba.
 5. A fusace ya zo nan.

Bayanau, kalmomi ne da ke yin bayanani game da aikatau a cikin jimla. Bayanau ya rarrabu zuwa bayanau na wuri wanda ke bayyana wurin da aka yi aiki, ko za a yi ko kuma ake cikin yin aikin. Sai kuma bayanau na lokaci, wanda ke bayyana lokacin da aka yi aikin, ko za a yi ko kuma ake cikin yin aiki. Haka nan kuma akwai bayanau na yanayi, wanda shi kuma nuni yake zuwa ga yadda aka aiwatar da aikin, ko za a aiwatar ko kuma ake aiwatar da aikin.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo da Koyarwa. Irshad Islamic Publication Cetre LTD. 31, Adelabu Street, Surulere, Lagos-Najeriya.

Jinju M.H. (1981). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company Limited.

Sani M.A.Z. (1999). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Sani M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub