Nahawun Hausa: Jimla

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Jimla


Gabatarwa

Jimla, Balarabiyar kalma ce aka Hausantar da ita (جملة). Ma’anar ta ɗaya ce a dukkan harsunan guda biyu; tana nufin jeren kalmomi waɗanda suke bayar da cikakkiyar ma’ana ga mai sauraro. Zarruƙ, Kafin Hausa da Alhassan (2010), sun ce: “Jimla jerin kalmomi ne masu alaƙa a wajen tsari waɗanda kuma suke bayyana wata manufa cikakkiya”. Misali:

  1. Garba mutum ne ƙaƙƙarfa.
  2. Kaji biyar ne a cikin akurki.
  3. Haƙuri abu ne mai kyau.
  4. Gonarka tana da yabanya.
  5. Waccar matar tana da haƙuri.
  6. Matar mutum ƙabarinsa.
  7. Yara manyan gobe.
  8. Ado yana noma a gona.
  9. Bello yakan tafi makarnta da wuri.
  10. Barira ta wanke riga.
  11. Shi ne ya karya baƙar kujerar can.
  12. Ilu ya gasa gyaɗa.
  13. Suna tafiya da sassarfa.
  14. Binta da Delu suna girki.
  15. Jar kaza ta yi ƙwai.

Bari mu duba mu gani, ko waɗannan jimloli da na kawo a sama sun cika ma’aunan da suka zo a cikin ma’anar jimla. Da farko an ce, jerin kalmomi. Abin nufi da jerin kalmomi shi ne a ajiye kalmomi a layi, ɗaya-bayan-ɗaya, daga hagu zuwa dama ba daga dama zuwa hagu ba sannan kuma daga sama zuwa ƙasa, kamar yadda ka ke iya gani a sama. Da zan jera layin farko kamar haka; ƙaƙƙarfa ne mutum Garba ko kuma:
Garba
Mutum
Ne
Ƙaƙƙarfa
Duk sun amsa sunan jere, amma dai ba jimloli ba ne a Daidaitacciyar Hausa. Dole a jera su daga hagu zuwa dama kamar haka: Garba mutum ne ƙaƙƙarfa.

Sai kuma ma’auni na biyu; masu alaƙa a wajen tsari. Me ake nufi da wannan? Ana nufin kalmomin su zama a jeranta su bisa tsarin da ya dace cewa ga kalmar da ta cancanci ta zo farko kafin waccar ta biyo bayanta. Ba wai haka kawai ake jera kalmomin ba. Misali, idan ka ɗauki jeren kalmomi na farko ka sake jerantu su kamar haka: Mutum Garba ne ƙaƙƙarfa. Haka ne ka jera kalmomi amma ba bisa alaƙar tsari ba. Saboda haka, alaƙa a wajen tsari ita ce kalmomin su zama sun daidaita da juna wajen bayar da ma’ana.

Waɗanda suke bayyana manufa cikakkiya. Haka malamai suka ce. Abin da ake nufi shi ne cewa, kalmomin da aka jera su bayar da cikakkiyar ma’ana. Zaɓi guda a cikin waɗannan biyun:

  1. Mutum Garba ne ƙaƙƙarfa.
  2. Garba mutum ne ƙaƙƙarfa.

A wacce daga cikin waɗannan biyun ka samu cikakkiyar manufa? A jere na biyu. Saboda haka sai ka jefar da jeren farko ka ɗauki na biyu, shi ne daidai. Kuma, ka kiyayi gaba, duk lokacin da ka zo gina jimla, sai ka aikata kamar yadda ka koya a nan.

Yankin Jimla

Masana Harshen Hausa sun yanka jimlar Hausa zuwa yankuna ko sassa guda biyu; yankin suna da kuma yankin bayani.

Yankin Suna: Shi ne yankin jimla da yake ɗauke da sunan wanda ya aikata aiki a cikin jimla. Shi yake zuwa a farkon jimla. Wasu suna kiransa da aikau kamar Sani (2007). Zarruƙ, Kafin Hausa da Alhassan (2010) kuma suka kira shi da ma’aikaci. Saboda haka idan manazarci ya ci karo da ɗaya daga cikin waɗannan sunaye guda uku; yankin suna, aikau ko ma’aikaci, to duk abu guda suke nufi.

Duba sashen farko na jimlolin da suka zo a sama; wanda aka tura shi sosai da launin baƙi sannan kuma aka kumbura shi kamar Garba, haƙuri da sauransu, to dukkaninsu; daga 1 zuwa 15, yankin suna ne.

Saboda haka, yankin suna yana iya ɗaukar sunan yanka, suna tattarau, suna gama-gari, jinsi mace ko namiji ko duka biyun a haɗe, tilo ko jama’u, wakilin suna, nunau, adadi, siffa da sauran rukunan nahawu. Sannan kuma shi yake zuwa a farkon jimla kuma a matsayin mai’aikata aiki ko kuma wanda ake bayyanawa a cikin jimla.

Yankin Bayani: Shi ne yankin jimla da yake biyo bayan yankin suna; wato shi ne yanki na biyu. Shi yake yin bayani game da yankin suna. Yana zuwa da aikatau da kuma mai karɓar aiki idan akwai a cikin jimla. Lura da kalmomin da aka rubuta da tafiyar tsutsa kamar mutum ne ƙaƙƙarfa, biyar ne a cikin akurki har zuwa jimlar ƙarshe, su ne yankin bayani a cikin jimla. Kuma cewa, Zarruƙ, Kafin Hausa da Alhassan (2010), sun kira Yankin Bayani da Lamari.

Rukunan Nahawu da suka haɗa da wakilin suna, lamirin suna, lamirin lokaci, aikatau, suna, sifa, bayanau da sauransu, duk sukan zo a yankin bayani a cikin jimla.

Lamirin suna da lamirin lokaci, suna zuwa kafin kalmar aiki a cikin yankin bayani. Duba jimla ta 5; Barira ta… kalmar ta, lamirin suna ce. Sai kuma Bello yakan… kalmar yakan, lamirin lokaci ce.

Su kuwa suna, wakilin suna, sifa da kuma bayanau, suna zuwa ne a bayan kalmar aiki. Wato sai an rubuta kalmar aiki kafin a rubuta su a yankin bayani a cikin jimla. Misali. Barira ta wanke riga. Kalmar riga suna ce; shi ne ya karya baƙar kujerar can. Kalmar baƙar, sifa ce; suna tafiya da sassarfa, kalmar sassarfa, bayanau ce.  Sai ka zurfafa bincike.

Rabe-Raben Jimla

Masana Harshen Hausa sun rarraba jimloli zuwa rabe-rabe da dama gwargwadon fahimta. A wannan rubutun za mu taƙaitu da guda uku kamar haka:

  1. Sassauƙar Jimla.
  2. Sarƙaƙƙiyar Jimla.
  3. Harɗaɗɗiyar Jimla

Sassauƙar Jimla

Sassauƙar Jimla ita ce jimlar da take ɗauke da sassan jimla biyu kacal; yankin suna da yankin bayani. Dukkan jimloli 15 da na kawo misalin da yake sama sauƙaƙan jimloli ne. Sai kuma ta sake kasuwa zuwa; jimla mai aikatau da kuma jimla maras aikatau. Abin nufi, sassauƙar jimla mai aikatau da kuma sassauƙar jimla maras aikatau.

Sassauƙar Jimla Mai Aikatau: Ita ce jimlar da take ɗauke da kalmar aiki ko aikatau ko kuma aka aikata wani aiki a cikinta, wanda yake fita a yankin bayani na cikin jimlar. Nazarci misalan da na kawo a sama, za ka samu cewa tun daga jimla ta 8 har zuwa ta 15, jimloli ne masu aikatau. Saboda kalmomin aiki da suka bayyana a cikin sashen bayaninsu.

Sassauƙar Jimla Maras Aikatau: Ita ce jimlar da babu aikatau a cikin yankin bayaninta. Idan ka sake waiwaitar waɗancan misali da na kawo a sama, za ka samu cewa, tun daga jimla ta 1 har zuwa ta 7, duk babu aikatau a cikin yankin bayaninsu. Saboda haka sun zama sauƙaƙan jimloli marasa aikatau kenan.

Sarƙaƙƙiyar Jimla

Daga sunan sarƙa aka samo wannan suna na Sarƙaƙƙiyar jimla. Ita kuwa ita ce jimlar da aka sarƙafa sauƙaƙan jimloli guda biyu suka zama ɗaya. Misali, idan ka koma sama ka ɗauko jimla ta ɗaya da ta tara, ka gutsure sunan Bello daga jimla ta tara, sannan ka sarƙafa yankin bayanin jimlar da jimla ta ɗaya. Za ka samu wata sabuwar jimla kamar yadda yake a ƙasa. To a nan ƙasa, jimla ta uku ita ce sarƙaƙƙiyar jimla.

  1. Garba mutum ne ƙaƙƙarfa.
  2. Bello yakan tafi makaranta da wuri.
  3. Garba mutum ne ƙaƙƙarfa yakan tafi makaranta da wuri.

Harɗaɗɗiyar Jimla

Jimla ce da ake samarwa ta hanyar haɗa sauƙaƙan jimloli biyu ko fiye da biyu, misali, idan muka haɗe jimla ta ɗaya da ta goma sha ɗaya, za mu samu sabuwar jimla ta uku a misalan da suke ƙasa.

  1. Garba mutum ne ƙaƙƙarfa.
  2. Shi ne ya karya baƙar kujerar can.
  3. Garba mutum ne ƙaƙƙarfa kuma shi ya karya baƙar kujerar can.

Za kuma mu iya haɗe jimla ta 1 da ta 2 da 11 domin mu samar da wata sabuwar jimlar kamar haka:

  1. Garba mutum ne ƙaƙƙarfa.
  2. Kaji biyar ne a cikin akurki
  3. Shi ne ya karya baƙar kujerar can.
  4. Garba mutum ne ƙaƙƙarfa, shi ne ya karya baƙar kujerar can sannan kuma yana da kaji biyar a cikin akurki.

Sai ka zurfafa bincike. Harɗaɗɗiyar jimla ta rabu gida biyu; mai ɗori da marasa ɗori.

Harɗaɗɗiyar jimla mai ɗori: Ita ce jimlar da aka haɗe ta hanyar amfani da kalmomin ɗori kamar irin su kuma, amma, sai dai, saboda, domin, kodayake, idan da sauransu. Misali:

  1. Waccar matar tana da haƙuri kuma haƙuri abu ne mai kyau.
  2. Jar kaza ta yi ƙwai kodayake kaji biyar ne a cikin akurki.

Harɗaɗɗiyar jimla maras ɗori: Ita ce jimlar da ake haɗe ta da alamomin rubutu. Msali:

  1. Waccar matar tana da haƙuri, haƙuri abu ne mai kyau.
  2. Jar kaza ta yi ƙwai, kaji biyar ne a cikin kejin.

Sai ka zurfafa bincike.

Manazarta:


Jinju M.H. (1981). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company Limited.

Sani M.A.Z. (1999). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Sani M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub