Nahawun Hausa: Jimla

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Mahaɗi


Gabatarwa

Mahaɗi, kalma ce da ake amfani da ita wajen ambaton kalmar da ake haɗe kalmomi, ibararori, ko jimloli da ita. Wato sukan haɗe kalma da kalma, ibara da ibara ko kuma jimla da jimla waje guda. Kamar a ce Ado da Idi sun shiga aji. Misali:

  • Haɗe kalma da kalma, kamar haka: Ado da Idi, Ado ko Idi. Da makamantansu.
  • Haɗe ibara da Ibara. Misali, gidan Bala da gidan Sani. Naman akuya ko naman Saniya.
  • Haɗe jimla da jimla. Misali, ka sayo naman akuya ko naman tinkiya. Ado ya ci tuwo amma bai ƙoshi ba.

Mahaɗi shi ne kalmar da ke haɗa kalma da kalma, ko ibara da ibara, ko kuma jimla da jimla. Idan aka ce Ado da Idi, an haɗe kalma da kalma. Gidan Bala da Gidan Sani kuma an haɗa ibara da ibara. Sai kuma, ka sayo naman akuya ko naman tinkiya, an haɗa jimla da jimla kenan.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo da Koyarwa. Irshad Islamic Publication Cetre LTD. 31, Adelabu Street, Surulere, Lagos-Najeriya.

Jinju M.H. (1981). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company Limited.

Sani M.A.Z. (1999). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Sani M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub