Nahawun Hausa: Jimla

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Suna


Gabatarwa

Suna, aji ne na kalma, wanda ke ƙunshe da dukkan wata kalma da idan aka furta ta, ta ke ɗaukar ma’anar sunan mutum, dabba, muhalli, ko wani abu dabam. Kenan, duk wata kalmar da idan aka furta ta, za a ambaci wani abu da ita, to ana kiranta suna.

Sani, yaro, Kano, birni, tuwo, mangwaro, akuya, mage, kurciya, tsintsiya, wuta, gida, da zogale. Dukkan waɗannan kalmomi sunaye ne. Idan aka furta kalmar Sani, an ambaci sunan wani mutum kenan daga cikin mutane. Kalmar Kano kuma, wani birni ake ambata da ita, saboda haka sai ta zama sunan wannan birnin. Haka, haka.

Ma’anar Suna

Suna, kalma ce da ake ambaton mutum, dabba, muhalli, ko wani abu da ita. Wato kenan, duk wata kalma da ake ambato da ita, ta faɗa ajin suna kenan.

Rabe-Raben Sunaye

Akwai hanyoyi da masana suka bi wajen rarraba sunaye.

  1. Suna na Zahiri: Shi ne sunan abin da ake iya gani da ido, ko a ji shi da kunne, ko kuma a taɓa shi da hannu. Sani, murya, bishiya, da sauransu. Dukkan waɗannan sunaye ne na zahiri.
  2. Suna na baɗini: Shi ne sunan ɓoyayyen abin da ba a ganinsa kuma ba a jinsa, amma ana iya ganin tasirinsa, saboda haka an san akwai shi kenan. Misali, farin ciki, ɓacin rai, yunwa, jahilci, ilimi, da sauransu. Idan muka lura da waɗannan kalmomi da aka ambata, babu ɗaya daga cikinsu da ake gani da ido ko a taɓa shi da hannu, ko kuma a ji shi da kunne, amma ana ganin tasirinsu.
  3. Sunaye Ɗaiɗaiku: Su ne sunayen abubuwan da za a iya ƙirga su komai yawansu. Misali, mutum, gida, gona, akuya, da sauransu. Waɗannan rukunin sunaye su ke ɗaukar jam’i. Wato ana iya mayar da su na da yawa. Misali, mutum ɗaya kenan, amma daga biyu zuwa fiye da biyu sai a ce mutane, hakama gida zai koma gidaje, gona kuma gonaki, da sauransu.
  4. Gagara-Ƙirga: Suna ne na abubuwan da ba a iya ƙirga su. Daga cikin irin waɗannan sunaye akwai ruwa, gishiri, da sauransu. Rukunin waɗannan sunaye ba sa ɗaukar jam’i.
  5. Sunan Yanka: Shi ne sunan da idan aka ambata shi yake ambato wani mutum, ko gari, ko kasuwa, guda ɗaya rak. Misali, Ado, Kano, Kasuwar Rimi, Juma’a, da sauransu. Idan muka lura, a nan, za mu fahimci cewa abubuwa ɗaiɗai ake ambata da kowane suna daga cikin sunayen da suka zo a wannan rukunin.
  6. Suna Gama-gari: Shi ne sunan da idan aka ambata shi yake nuni zuwa ga abubuwa da yawa masu jinsi ko nau’i ɗaya. Wato suna ne na tarayya. Dukkan abin da ke da irin wannan jinsi ko nau’i, an yi tarayya da shi a cikin wannan sunan. Misali, mutum, yaro, gari, abinci, ruwa, da sauransu. Idan aka ce mutum, kai ma mutum ne, ni ma mutum ne, saboda haka duk muna ciki.
  7. Tattarau: Suna ne da ya dunƙule abu fiye da ɗaya a cikinsa. Wato suna ne da ya tattaro abubuwa masu yawa a cikinsa. Misali, garke, ƙungiya, ayari, gungu, da sauransu.
  8. Ɗan Aikatau: Suna ne da aka samo shi daga aikatau. Misali, sharewa, kuka, wanka, girki, wankewa, da sauransu.

Jinsi

Jinsi, a suna, kala biyu ne; Namiji da Mace. Wato kenan, idan suna ba namiji bane, to mace ce. Ana bambance tsakanin waɗannan sunaye ne da wasulla.
  1. Jinsin maza yana ƙarewa da wasalin, e, ko i, ko o, ko kuma u (e, i, o, u).
    Sunaye masu wasalin e:
    Dambe, tsage, jele, kare, reshe, jemage, talle, tsalle, bene, talge, balarabe, d.s.
    Misali, Reshe ya faɗo. Bene ya yi kyau. Da sauransu.
    Sunaye masu wasalin i:
    Santsi, hantsi, hatsi, katsi, santi, zogi, zagi, jirgi, fili, ɗaki, mari, d.s.
    Misali, Hantsi ya yi. Zagi ya bi sarki. Hatsi ya nuna. Da sauransu.
    Sunaye masu wasalin o:
    Tsawo, dolo, coko, filo, lilo, doro, dodo, koko, ƙoƙo, nono, tuwo, tsoro, d.s.
    Misali, Dolo ne shi. Ƙoƙo ya fashe. Yawan tsoro ba shi da daɗi. Da sauransu.
    Sunaye masu wasalin u:
    Tulu, hutu, guru, turu, shiru, tudu, d.s.
    Misali, Tulu ne a can. Komai daɗin kiɗa, shiru ya fi shi. da sauransu.
  2. Jinsin mata yana ƙarewa da wasalin a.
    Zana, fawa, ragaya, magana, hasara, gardama, tabarma, damina, d.s.
    Misali, Zana ta faɗi. Hasara bata da daɗi. Da sauransu.

Sauran Ƙa’idoji Game da Jinsi

  1. Dukkan sunan da ake kiran mace da shi to mace ne ko da wane irin wasali ya ƙare. Misali, Rabi, Delu, A’isha, Kade, Mairo, d.s. Har abada waɗannan sunayen mata ne.
  2. Dukkan sunayen unguwanni, garuruwa, birane, ƙasashe, da nahiyoyi, jinsin mace ne. Misali, Garu, Dutse, Najeriya, Afirka.
    Garu unguwa ce a cikin garin Dutse, da ke Najeriya a Afirka. Ita kuwa Afirka, nahiya ce daga cikin nahiyoyin duniya.
  3. Dukkan sunayen ranaku, watanni, da shekara, jinsin mace ne. Misai, Lahdi, jiya, yau, gobe, Muharram, bara, bana, baɗi, d.s. Lura da wannan. Idan wannan Lahdin ta zo, sati biyu kenan. Jiya ta riga ta wuce. Muna fata shekara mai zuwa ta fi ta bana kyau.
  4. Dukkan sunayen kusurwoyi da suka haɗa da Gabas, Yamma, Kudu, da kuma Arewa. Misali, tsakanin Gabas da Yamma wacce ka fi bi?
  5. Sunayen lambobi ma duk jinsin mace ne. Misali, mecece wannan 1? Ɗaya ce. Wannan 2,000,000 fa? Miliyan biyu ce. Da sauransu.
  6. Ana juya jinsi ta hanyar ƙarin wasu harrufa da ke ƙarawa wannan suna ma’ana. Misali:

    Ƙarin harrufan uwa

    Namiji: Gajere, Mace: Gajeruwa.
    Namiji: Dogo, Mace: Doguwa.
    Namji: Baƙo, Mace: Baƙuwa.
    Namiji: Tsoho, Mace: Toshuwa.
    Namiji: Gwauro, Mace: Gwauruwa.

    Ƙarin kalmar ɗan ko 'yar:

    Kalma: Kasuwa,  Namiji: Ɗan kasuwa,  Mace: 'Yar kasuwa.
    Kalma: Sarki, Namiji: Ɗan sarki, Mace: 'Yar sarki.
    Kalma: Baba, Namji: Ɗan baba, Mace: 'Yar baba.
    Kalma: Maiganye, Namiji: Ɗan maiganye, Mace: 'Yar maiganye
    Kalma: Ƙwalisa, Namiji: Ɗan ƙwalisa, Mace: 'Yar ƙwalisa.

Adadin Suna

Abin da ake nufi da adadin suna shi ne yawansa, wanda ka iya zama guda ɗaya rak, ko kuma daga biyu zuwa fiye da biyu. A Hausance, nau'ukan adadi biyu ake da su. Akwai mufuradi, guda ɗaya, da kuma jam'i da ke ɗaukar fiye da ɗaya.

Lura da kalmomin mutum, gida, riga, doki, da kuma fitila. Dukkan waɗannan sunayen ɗaiɗaikun abubuwa ne, saboda haka sun zama mufuradai kenan. Amma idan aka juya su, suka zama mutane, gidaje, riguna, dawakai, da kuma fitulu, to, ana nufin fiye da ɗaya kenan. Saboda haka sun zama jam'i. Misali, idan aka ce mutane, za su iya zama daga biyu har zuwa sama da dubu ko fiye. Masana harshen Hausa, sun fitar da hanyoyi da dama don yin jam'in sunaye daga mufuradi, daga cikin waɗan hanyoyi akwai:

  1. Ƙarin wasalin a, i, e, ko u a kan asalin saiwar kalma. Sai dai, a wasu lokutan ba kai tsaye ake ƙarin wasalin ba, sai an jirkita saiwar suna ta hanyar ƙari ko ragin wani daga cikin harrufan saiwar. Misali, idan muka canja sunan kaza zuwa kaji, za a fahimci cewa an jirkita sunan.
    • Suna:  Makaranci Saiwa: Ma-karant Jam'i: Makaranta
    • Suna: Mahauci Saiwa: Ma-hauc Jam'i: Makahauta
    • Suna: Maƙeri Saiwa: Ma-ƙer Jam'i: Maƙera
    • Suna: Mashayi Saiwa: Ma-shay Jam'i: Mashaya
    • Suna: Baƙo Saiwa: Baƙ Jam'i: Baƙi
    • Suna: Zabo Saiwa: Zab Jam'i: Zabi
    • Suna: Fara Saiwa: Far Jam'i: Farare
    • Suna: Ƙwaro Saiwa: Ƙwar Jam': Ƙwari
    • Suna: Kaza Saiwa: Kaz/Kaj Jam'i: Kaji
    • Suna: Aska Saiwa: ask Jam'i: Asake
    • Suna: Bafatake Saiwa: Ba-fatak Jam'i: Fatake
    • Suna: Kasko Saiwa: Kask Jam'i: Kasake
    • Suna: Kulki Saiwa: Kulk Jam'i: Kulake
    • Suna: Birni Saiwa: Birn Jam'i: Birane
    • Suna: Mashi Saiwa: Mash Jam'i: Masu
    • Suna: Gurgu Saiwa: Gurg Jam'i: Guragu
    • Suna: Maye Saiwa: May Jam'i: Mayu
    • Suna: Laya Saiwa: Lay Jam'i: Layu
    • Suna: Ɗanye Saiwa: Ɗany Jam'i: Ɗanyu
  2. Ƙarin ɗaurin ai. Abin lura a nan shi ne cewa haɗa wasalin a da i kamar yadda suke a nan ba wasali ba ne ɗauri ne. Saboda haka a iya cewa ana gina jam'i ta hanyar ƙarin ɗaurin ai. Sannan kuma dai a wasu lokutan sai an jirkita saiwar sunan. Ga misalai kamar haka:
    • Suna: Makaɗi Saiwa: Ma-kaɗ Jam'i: Makaɗa
    • Suna: Jaki Saiwa: Jak Jam'i: Jakai
    • Suna: Masaki Saiwa: Masak Jam'i: Masakai
    • Suna: Gona Saiwa: Gon Jam'i: Gonakai
    • Suna: Tumaki Saiwa: Tumak Jam'i: Tumakai
    • Suna: Makwanci Saiwa: Ma-kwanc Jam'i: Makwantai
  3. Ƙarin Harrufan aye.
    • Suna: Ɓera Saiwa: Ɓer Jam'i: Ɓeraye
    • Suna: Ganye Saiwa: Gany Jam'i: Ganyaye
    • Suna: Fili Saiwa: Fil Jam'i: FIlaye
    • Suna: Gaula Saiwa: Gaul Jam'i: Gaulaye
    • Suna: Gwani Saiwa: Gwan Jam'i: Gwanaye
  4. Ƙarin harrufan una da kuma uka:
    • Suna: Riga Saiwa: Rig Jam'i: Riguna
    • Suna: Ɗaki Saiwa: Ɗak Jam'i: Ɗakuna
    • Suna: Carbi Saiwa: Carb Jam'i: Carbuna
    • Suna: Mage Saiwa: Mag Jam'i: Maguna
    • Suna: Magani Saiwa: Magan Jam'i: Magunguna
    • Suna: Rafi Saiwa: Raf Jam'i: Rafuka
    • Suna: Zance Saiwa: Zanc Jam'i: Zantuka
    • Suna: Ƙauye Saiwa: Ƙauy Jam'i: Ƙauyuka
    • Suna: Tafi Saiwa: Taf Jam'i: Tafuka
    • Suna: Shafi Saiwa: Shaf Jam'i: Shafuka
  5. Akwai kuma wanda ba a bambantawa tsakanin mufuradi da kuma jam'i. Kalmomin ruwa, iska, farin ciki, suga, gishiri, da makamantansu.

Suna dai kamar yadda aka gani aji ne na kalma da ke ɗaukar ma'anar duk wata kalma wacce idan aka furta ta ke ambaton mutum, dabba, guri, ko kuma wani abu dabam. Sannan kuma mun ga cewa shi kansa sunan, iri-iri ne, akwai suna na zahiri, suna na baɗini, sunan yanka, suna gama-gari, suna ɗaiɗaiku, suna tattarau, suna gagara ƙirga, da kuma zagin aikatau. Haka nan kuma suna yana da jinsi wanda ka ka iya zama namiji ko mace. Ana kuma sauya shi daga namiji zuwa mace ta hanyar ƙarin wasu harrufa da ke ƙaramasa ma'ana. Shi suna yana da lamba wanda ke kasancewa mufuradi (sunan abu ɗaya) ko kuma jam'I (daga biyu zuwa sama). Ana juya suna ya zama jam'i daga mufuradi ta hanyar yi masa ƙarin wasu harrufa da ke ƙara masa ma'ana. Wannan shi ne abubuwan da wannan rubutu ya ƙunsa.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo da Koyarwa. Irshad Islamic Publication Cetre LTD. 31, Adelabu Street, Surulere, Lagos-Najeriya.

Jinju M.H. (1981). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company Limited.

Sani M.A.Z. (1999). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Sani M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub