Nahawun Hausa: Jimla

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Wakilin Suna


Gabatarwa

Walikin suna kalma ce da ake amfani da ita a gurbin da ya kamata a ce suna ne ya zo. Wato kenan idan ana cikin zance, sai aka zo wata gaɓar da ya kamata a ce an ambaci suna amma sai a ƙi ambatar sunan, sai a yi amfani da wannan kalma ta maye gurbin sunan, ka ga ke nan ta wakilce shi ba sai ya zo da kansa ba.

Kalmomi irin su ni, kai, ke, nawa, naku, da sauransu, dukka wakilan suna ne. Misali, maimakon na ce, Na san Ado mutum ne mai haƙuri, zan iya cewa, na san shi mutum ne mai haƙuri. Idan aka lura za a ga cewa kalmar ni, ta wakilci sunana, shi kuma ta wakilci Ado.  

Sannan kuma wasu masana sukan kira shi da Lamiri. Ita kuwa kalmar Lamiri (ضَمِيرْ), kalmar Larabci ce, kuma kai tsaye tana nufin wakili.

Ma’anar Wakilin Suna

Wakilin suna shi ne duk wata kalma da ake amfani da a madadin suna. Ko kuma mu ce, wakilin suna kalma ce da ake amfani da ita a maimakon suna.

Rabe-Raben Wakilin Suna

Masana harshen Hausa sun rarraba wakilin suna zuwa aji-aji, daga ciki akwai:

 1. Katsattse: Wakilin suna katsatte shi ne wanda yake wakiltar mutum kai tsaye. Sannan kuma yana tsayuwa da ƙafarsa. A wannan aji akwai wakilan suna da suka haɗa da ni, kai, ke, shi, ita, su, mu, da kuma ku. Shi ne wakilin sunan da aka sake karkasa shi gida uku ta fuskacin yadda ake magana.
  • Mai yin magana:
   Mufuradi: Ni
   Jam'i: Mu
  • Wanda ake magana da shi:
   Mufuradi: Kai/ke
   Jami'i: Ku
  • Wanda ake magana a kansa:
   Mufuradi: Shi/ita
   Jami'i: Su
 2. Ɓoyayye: Shi ne wakilin sunan da baya fito da wanda ake magana a kansa fili. Wato idan aka ambata shi, kowa ma yana iya shiga ciki. Waɗannan su ne wane, wance, su wane, su wance. Akan yi amfani da wannan waikilin suna a irin maganganu da suka shafi habaici, baƙar magana, harbin iska, tsegumi, da makamantansu. Misali, idan ana son yin tsegumin wani a cikin mutane, ana iya cewa, ai jiya na ga wane a gefen hanya yana sayen gyaɗa. Ko kuma a cikin habaici a ce, wane, na ga kana wani shisshige min, to ina mai tabbatar maka da cewa hawaniyarka ta kiyayi ramata. Da  sauransu.
 3. Madubi: Wakilin suna ne da ya ke wakiltar mutumtaka. Yana muhimmantar da abin da ake magana a kansa. Sannan yakan zo bayan suna ko wakilin suna katsattse. A cikin wannan ƙunshi na wakilin suna akwai kaina, kansa, kanka, kanku, kanki, kanta, da kuma kanmu. Misali, ni da kaina na je gurin. Ka ce shi kansa na ke so ya zo. Yanzu idan aka share ɗakin ai ku kanku za ku fi jin daɗin zama a ciki.
 4. Wakilin Sunan Mallaka: Wakilin suna ne da ya ke nuna mallaka. Sannan ya kasu gida biyu:
  • Masu zaman kansu. Waɗannan wakilan suna suna ɗaukar jinsi. Namiji: nawa, naka, naku, nasu, naki, nata, namu. Mace: tawa, taka, taku, tasu, taki da kuma tata. Waɗannan a duk lokacin da ake rubutu, ba a haɗe su. Misali, wannan gidan nawa ne, da kuma waccar motar, tawa ce.
  • Marasa zaman kansu. Maza na, nmu, nki, nta, nsu, nka da kuma nsa. Mace ta, rta, rmu, rki, rta, rsu, rsa, da kuma rka. Su kuma ba a raba su da suna, haɗe su ake yi a rubutu. Misali gidana, gidanku. Rigata, rigarku, da sauransu.
 5. Nunau: Wakilin suna ne da yake nuni zuwa ga guri, kusa ko nesa. Waɗannan su ne, nan, can, wannan, wancan, waccar, da kuma waɗannan. Misali, waccar rigar ta faɗo. Wancan mutumin baƙo ne. A nan za ka zauna. Matsa can. Da sauransu.
 6. Game duniya: Shi ne wakilin sunan da ba a tantance abin da yake wakilta kai tsaye. Wasu masanan kuma sun kira shi da wakilin suna maras ƙaidi. Cikin irin waɗannan wakilan suna akwai kowanne, kowacce, wani, wata, wasu, waɗannsu, da sauransu. Misali, idan aka ce kowanne ɗalibi ya tabbata ya iya rubutun Hausa. A nan, dukkan ɗalibin da ya ji wannan magana, da wanda ya iya rubutun, da wanda bai iya ba, zai ɗauka da shi ake.
 7. Tambayau: Wakilan suna ne da ake yin tambaya da su. Irin waɗannan su ne, wane? Wace? Waɗanne? Me? Da sauransu. Misali, wane ya rufe wannan ƙofar. Haka kuma ana iya ƙara musu ne, misali, wanene ya rufe wannan ƙofar?

Kenan, yanzu an fahimci cewa, wakilin suna shi ne dukkan wata kalma da za a iya amfani da ita a gurbin da ya kamata a yi amfani da suna. Sannan kuma cikin azuzuwan wakilan suna akwai, katsattse, ɓoyayye, madubi, wakilin sunan mallaka, nunau, game duniya, tambayau, da kuma sauran waɗanda ba mu ambata ba.  

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo da Koyarwa. Irshad Islamic Publication Cetre LTD. 31, Adelabu Street, Surulere, Lagos-Najeriya.

Jinju M.H. (1981). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company Limited.

Sani M.A.Z. (1999). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Sani M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan - Najeriya.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub