Tsarin Sauti

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tsarin Sauti


Gabatarwa

Sauti (الصوت ), kalmar aro ce, mai asali daga Larabci. Amma a Hausa ƙara ake cewa. Kamar k ace, na ji ƙarar mota a misalce. Saboda haka kenan, sauti yana nufin ƙara.

A wannan rubutu kuwa, sauti yana nufin furuci, furuci kuma na magana. Wannan rubutu zai yi magana ne kai tsaye game nazarin sauti, Harshen Hausa.

Ma’nar Sauti

Masana fannin Hausa, sun ba shi ma’anoni da dama, a wannan rubutun za mu ɗauki ta Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa (2006), saboda zamowarta gamammiya. Suka ce: “Sauti shi ne duk wata ƙara wadda za a iya jin ta da kunne”.

Wannan ita ce gamammiyar ma’anar sauti, amma idan muka dawo fannin nazarin sauti a keɓance, to sauti kuma a nan, yana nufin furuci. Shi kuwa furuci, ma’anarsa ita ce fitar da sauti daga baki. Idan sauti ya baro baki, ya fito waje, to ya zama furuci.

Ƙwayoyin Sauti

“Ƙwayar sauri ita ce alama mafi ƙanƙanta da akan yi da murya, wadda kuma ke haɗuwa da ‘yan’uwanta su bayar da siga irin ta magana” kamar yadda ya zo a Sani, Kafin Hausa da kuma ALhassan (2010).

Daga wannan ma’ana za mu fahimci cewa, ƙwayoyin sauti su ne irin su /b/, /l/. /a/ da sauransu. Misali, da za mu ɗauki kalmar biro, za mu samu cewa akwai ƙwayoyin sauti har guda huɗu a cikinta kamar haka: /b/, /i/, /r/ da /o/. Kenan, dukkan wani harafi daga cikin harrufan abjadin Hausa sauti ne.

Samuwar Sauti

Sauti, abu ne samamme daga iska da kuma aikin wasu gaɓɓan jiki. Waɗannan gaɓɓai su ne ke tare iska idan ta fito daga huhu zuwa waje. Idan haka ta faru sai sauti ya samu.

Gaɓoɓin Sauti

Gaɓoɓi ko gaɓuɓɓa ko sassan jikin ɗan’adam da ke da ruwa-da-tsaki wajen samar da sauti su ne: Leɓɓa, haƙora, harshe, saman baki, maƙwallato da tantanin maƙwallato.

Duk da rarrabuwar masana game da waɗannan sassa, da kuma sunayen da suka riƙa kiransu da su, waɗannan da aka ambata a sama su ne gama-gari.

Waɗannan sassa, sun rabu zuwa gida biyu: Masu motsi da marasa motsi. Mai karatu, kafin na lissafa maka rukunansu, zan so ka buɗe bakinka. Yanzu na san bakinka, ya rabu gida biyu, wasu ayarin sassan suna sama, wasu kuma an bar su a ƙasa. To, duk sassan bakinka da suke a ƙasa (Leɓen ƙasa, haƙora da harshe), su ne masu motsi; su suke motsawa su yi sama, su haɗu da na sama. Idan suka je sama kuma, sukan taras da leɓen sama, haƙoran sama, da kuma saman baki da aka karkasa shi zuwa; hanƙa, ganɗa da kuma hanɗa. Saboda haka kenan muna da gaɓoɓin sauti da suka haɗa da:

  1. Leɓɓa: Guda biyu ne; akwai ɗaya a ƙasan baki da kuma ɗaya a saman baki. Ana kiransu da leɓen sama da leɓen ƙasa.
  2. Haƙora: Haƙora seti biyu ne, ɗaya a ƙasan baki ɗaya kuma a saman baki.
  3. Harshe: Harshe guda ɗaya ne a cikin baki. Yana kwamce a  ƙasan baki. Sannan kuma an karkasa shi zuwa tsinin harshe, gaban harshe, doron harshe da kuma jijiya a bisa rabon (Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa, 2006). Shi kuwa Sani (2007), ya raba shi zuwa; tsinin harshe, ƙirjin harshe, gaban harshe da kuma doron harshe. A wannan rubutun za mu yi aiki da rabon na ƙarshe na Sani (2007).
  4. Saman Baki: Shi ne sararin cikin baki ta sama wanda harshe yake taɓawa. Shima ya kasu zuwa gida uku kamar haka: Hanɗa, ganɗa da hanƙa.
  5. Maƙawallato: Shi ne sashen maƙogwaro da ya fi ko’ina tudu; wato shi ne guri mafi tudu a jikin maƙogwaro wanda ana iya ganin tudunsa daga waje har ma a iya taɓa shi da hannu. Yana motsawa a lokacin da ake magana.

Mai karatu, zan so ka shafa wuyanka ta saman maƙogwaronka daga mahaɗar jiki zuwa mahaɗar kai, duk muhallin da ka ji ka taɓa wani abu mai tudu kamar ƙashi da ya fi ko’ina tudu a jikin maƙogwaron naka daga ciki, to nan ne maƙwallato.  

Iska

Iska, tana da matuƙar muhimmanci wajen samar da sauti, babu wani amo ko murya da za ta iya samuwa ba tare da iska ba. Wannan dalili ne ma ya saka Sani, Muhammad da Rabeh (2000), suka ambata cewa: “Babu furucin da za a iya yi ba tare da iska ba”.

Asalin wannan iska mai samar da sauti da muke magana a kanta, ta kasu gida biyu: Iskar huhu da kuma iskar maƙwallato. Ita iskar huhu, ita ce wacce take fitowa daga huhu kai tsaye, kuma ta sake rabuwa gida biyu; mai fitowa waje da mai faɗawa ciki. Dukkan masana fannin sautin Hausa sun ce mai fitowa wajen nan ita ce mai amfani wajen samar da sauti. Ita kuwa mai komawa cikin bata da wani amfani sai dai hamma.

Ita ma kuma iskar maƙwallaton asalinta daga huhu ne, idan ta fito ta iyo sama kamar za ta fita, sai shi maƙwallaton ya datse ta ta hanyar rufewa da buɗewa da yake yi. Idan ya datse ta, sai wata ta faɗa ciki wata kuma ta fito waje. Saboda haka shima sai tasa iskar ta kasu gida biyu; mai fita waje da mai faɗawa ciki, amma dukkansu biyun masu amfani ne wajen samar da sauti.

Yawan Harrufan Hausa

Dangane da abin da ya shafi sauti, Daidaitacciyar Hausa tana da adadin harrufan da ake amfani da su. Idan kuma aka ce harrufa a nan, to ana nufin haɗakar baƙaƙe da wassula waɗanda kowane ɗaya daga cikinsu ƙwayar sauti ce.

A dunƙule, Hausa tana da harrufa; wato sautuka guda 44, talatin da biyu daga ciki baƙaƙe, goma sha biyu kuma wassula kamar yadda ya zo a Yahaya, Zariya, Gusau da kuma ‘Yar’aduwa (2006).

Manazarta:


Junaidu I. da ‘Yar’aduwa T.M (Babu Shekara). Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Nigeria.

Sani M.A.Z. (2007). Tsarin Sauti Da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Sani M.A.Z., Muhammad A. Da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Langugae Don Masu Rubuta Jarabawar WASC da SSCE. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M da ‘Yar’aduwa T.M. (2006). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub