Ohinoyi Mohammed Sani Omolori

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ohinoyi Mohammed Sani Omolori 1956 - 1996 A.D.


Gabatarwa

Bayan sabauta saukar Attah Ibrahim daga karagar mulki da guguguwar dimokuraɗiyya ta yi, sai kuma aka samu sabon sauyi a yanayin naɗa wanda zai ɗare karagar mulkin ƙasar Ibira, ta yadda ya zamo a wannan karon jama'a ma suna da rawar takawa, ba wai kawai Turawa ne suka yi gaban kansu suka naɗa musu sarki ba kamar yadda ya gabata a baya. Saboda wannan dalilin sai shi kansa taken sarautar ya tashi daga Attah, ya koma Ohinoyi, kalmar da ke da ma'ana ta sarki idan aka juya ta zuwa Hausa.

Alhaji Mohammed Sani Omolori, wanda yake tsohon ma'aikacin hukumar gargajiya (Native authority) ne, a wannan karon shi ya samu goyon bayan jama'a wanda kuma Turawa suka amince da naɗinsa a matsayin sabon sarkin Ibira a karo na huɗu.

Manazarta


Edo V. O. (2008). The Evolution and Development of Central Administration in Ebiraland, 1920-1997. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.nobleworld.biz/images/Edo.pdf

Okene A.A. da Suberu O.A. (2013). The British Conquest of Ebiraland, North Central Nigeria 1886-1917: A Military Interpretation of Sources. Professor (History & International Studies) Nigerian Defence Academy Kaduna, Africa’s Top Military University PMB 2109, Kaduna – Nigeria. American International Journal of Contemporary Research Vol. 3 No. 6; June 2013.

Segun J. A. (2013). Politics and Conflicts: A Study Of Ebiraland, Nigeria (1977-2007). Department of Political Science and International Relations, School of Social Sciences, College of Development Studies, Covenant University, Ota, Nigeria.Masarautar Okene

Sarakuna Ƙasar Ibira

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub