Me ka ke nema?


Shafin Farko

Alhaji (Dr.) Ibrahim Sulu-Gambari, CFR


Gabatarwa

Mai Martaba Sarkin Ilorin kuma ciyaman na majalisar sarakunan Jahar Kwara, Alhaji (Dr.) Ibrahim Sulu-Gambari. Mutum ne mai ilimin addini da na zamani. Tsohon lauya ne. Mutum ne mai son jama’arsa da addininsa. Ƙwararre ne shi a fannin shari’a.


Mai Martaba sarkin Ilorin: Alh. Ibrahim Sulu Gambari, OFR.

Salsalarsa

An haifi Mai Martaba Sarkin Iliroin na goma sha ɗaya, Alhaji (Dr.) Ibrahim Sulu-Gambari a garin Ilorin wacce yanzu ta zama helikwatar mulkin Jahar Kwara, sannan kuma fadar mulkin Masarautar Ilorin.

An haife shi a ranar 6 ga watan Yuni na shekarar 1940. Shi ɗa ne ga sarkin Ilorin na tara, wato Shehu Sulu Gambari, wanda shi kuma ɗa ne ga Muhammed Laufe Aremo Bawa, hakimin Lanwa, shi kuma ɗan Bawa, sarkin Ilorin na bakwai, shi kuma ɗan Zubairu, sarkin Ilorin na uku, shi kuma ɗan Abdussalami, sarkin Ilorin na farko, shi kuma malam Abdussalami ɗa ne ga Shehu Alimi.

Sunan mahaifiyarsa Hajiya A’ishatu Bolanta Sulu-Gambari. Auren zumunci aka yi tsakanin mahaifi da mahaifiyar Mai Martaba Sarkin Ilorin, Alhaji (Dr.) Ibrahim Sulu-Gambari. Ita mahaifiyarsa ‘ya ce ga sarkin Ilorin na takwas, Abdulƙadir Kelani wanda shi kuma ɗa ne ga sarkin Ilorin na bakwai. Saboda haka shi kakannin Mai Martaba Sarki Alhaji (Dr.) Ibrahim Sulu-Gambari na wajen mahaifiya wato Muhammed Laufe da kuma kakansa na wajen mahaifi wato Abdulƙadir Kelani, wa da ƙani suke; dukkansu ‘ya’yan sarkin Ilorin na bakwai ne, wato Bawa, sai suka haɗa auren zumunci tsakanin ‘ya’yansu biyu; Shehu Sulu Gambari ɗan Muhammed Laufe, da kuma ita Hajiya A’ishatu Bolanta ‘yar Abdulƙadir Kelani, cikin hukuncin Allah kuma su suka haifi sarkin Ilorin na goma sha ɗaya.

Karatunsa

Alhaji (Dr.) Ibrahim Sulu-Gambari (CFR), ya yi karatunsa na firamare a makarantar ‘Natiɓe Authority School, Omu-Aran’ daga shekarar 1953 zuwa 1956. Daga nan kuma ya wuce zuwa ‘Offa Grammar School’ inda a nan ya yi karatun sikandire daga shekarar 1957 zuwa 1960. Sai kuma makarantar ‘Oakham School Rutland’ ta ƙasar Ingila daga 1961 zuwa 1962. Daga nan kuma sai ‘City of Westminister College’ ita ma a Ingila daga shekarar 1962 zuwa 1963.

Ya kuma karanci aikin Lauya a makarantun ‘Middle Temple’ ta Landan daga 1964 zuwa 1967. Sai kuma ‘Nigerian Law School’ da ke Legas daga 1967 zuwa 1968. Sai kuma ‘Kings College, Uniɓersity of London’ inda ya karanta digiri a fannin Lauya mai darajar L.L.B. Hons a shekarar 1966. Ya kuma samu L.L.M. Degree a shekarar 1967. Saboda haka shi cikakken Lauya ne mai lasisi.

Muƙaman da ya riƙe

Ya riƙe muƙamai da dama, daga ciki a kwai zamowarsa ‘Permanent Secretary and Solicitor General’ na tsohuwar Jahar gongola a shekarar 1976. Sannan ya taɓa riƙe muƙamin Alƙalin Alƙalai na Jahar Bauchi, Bornu, da Gongola a shekarar 1977. Ya kuma taɓa zama alƙalin Babbar kotun Barno (Judge, high court, Borno) daga 1978 har zuwa 1983. Sannan kuma ya zama ‘Justice Court of Appeal’ daga 1983 zuwa 1995 na reshen Lagos muƙamin da daga kansa ya samu sarauta ya bar aiki.

Zamowarsa Sarki

Mai Martaba Sarkin Ilorin, Alhaji (Dr.) Ibrahim Sulu-Gambari, ya ɗare kujerar sarautar Ilorin a ranar 20 ga watan Agusta na shekarar 1995. An kuma yi bikin naɗinsa a ranar 11 ga watan Nuwamba na shekarar 1995. Tun waccar shekara ta 1995, wacce zuwa yau shekaru (2016), yana da shekaru 21 kenan a kan karagar mulkin masarautar Ilorin ɗin.

Manazarta:


Kalandar Shekara-Shekara ta Masarautar Ilorin. Bugun 2016.

Jimba A.S. (2008). Portraits of Royalty, An Illustrated Spotlight on the 11th Emir of Ilorin, Mai Martaba Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari. The Queen Mother, Hajiya Aishat Bolanta Sulu-Gambari And the Emir's Senior CHiefs and Top Aides.



Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub