Lawal Isa Kaita

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Lawal Isa Kaita


Gabatarwa

Alhaji Lawal Kaita mutumin jahar Katsina ne, Ya yi gwamnan jahar Kaduna daga shekarar 1983 zuwa 1983.

Haihuwa

An haifi Alhaji Lawa Kaita a garin Katsina helikwatar mulkin jahar Katsina, a watan Oktoba na shekarar 1932.

Karatu

Alhaji Lawal Kaita ya yi karatunsa a 'Elementary School, Katsina' a 1939 zuwa 1944, daga nan kuma sai 'Middle School, Katsina' a shekarar 1944 zuwa 1946. Ya kuma halarci kwalejin Kaduna, da kwalejin Barewa ta Zariya, duka daga 1946 zuwa 1950. A shekarar 1950 ya shiga 'College of Veterinary Medicine Vom, Plateu State' inda ya kammala a shekarar 1953, a shekarar ya shiga makarantar tsimi da kimiyyar siyasa (School of Economic and Political Science) da ke ƙasar Landan, inda ya kammala a shekarar 1971.

Gogayyar Aiki

Ya riƙe muƙmai da yawa, daga ciki akwai muƙamin 'Veterinary Assistant' daga shekara 1953 zuwa 1963 na 'Northern Region', sannan kuma ya zama 'Principal Livestock Officer' na dai yankin arewan daga shekarar 1963 zuwa 1966, sai kuma zamowarsa 'Principal Development Officer' wannan kuma a ƙarƙashin hukumar gwamnatin tarayyar Najeriya mai suna 'Federal Livestock and Meat Authority', ya kuma riƙe muƙamin sakataren hukumar ruwa ta Jahar Tsakiyar Arewa (North Central State) wacce ke da helikwata a Kaduna, sai kuma muƙamin 'Presidential Liasing Office' na Kano da ya riƙe daga shekarar 1979 zuwa 1983.

Zamowarsa Gwamna

An zaɓi Alhaji Lawal Kaita a matsayin gwamnan jahar Kaduna, a shekarar 1983 a ƙarƙashin tutar jamai'iyyar NPN. Wannan mulki nasa ya gamu da cikas ɗin sojoji inda suka hamɓar da gwamnatin farar hula ta shugaba Alhaji Shehu Shagari, Saboda haka ya yi mulki ne na tsawon watanni uku kacal, daga Oktoba na 1983 zuwa Disamba na 1983.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).



Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub