Patric Ibrahim Yakowa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Mr. Patrick Ibrahim Yakowa


Gabatarwa

Mr. Patrick Ibrahim Yakowa, haifaffen garin Fadan Kagoma ne da ke cikin ƙaramar hukumar Jema'a ta jahar Kaduna. An haife shi a ranar 1 ga watan Disamba na shekarar 1948.

Karatu

Ya yi karatunsa a makarantun 'St. Mary's Secondary School, Fadan Kaje', da kuma 'St. John College, Kaduna', daga nan kuma ya shiga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Ya fita da digiri na farko a fannin 'Social Science' a watan Yuni na shekarar 1972.

Gogayyar Aiki

Ya fara aiki tun a tsohuwar Jahar Tsakiyar Arewa (North Central State) da ke da helikwata a Kaduna, har sai da ya kai matsayin 'Permanent Secretary' a 'Ministry of Health, Works, and Transport', a shekarar 1990. Daga wannan muƙami kuma sai ya koma gwamnatin tarayyar Najeriya, har zuwa lokacin da Marigayi janaral Muhammadu Abacha ya yi masa muƙamin kwamishina a Kaduna a shekarar 1994 zuwa 1997, sannan kuma aka mayar da shi muƙamin darakta na 'Joint Services' a ma'aikatar tsaro 'Ministry of Defence'daga shekarar 1997 zuwa 1998, sannan kuma aka yi masa darakta a 'Ministry of Solid Minerals Development' daga 1998 har zuwa 1999 lokacin da aka yi masa 'Permanent Secretary', daga nan kuma ya bar aiki.

Shigarsa Siyasa

Tun barowarsa aikin gwamnati, sai kuma ya shiga harkokin siyasa. Ya riƙe manyan muƙamai a siyasa kamawa tun daga na kamfen har zuwa na gwamnati. Ya bada gudunmawa sosai wajen kamfen ɗin takarar gwamnan Kaduna Ahmed Muhammad Maƙarfi a zaɓen 2003, sannan kuma shi ne ciyaman na kwamatin tantance 'yan takarar jahar Rivers na jama'iyyar PDP duk a 2003. Sannan kuma ya zama sakataren gwamnatin Kaduna a 2003.

Mataimakin Gwamna

Mr. Patric Ibrahim Yakowa ya zama mataimakin gwamnan jahar Kaduna a shekarar 2005 bayan rasuwar Stephen Shekari.

Zamowarsa Gwamnan Kaduna

An rantsar da Mr. Patric Ibrahim yakowa a matsayin gwamnan jahar Kaduna a shekarar 2010, bayan ɗaukakar Arc Mohammed Nmadi zuwa mataimakin shugaban ƙasa.

Mutuwarsa

Mr. Patrick Ibrahim Yakowa ya rasu a kan wannan kujera ta gwamna a shekarar 2012 a sanadiyyar hatsarin jirgin sama.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).



Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub