Ƙasar Yarbawa Kiɗan Dundun

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙasar Yarabawa Kiɗan Dundun


Gabatarwa

Dundun: Kiɗa ne daga cikin kaɗe-kaɗen Ƙasar Yarabawa. Yana daga cikin keɗe- keɗe mafiya shahara da kuma tasiri daga cikin kaɗe-kaɗen gargajiya a ƙasar Yarabawa. Ana kaɗa shi a bukukuwan binne shahararrun mutane da suka mutu. Ana yi musu kirari ta hanyar ambato irin kyawawan ayyukan da suka gudanar a lokacin rayuwarsu ta cikin kiɗan, (Adenike, 2014). Ƙari a kan wannan kuma, Adedeji (2005), ya saka kiɗan dundun a cikin jerin karɓaɓɓun kaɗe-kaɗen gargajiya na addinin Kirista a Ƙasar Yarabawa.

Amfani

Oluga da Babalola (2012), suka ce, ƙari a kan damar da kiɗan dundun yake da shi na samar da sauti domin a yi rawa, ana kuma amfani da shi wajen:

 1. Isar da saƙon muzantawa.
 2. Yabo.
 3. Bayar da shawara.
 4. Karin magana.
 5. Sanar da bayyanar babban baƙo da kuma tafiyarsa a wajen taro.
 6. Yin kirari ga mutane.


Gangar Iya ilu

Ayarin Ganguna

Ana amfani da ayarin ganguna a cikin kiɗan dundun waɗanda sukan bambanta ta fuskacin yawa. Ga guda bakwai daga ciki (Adenike, 2014; Oluga da Babalola, 2012):

 1. Iya Ilu Dundun/Iyaalu: Ita ce ganga mafi muhimmanci da kuma tsawo a cikin jerin gangunan, ana ɗaukar ta a matsayin uwar sauran gangunan da ke cikin ayarin. Ana kaɗa ta da gula tare kuma da matse ta da hannu a lokaci guda domin samun irin muryar da ake so. Tana fitar da muryoyi barkatai.
 2. Kerikeri: Ita ke biye wa Iya Ilu a girma. Ganga ce da ke bayar da murya ɗaya a cikin wannan kiɗan.
 3. Gangan: Siffarta ɗaya da Kerikeri.
 4. Gudungudun wadda take ganga ce da ke fitar da murya biyu a cikin wannan kiɗa.
 5. Isaaju: ‘Yar jagora, ƙarama ce ita ta fuskacin girman jiki idan aka kwatanta ta da waɗanda suka gaba ce. Ita ke jagorancin sautin kiɗa ta fuskanci tafiyar kiɗan cikin sauri ko sannu-sannu.
 6. Kanango: Ita ce mafi ƙaranta a cikin jerin ganguna da suke kama guda. Tana aiki irin na isaaju.
 7. Omele: Ita kuma murya ɗaya take bayarwa a cikin wannan kiɗa kuma siffarta daban da saura.

Manazarta


Adedeji F. (2005). Classification of Nigerian gospel music styles. An ciro daga a shekarar 2020, daga shafin:https://www.revistas.usp.br

Adenike I.A. (2014).The media, the reconstruction of drumming, and the tradition of the dùndún and the bàtá ensemble of the Yorùbá in South Western Nigeria. Delta State University, Nigeria.

Oluga S. O. da Babalola H. A. L. (2012). Drummunication: The Trado-Indigenous Art of Communicating with Talking Drums in Yorubaland. Global Journal of Human Social Science, Arts and Humanities, Volume 12, Issue 11, Version 1.0. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://globaljournals.org/GJHSS_Volume12/5-Drummunication-The-Trado-Indigenous.pdf

Masarautun Ƙasar Yarabawa

Ijoba ile Yoruba
Kingdoms of Yorubaland
Kaɗe-Kaɗe


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub