Ƙasar Yarbawa Gudugud

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙasar Yarabawa Gangar Gudugudu


Gabatarwa

Gudugudu, ɗaya ce daga cikin ayarin gangunan Yarabawa da ake kaɗawa a cikin kiɗan dundun. Tana da kai guda ɗaya sannan kuma ana kaɗa ta da gular da aka yi daga fatar rago ko ta akuya.


Gangar Gudugudu
Hoto:MIMO; musical instrument museums online

Kayan Haɗi

Ana yin gudugudu da kewayayyen katako wanda ake yi wa sha ko siffa irin ta ƙaramar rariya ko matankaɗi sannan a rufe gefe ɗaya da jemammiyar fatar akuya ko ta rago. Sannan sai a yi mata mariƙa da wasu ‘yan gajejjerun itatuwa guda biyar a ɗaure su a jikinta tare da lulluɓe su da fata. Ana manna mata nake, abin da aka kira ida a Yarabance a tsakiya. Ana yi mata maratayi da saƙaƙƙiyar igiyar suturar da aka saƙa.

Gudugudu, ganga ce da ke fitar da amo kala biyu. Idan aka daki kan nake, tana fitar da ɗan ƙaramin amo, idan kuma aka daki fatar kai tsaye sai ta fitar da wani amon daban.

Da ita ake fara koya kiɗa. Yara ‘yan shekaru biyar zuwa takwas ne ke fara koyon kiɗa da ita. Suna kaɗa ta suna rera waƙa kamar haka: b’ótán ma tún r’oko wadda za a iya fassarawa da, idan ta ƙare zan koma gona.

Manazarta


Ajewole J. (2009). Indigenous Knowledge System in Dundun Sekere Court Music. Department of Creative Arts, University of Lagos, Lagos, Nigeria. The Performer (Vol. 11, 2009). An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://ejournals.unilorin.edu.ng

Akintonde M. A. da Areo M. O. (2013). Art and Craft of Old Oyo: It’s Manifestation in the Present Oyo. Department of Fine and Applied Arts, Ladoke Akintola University of Technology, Ogbomosho, Nigeria. IOSR Journal Of Humanities And Social Science (IOSR-JHSS) Volume 15, Issue 5 (Sep. - Oct. 2013), PP 50-59. An ciro a shekarar 2020 daga shafin:  http://www.iosrjournals.org/iosr-jhss/papers/Vol15-issue5/H01555059.pdf?id=7746

Ihunwo O. (2018). Drums as a unifying deity in Africa: Reminiscing the Nigerian drum festival. Department of Theatre and Film Studies University of Port Harcourt, Nigeria. International Journal of Applied Research. An ciro a shekarar 2020 daga shafin:  http://www.allresearchjournal.com

Masarautun Ƙasar Yarabawa

Ijoba ile Yoruba
Kingdoms of Yorubaland
Kaɗe-Kaɗe


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub