Ƙasar Yarbawa Kiɗa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kiɗa a Ƙasar Yarabawa


Gabatarwa

Kiɗa, hanya ce ta sadarwa sannan kuma ginshiƙi a harkar cuɗanya a tsakanin mutanen Afirka, Oikelome (2013). Abu ne da yake taka muhimmiyar rawa wajen nishaɗantar da ɗan’adamu.

Kiɗa abu ne mai matuƙar tasiri a cikin al’adun Yarabawa. Kusan babu wata sabga ta rayuwa da babu kiɗa a cikinta a Ƙasar Yarabawa.  Suna da nau’ukan kaɗe-kaɗe da dama da suka keɓanta da kowace sabga tasu kamawa tun daga haihuwa, aure, addini, har zuwa mutuwa.

Muhimmancin Kiɗa

Owoaje (2014), ya siffata kiɗa a matsayin muhimmin abu a cikin al’adun Yarabawa wanda ake danganta asalinsa da zuriyar Àyàn; wato makaɗa. Makaɗa suna da matuƙar muhimmanci a dukkan na’ukan bautar Yarabawa, kusan ana iya cewa kowane nau’in bauta a ƙasar Yarabawa yana da wani keɓantaccen kiɗa, waƙa da kuma rawa ta musamman.

Rabe-Raben Kayan Kiɗa

Ana iya rarraba kayan kaɗe-kaɗen Yarabawa ta hanyar la’akari da yadda ake amfani da abin kiɗan kamar haka: Ganguna, kayan busa da kuma kayan girgizawa.

Nau’ukan Kiɗa

Kaɗe-kaɗen Yarabawa suna da tarin yawa, amma muhimmai daga ciki kuma mafiya tasiri guda biyu ne: dundun da kuma bata. Su ne suke neman zama ruwan dare, game duniya a cikin kaɗe-kaɗen Yarabawa. Ana kaɗa su kusan a kowace sabga ta Yarabawa idan ka cire harkar sarauta.

David (2018) ya lissafo waɗannan a matsayin nau’kan kaɗe-kaɗen Yarabawa: Dundun, Bata, Gbedu, Sakara da kuma Gelede.

Manazarta


David J. F. (2018). Traditional Music Education in Nigeria: Bata Drum in Perspective. Music Unit, Department Of Faa/ Music Federal University Ndufu-Alike, Ikwo. American Journal of Humanities and Social Sciences Research (AJHSSR) e-ISSN: 2378-703X, Volume-02, Issue-09, pp-136-139. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: www.ajhssr.com

Oikelome A. (2013). Performance Practice in Afrobeat Music of Fela Anikulapo Kuti. Department of Creative Arts, University of Lagos, Nigeria. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://theartsjournal.org

Owoaje T. O. (2014). The Yorùbá Native Air Tradition of Choral Music in Christian Liturgy 1920-1980. Institute of African Studies, University of Ibadan. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https:// ir.library.ui.edu.ng

Masarautun Ƙasar Yarabawa

Ijoba ile Yoruba
Kingdoms of Yorubaland
Kaɗe-Kaɗe


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub