Ƙasar Yarbawa Gangar Sekere

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙasar Yarabawa Gangar Sekere


Gabatarwa

Sekere wanda ake furta shi da Shekere a Yarabance, ɗaya ne daga cikin kayan kiɗan Yarabawa; muatnen Kudu Maso-Yammacin Najeriya, wanda ake girgiza shi tare da shafawa wanda kuma asali butar duma ce babba ake yi mata ƙarin wasu kayayyaki take rikiɗewa ta zama ganga amma daga cikin ayarin kayan girgizawa.

Oikelome (2013), ya siffata sekere da cewa, sèkèrè yana daga cikin dangin kayan kiɗan da ake girgizawa wanda kuma asalinsa butar duma ce wadda ake lulluɓe wani gefenta da raga sannan a mammaƙala wuri a jikinta. Ana riƙe ta da hannu ɗaya daga wuyanta sannan a riƙa girgiza ta tare kuma da shafa ta ko kuma bugu a hankali da tafin ɗaya hannun domin a riƙa sarrafa sautin da take fitarwa.


Sekere (Shekere)

Amfani

Sekere, abin kiɗa ne da ake amfani da shi a mabambantan sabgogin da suka shafi al’adun Yarabawa, Iroko Theater (2009); yana daga cikin ayarin kayan kiɗan addinin Musulunci a garin Ilorin, Femi (2018); ana amfani da sekere wajen dasa kyakkyawar tarbiyyar zaman tare ta cikin karin magana, Olatunji (2012); Yana daga cikin ayarin kayan kiɗan sarkin Oyo (Oloofin of Oyo), Ajewole (2009), Akintonde da Aeo (2013) inda na ƙarshen suka ƙara samuwar mutum-mutumin sekere a ƙofar fadar Sarkin Oyo a cikin rubutunsu saboda muhimmancin da yake da shi a gurin sarkin. Ana girgiza sekere tare da sauran kayan kiɗa a lokacin bukukuwan naɗin sarauta, suna, aure da kuma lokutan bukukuwan binne gawarwaki, Ajewole (2009).

Manazarta


Ajewole J. (2009). Indigenous Knowledge System in Dundun Sekere Court Music. Department of Creative Arts, University of Lagos, Lagos, Nigeria. The Performer (Vol. 11, 2009). An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://ejournals.unilorin.edu.ng

Akintonde M. A. da Areo M. O. (2013). Art and Craft of Old Oyo: It’s Manifestation in the Present Oyo. Department of Fine and Applied Arts, Ladoke Akintola University of Technology, Ogbomosho, Nigeria. IOSR Journal of Humanities and Social Science (IOSR-JHSS), Volume 15, Issue 5 (Sep. - Oct. 2013), PP 50-59. An ciro a shekarar 2020 daga shafin:  http://www.iosrjournals.org/iosr-jhss/papers/Vol15-issue5/H01555059.pdf?id=7746

Femi A. (2018). Nigerian Popular Music is Everywhere: Proliferation or Development? Department of Music Obafemi Awolowo University Ile-Ife, Nigeria. International Journal of Humanities and Cultural Studies ISSN 2356-5926. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://link.springer.com

Iroko Theater (2009). London African Story 2009. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: http://www.irokotheatre.org.uk/docs/Artefacts.pdf

Oikelome A. (2013). Performance Practice in Afrobeat Music of Fela Anikulapo Kuti. Department of Creative Arts, University of Lagos, Nigeria. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://theartsjournal.org

Olatunji M. O. (12). Yorùbá Proverbs and Musicality. Department of Music, Obafemi Awolowo University, Ile-Ife, Nigeria. Legon Journal of the HUMANITIES, Volume 23. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.ajol.info/index.php/ljh/article/viewFile/87359/77073

Masarautun Ƙasar Yarabawa

Ijoba ile Yoruba
Kingdoms of Yorubaland
Kaɗe-Kaɗe


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub