Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kwararrafa


Gabatarwa

Kwararrafa, wata tsohuwar daula ce da rukunin ƙabilun da ake kira Ƙawancen-Kwa (Kwa-Group) suka kafa ta a yankin Arewacin Kogin Binuwai. Daula ce da wasu masana tarihi suke ganin an kafa ta a cikin ƙarni na 14. Ta kuma yi sharafinta daga wannan ƙarni har zuwa cikin ƙarni na 17 (Dinslage da Leger, 1996). Haka nan, Okpeh da Ochefu (babu lokacin bugu) sun ambata cewa tarihi ya tabbatar da samuwar wata daula mai suna Kwararrafa a arewa da kogin Binuwai. Wannan daula ta haɗaka tsakanin waɗannan ƙabilu masu asali guda, Jukunawa ne suka shugabance ta.


Jukanawa suna gaisar da sarkinsu

Asali

Rubuce-rubuce masu tarin yawa, kamar irin su Dr. Dawuda (2011), Mac-Leva (2009), Okunna, Emman, Gausa, da Solomon, (2014), Ujorha (2012), Dinslage da Leger (1996), sun ruwaito cewa, yarurrukan da suka kafa wannan daular ƙwance ta Kwararrafa daga Gabas suka fito tare da ayyana Yamen a matsayin tushen su.

Yararruka

Yarurrukan da suka haɗu suka kafa wannan daula ta haɗaka suna da tarin yawa, amma kaɗan daga cikin su sun haɗa da: Jukun, Igala, Ibira, Idoma, Alago (Boumo, 2011; Onawo, 2016), Boumo (2011) ya ƙara da Nupe, Mada, Kantana, Rindre, Eggon, Bassa Nge da Bassa Komo. Onawo (2016), ya ƙara da Goemi, Migili, Etulu, Iyala da Aros. Dinslage da Leger (1996), kuma suka zayyano Kwami, Kupto, Kushi, Piya, Bole, Bantu, Bole, Ngamo, Karekare, Kirfi, da Galembi. Andoma na Doma; wato Onawo (2016), ya ce, Jukunawa su ne shugabanni tare da Aku a matsayin jagoran addini.

Yaƙuƙuwa

Mutanen Daular Kwararafa, mutane ne masu matuƙar jarumtaka wajen yaƙi, an ruwaito cewa, sun yi galaba a yaƙin da suka gwambza da manyan masarautun ƙasar Hausa waɗanda suka haɗa da Kano, Katsina, Dutse, Ningi, da kuma Zazzau (Wikipedia, 2016; Northern Nigerian Publishing Company, 1970; Sanusi, 2009).

Wannan magana, ana iya ƙarfafarta da sunayen wasu unguwanni guda biyu da ke cikin garuruwan Kano da Zariya. A garin Kano akwai wata unguwa mai suna “Yakasai”, wacce ruwayar kunne-ya-girmi-kaka ta sheda mana cewa kalma ce da ke nufin “Za mu dawo ko muna dawowa” wacce ta fito daga bakin su Jukunawa a lokacin da suka ci Kano da yaƙi. Haka nan kuma akwai unguwa mai suna ‘Tudun Jukun” a cikin garin Zariya.

Durƙushewa

Rikicin shugabanci (tattaunawa da sarkin Pindiga), gujewa hare-hare daga daular Barno ta wani gefen, da kuma mayaƙan musulunci na daular Shehu Ɗanfodiye daga wani gefen (David, 2013; Boumo, 2011), na daga cikin manyan dalilan da ya kawo ƙauracewar wasu yarurrukan daga wannan yankin suka ƙetara zuwa kudu da Kogin na Binuwai.

Manazarta:


David M.A. (2013). Ebira Youth Forum Association (E.Y.F.A). An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://ebirayouthforumassociation.blogspot.com.ng /2013/05/history-of-ebira-people.html

Dawuda G.A. (2011). Are The Jukuns Jews? Nigerian Masterweb Citizen News. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://nigeriamasterweb.com/blog/index.php/2011/06/ 04/are-nigeria-s-jukuns-jews

Mac-Leva F. (2009). Nigeria: How Giant Crocodiles Guided Jukun to Kwararafa. Daily Trust. An ciro a chekarar 2016, daga shafi: http://allafrica.com/stories/200906240052.html

Northern Nigerian Publishing Company. (1970). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company, Zariya – Najeriya.

Okunna, E da Gausa, S. (2014). Adapting the Jukun Traditional Symbols for Textile Design and Production. Mgbakoigba: Journal of African Studies. Vol. 3. July, 2014

Sanusi N. M. (2009). Stories of Dutse Palace 1421 – 2009. An buga wannan littafi a maɗaba’ar jahar Jigawa.

Ujorha T. (2012). Did the Jukun originate from Egypt? Daily Trust. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.dailytrust.com.ng/weekly/index.php/feature s/10585-did-the-jukun-originate-from-egypt

Boumo E. (2011). Factoring Inter-Group Relations In The Lower Benue Valley To Circa 1900 A.D. Department of History, Benue State University Makurdi, Benue State, Nigeria. African Journal of Arts and Cultural Studies Volume 4, Number 2, 2011

Dinslage S. and Leger R. (1996). Language And Migration The Impact Of The Jukun On Chadic Speaking Groups In The Benue-Gongola Basin. Berichte des Sonderforschungsbereichs 268, Band 8, Frankfurt a. M. 1996: 67-75

Edo V. O. (2008). The Evolution and Development of Central Administration in Ebiraland, 1920-1997. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.nobleworld.biz/images/Edo.pdf

Okpeh O.O. da Ochefu Y.A. (Babu Lokacin Bugu). The Idoma Ethnic Group: A Historical And Cultural Setting.


Daular Kwararrafa

Yarurrukan Kwararrafa


Masarautun Jukun


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub