Burumawa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Burumawa


Burumawa, ƙabila ce wacce ta fi yawa a ƙaramar hukumar Kanam, yawanta ya kai kashi tamanin (80%) cikin ɗari na yawan jama’ar ƙaramar hukumar ta Kanam, a cikin Jahar Plateau ta Tarayyar Najeriya. Haka nan ma kuma ana samun su a ƙaramar hukumar Wase, wanda a can kuma yawansu ya kai kashi arba’in (40%) cikin ɗari na yawan jama’ar ƙaramar hukumar ta Wase.

Sannan kuma ana samun su a cikin yankin tsakiyar Najeria (Middle Belt). Har-wa-yau dai ana samun cu a jahar  Taraba, a garin Wukari da kuma wasu garuruwan. Hakanan kuma, akan same su a garuruwan Lantang, Shendem, Ƙua’an-Pan, da sauransu a cikin jahar ta Plateau.

Asalin sunan wannan ƙabila shi ne Bogghom, ana ambatonta da furuci mabambanta bisa bambancin ƙabilu. Furucin Hausawa; Burum, shi ne wanda ya fi karɓuwa, ya danne saura. Saboda haka sai ƙabilar ta fi shahara  da suna Burumawa.

 

 

 

Babban Shafin Tarihi

Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka ya?a shafin