Sarkin Burum Alhaji Shehu Sulaiman

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Burum, Alhaji Shehu Suleiman



Alhaji Shehu Suleiman, Pankwal Bogghom


Gabatarwa

Alhaji Shehu Sulaiman, shi ne mai martaba sarkin Masarautar Bogghom na farko. Mutum ne shi masanin harkar sarauta wanda ya ɗauki tsawon shekaru hamsin a cikin harkar sarauta. Kuma, ya fara ne daga tushe, wato daga matakin dagaci, ya zama hakimi, yanzu kuma sarkin yanka mai daraja ta biyu. Kenan, idan ka so kana iya ce da shi farfesa a sarauta.

Mutum ne shi mai haƙuri, karimi, jajirtacce, mai sauƙin hali, sannan kuma mai matuƙar son zaman lafiya da haɗin kai, wannan dalilin ne ma ya saka har ya iya haɗa kan al’ummar Bogghom; Musulmi da Kirista. Manomi ne shi, makiyayi, ɗankasuwa, sannan kuma gogaggen basarake.

Mai karatu, akalar wannan rubutu ta doshi kawo maka ɗan taƙaitaccen tarihin Alhaji Shehu Sulaiman; dagacin Namaran, hakimin Namaran, hakimin Dengi, Pankwal Tankwal, yanzu kuma Pankwal Bogghom.

Haihuwa

Duk da cewa, ba a samu cikakkiyar ranar haihuwarsa ba, amma dai ya zuwa yanzu yana da shekaru tamanin a duniya. Wato kenan an haife shi a shekarar 1938.

Salsala

Pankwal Bogghom, Alhaji Shehu Sulaiman, ya fito daga zuriyar gidan maharbin nan Nammam, wanda ya kafa garin Namaran. Shi ɗa ne ga Sulaimanu, shi kuma ɗan Jibji, shi kuma ɗan Ki’ssah, shi kuma ɗan Layi, shi kuma ɗan Jatnong, shi kuma ɗan Shinsho, shi kuma ɗan Lo’op, shi kuma ɗa ga Nammam maharbi sannan kuma wanda ya kafa garin Namaran sama da shekaru 500 da suka shuɗe. Wato zamanin da sana’ar harbi ce babbar hanyar samun abinci.

Karatu

Pankwal Bogghom, Alhaji Shehu Sulaiman ya tashi da karatun Al-Ƙur’ani. An kai shi makarantar allo a garin Salluwei wanda a yanzu wannan gari yana cikin ƙaramar hukumar Wase ta jahar Plateau a jamhuriyar Najeriya.

Alhaji Shehu Suleiman, bai jima a wannan gari ba Allah ya karɓi rayuwar sarkin garin mai suna Abubakar sarkin Dutse; sarkin Wase kenan. Wannan rasuwa ta haifar da ɓaraka game da waye zai maye gurbin marigayin sarkin, abinda ya kai ga salwantar wata yarinya, wanda hakan kuma ta saka mahaifin Alhaji Shehu ya ɗauke shi daga wannan gari, ya mayar da shi gabansa, domin cigaba da karatun.

A wancan lokaci da muke bayani, akwai matuƙar ƙarancin makarantun boko na gwamnati a wannan yankin, sai dai ɗan abin da ba za a rasa ba na makarantun Kiristoci ‘yan mishan. Saboda haka, Alhaji Shehu bai samu nasarar shiga makarantar zamani ba a lokacin ƙuruciyarsa. Amma daga baya,  bayan ya girma, ya saka kansa-da-kansa a makarantar yaƙi-da-jahilci. Inda ya samu nasarar samun ilimi bakin gwargwado, wanda har ma yakan iya sarrafa na’urar lissafi ta zamanin wato Raskwana (Reckoner).
Girma.

Alhaji Shehu Suleiman, ya tashi a gaban mahaifansa tun ƙuruciyarsa, yana taya su ayyukan gida da na gona, shi ma kuma yana yin nasa domin ya zama mai dogaro da kansa kamar yadda aka saba, har zuwa lokacin da ya yi aurensa na farko; ladan noma, inda a wannan gaɓar ma, ya keɓe nasa gidan a cikin gidansu, kafin daga baya ya fice daga gandu, ya koma nasa gidan na kansa. Wannan kuma ita ce tsohuwar al’adar Bahaushe wacce yawancin ƙabilun arewancin Najeriya suka koya, musamman ma Musulmin cikinsu.

Sana’a

Tun kafin wannan gaɓar na gaya muku cewa shi manomi ne, makiyayi sannan kuma ɗankasuwa.

Noma

Na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya taras. Haka nan ma Alhaji Shehu, tun yana ƙarami ya ke zuwa gona domin taya mahaifinsa aiki. Da ya ɗan data, sai ya raba biyu, da safe ya je gonar mahaifinsa ya yi masa aiki, da yamma kuma ya tafi gawainarsa/gayaunarsa ya noma nasa amfanin gonar, domin ya zama mai dogaro da kansa. Idan buƙatar kashe kwabo da ɗari ta taso, ba sai ya tambaya a gida ba.

Sannu a hankali lamarin gawainar Alhaji Shehu ya bunƙasa, har ta kai ga noma ya zamar masa sana’a, ya mallaki abubuwan da suka jefa shi cikin lissafin attajiran gari.

Kiwo

Bayan noma, Alhaji Shehu yakan ɗaure dabbobi ya kiwata. Dabbobin da ya ke kiwatawa su ne shanu, abinda ya bashi damar mallakar garken shanu.

Kasuwanci

Alhaji Shehu Suleimanu, ya kasance mutum mai sha’awar dogaro da kansa, saboda haka bayan da ya yi fice a harkar noma, sai kuma ya fara saye-da-sayarwa, abin da ya kai shi ga buƙatar ubangida domin ya koyi harkar cinikayya. Fitattun ‘yan kasuwar da Alhaji Shehu ya koyi kasuwanci a hannunsu akwai Alhaji Ibrahim Kuku, wanda ya koyi kasuwanci a hannunsa tun yana matsayin wakilinsa, har ta kai ga yana cin gashin kansa. Sannan kuma sai hamshaƙin mai kuɗi na lokacin, Alhaji Musa Ali Gere na garin Dengi, wanda Alhaji Shehu ya koyi sana’ar auduga a gurinsa.

Wannan harka ta kasuwanci, ita ce babbar abinda ta haɓɓaka tattalin arziƙin Alhaji Shehu, sannan kuma ta share masa fagen zamowa basarake.

Sarauta.

Gogaggen basarake, idan ka so kana iya ce da shi farfesa a sarauta. Tun yana ɗan shekara talatin a duniya aka ɗora masa rawanin dagaci. Sannu a hankali ya zama hakimi, yanzu kuma ya ke kan kujerar sarki mai martaba ta biyu, a tsawon shekaru hamsin.

1968 Dagacin Namaran

Sarautar garin Namaran, sarauta ce da gidaje biyu ke gadonta; akwai Ba’Shinsho mai ma’ana ta zuriyar Shinsho, waɗanda su ne asalin masu garin, jikokin Nammam, wanda ya sari garin, akwai kuma Ba’Kyak; wato zuriyar gidan Kyak, wanda su kuma wani dalili ne ya saka rawani ya faɗa gidansu. Waɗannan na biyu, rawanin ya daɗe a gidansu sama da shekaru ɗari, kafin Allah ya kawo Alhaji Shehu Suleiman a cikin shekarar 1968, ya dawo da ita gida.

Bayan rasuwar dagacin Namaran Adamu Li-layi, sai kujera ta zama babu kowa a kanta. Mahaifin Alhaji Shehu, Suleimanu, wanda a lokacin shi ne Ciroman Namaran, shi ya nemi wannan kujera, amma Allah cikin hikimarsa ya ɗora ɗansa Alhaji Shehu a kai. Suleimanu ya nemi wannan kujera tare da sauran ‘yan takara daga ɗaya gidan, amma da lamari ya cukur-kuɗe, bayan ƙarfin Suleiman ya ƙare, sai ya nemi tallafin ‘ya’yansa game da cigaba da ɗaukar ɗawainiyar takarar wannan kujera. Alhaji Shehu, ba tare da nufin komai ba a ransa, sai ya kwashi shanunsa guda shida, ya kai kasuwa ya sayar, ya kawo kuɗin ya baiwa mahaifinsa domin cigaba da wannan ɗawainiya.
Allah cikin hikimarsa, sai ya saka Alhaji Suleimanu ya riƙa tura ɗansa Alhaji Shehu zuwa gidan sarkin Kanem, domin kai saƙonnin da kuma jiyo cigaban da aka samu dangane da neman wannan kujera. Wata rana Alhaji Shehu yana kan hanyarsa ta komawa gida Namaran daga Kanam, sai ya ci karo da wani tsoho tukuf, kekensa ya lalace, ya rasa yadda zai yi. Wannan tsoho yana cikin wannan hali sai ga Alhaji Shehu. Saboda haka tsohon nan ya tsayar da Alhaji Shehu, ya nemi taimakonsa. Kasancewar Alhaji Shehu mutum mai tausayi, sai ya baiwa wannan tsoho nasa keken, shi kuma ya karɓi na tsoho, ya tura zuwa gari bisa yarjejeniyar, Alhaji Shehu zai je ya gyara ya kaiwa tsoho har gida sannan ya karɓi nasa. Har Alhaji Shehu ya fara tafiya, sai tsohon nan ya kiraye shi, ya tambaye shi ko daga ina yake kuma wanne dalili ne ya kai shi gurin? Alhaji Shehu ya kwashe dukkan labari ya gayawa tsoho, da tsoho ya ji dalili, sai ya ce ai kuwa na ga kamar kai za a yiwa wannan sarauta ba mahaifin naka da ka ke nemawa ba, hankalin Alhaji Shehu ya tashi, saboda gudun kar mahaifin nasa ya ce dama munafurtarsa yake yi.

Da Alhaji Shehu ya isa gida, sai ya je ya gyara keke, ya kaiwa wannan tsoho. A kan wannan gaɓa ma sai wannan tsoho ya nemi Alhaji Shehu da ya je ya samo masa farin yadi. A lokacin, farin yadin nau’i biyu ne; akwai mai tsada, akwai kuma alawayye mai sauƙin kuɗi, saboda haka sai Alhaji Shehu ya sayawa wannan tsoho alawaiye ya kai masa. Wani abu da ya ƙara baiwa Alhaji Shehu mamaki, da irin wannan alawaiye da ya kaiwa tsoho aka naɗa masa rawanin sarautarsa ta farko. Wannan lamari ya yi matuƙar baiwa Alhaji Shehu mamaki.

A tare da faruwar wannan labari da aka ambata, su kuma ‘yan adawa a ta nasu ɓangaren, sai rura wutar ƙorafe-ƙorafe suke yi game da takarar Suleimanu, ciki har da cewa shekarunsa sun yawaita, ba zai iya wannan ɗawainiyar ba. Da abu ya zama haka, sai sarkin Kanam ya kira Suleimanu ya shaida masa haka, amma kuma ya bashi zaɓin cewa ya bayar da sunan ɗansa wanda yake ganin hankalinsa ya kwanta da shi, zai iya riƙe wannan kujera, tun da dai ya alƙawarta musu cewa kujera za ta koma gidansu. Wannan lamari an yi shi cikin sirri mai tsanani. Saboda haka sai Suleimanu ya bayar da sunan Alhaji Shehu, da labari ya ɓulla ta wata kafa, ai fa sai lamari ya sake salo, daga ƙarshe, sun yi yunƙuri sace Alhaji Shehu domin su halakar da shi. Amma, ta Allah ba tasu ba, sai da wannan rawani ya hau kan Alhaji Shehu.

1981 – 1983 Hakimin Namaran

A cikin shekarar 1981, gwamnatin jahar Plateau ta ƙirƙiri wasu sababbin gundumomi guda uku a ƙasar Bogghom, wanda Namaran ta zamo ɗaya daga ciki. Wannan shi ne dalilin da ya saka Alhaji Shehu ya zama hakimin sabuwar gudunmar Namar.

Gwamnatin soja ta shugaba Buhari, ita ta yi fatali da dukkan irin waɗannan sababbin gundumomi da ƙananan hukumomi da wasu gwamnatocin jahohi suka ƙirƙira da nufin kusantar da harkar mulki ga jama’a a duk faɗin ƙasa. Wannan lamari ya rutsa da wannan sabuwar gunduma ta Namaran, wacce aka jone ta da gundumar Dange tare da sauran ƙawayenta.

1994 – 1996 Hakimin Riƙo na Dengi

Naɗin Alhaji Shehu a matsayin hakimin riƙo na Dengi ya biyo bayan rasuwar hakimin Dengi, Malam Halilu Bawa. Rikice-rikice da suka biyo bayan rasuwar da kuma naɗin Alhaji Ibrahim Bawa, Galadiman Kanam, a matsayin hakimin riƙo, su suka sabauta shigar gwamnatin Plateau cikin lamarin tare kuma da bayar da umarnin gudanar da zaɓen wanda zai maye gurbin, biyowa bayan bore da Burumawa; ƙabilar Bogghom suka yiwa wannan naɗin, sakamakon su ne jama’a mafiya yawa a wannan yankin.

Dagatai uku suka tsayawa wannan takara, inda Alhaji Shehu ya doke su da ƙuri’u goma sha uku daga cikin goma sha biyar. Sakamakon da ya nuna sauran ‘yan takarkarun kowa ya zaɓi kansa kenan.

1996 Hakimin Dange Mai Cikakken Iko

Bayan riƙon ƙwarya ta wannan kujerar hakimci da Alhaji Shehu ya yi na tsawon shekaru biyu, sai gwamnati ta sake bayar da umarnin gudanar da zaɓen cikakken hakimi. A wannan karonma, tarihi ne ya maimaita kasan. Waɗancan digatai guda uku su suka sake tsayawa takara. Sannan kuma dai, da adadin waɗancan ƙuri’u guda goma sha uku Alhaji Shehu ya sake cin wannan zaɓe.

Pankwal Tankwal
2005 Pankwal Bogghom


Alhaji Shehu Suleiman, Pankwal Bogghom

Pankwal Bogghom, muƙami ne da ke da fassara ta sarkin Bogghom; ita kuwa masarautar Bogghom, masarauta ce ta sarkin yanka mai daraja ta biyu; wato second class emir a Turance. Alhaji Shehu Suleiman, shi ne wanda ya fara riƙe wannan muƙami a tarihin masarautar ta Bogghom.

An sha fama kafin wannan masarauta da wannan sarki nata su zauna da gindinsu. Tun bayan kafa wannan masarauta da gwamnatin Plateau ta yi a zamanin gwamna Joshua Dariye, a ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2002, ake ta kai ruwa rana tsakanin masu buƙatar ganin wannan masarauta ta tabbata da kuma masu adawa da hakan musamman ma masarautar Kanam, wacce take ganin daga jikinta za a yagi wannan masarauta.

Daga cikin mafiya munin matakan da ‘yan adawa suka ɗauka har da sace wani daga cikin jiga-jigan fafutikar neman kafa masarautar da kuma shi kansa Pankwal Bogghome ɗin, amma Allah cikin ikonsa haƙarsu bata cimma ruwa ba duk da cewa sun yi nasarar sace mutum ɗaya.

Bayan dukkan kwan-gaba-kwan-baya da aka yi ta samu game da kafuwar wannan masarauta, gwamnatin zaɓaɓɓen gwamnan Plateau, Solomon Lalong, ta tabbatar da wannan masarauta tare kuma da naɗin Alhaji Shehu Suleiman a matsayin sarkinta na yanka mai daraja ta biyu a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2917, kamar yadda ya ke ɗauke cikin takardar tabbatarwar. Cikakken bayanin abubuwan da suka wakana yana shafin fafutikar kafa Masarautar Bogghom.

Gogayyar Aiki

Shekaru hamsin a kujerar sarauta, ba makawa dole a samu gogayya. Kira shi farfesa a sarauta, bana jin ka samu matsala. Ya fara daga digaci, ya zama hakimi yanzu kuma sarkin yanka mai daraja ta biyu.

Idan kuwa muka leƙa taskar adana bayanan muƙamai da ya riƙe, to sai mu tsakurowa mai karatu cewa ya riƙe muƙaman da suka haɗa da:

  1. 1968 zuwa yau: Mamba a majalisar sarakunan Ƙaramar Hukumar Kanam tun daga 1968 har zuwa yau, abin da ya bashi damar zamowa mamba mafi daɗewa a wannan majalisa.
  2. 1968 zuwa yau, ya kasance mamba a wasu kwamitocin da suka haɗa da, kwamatin zaɓar tantance sarakunan Ƙaramar Hukumar Kanam; kwamatin aikin hajji na ƙaramar hukumar Kanam; kwamatin tantance iyaka tare da faɗaɗata na ƙaramar hukumar Kanam; kwamatin annobar ambaliyar ruwa, da sauransu.
  3. 1970 da 1983: Ya yi aiki a kwamatin naɗa sarkin Kanam mai daraja ta ɗaya a shekarar 1970 da kuma rantsar da shi a shekarar 1983.
  4. 1975: Ya halarci Bikin Daba na farko na arewacin Najeriya da aka yi a garin Kaduna a cikin shekarar 1975.
  5. 2001 zuwa Yau: Mamba a kwamatin tsaro na jahar Plateau, mai kula da rikicin ƙabilanci dana addini a jahar Plateau.
  6. 2004 – 2005: Shugaban riƙo na majalisar sarakunan Ƙaramar Hukumar Kanam. Muƙamin da shi kaɗai ya taɓa riƙewa  bayan rasuwar sarkin Kanam har zuwa naɗin sabon sarkin mai ci yanzu.

Gudunmawa

Tun tasowar Alhaji Shehu Suleiman ya ke bayar da gudunmawa wajen ganin al’ummarsa ta ci gaba domin sauƙe nauyin jagorancin da aka ɗora masa. Zamowarsa adali, cikakkiyar dama ce da ya samu ta daidaita tsakanin jama’arsa ba tare da nuna bambanci ba tsakanin addinai da kuma sauran yarunkan da ke ƙarƙashin mulkinsa waɗanda ba yarensu ɗaya ba.

Alhaji Shehu Suleiman ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen haɓɓaka harkar al’adun jama’arsa, samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, inganta harkokin tsaro da addini, ciyar da harkar ilimi gaba, da sauran fannonin rayuwa da ambato su ke da wahala.

Iyali


Alhaji Shehu Suleiman, tare da wasu jikokinsa"

Alhaji Shehu Sulaiman, Pankwal Bogghom, yana da mata huɗu, yaya goma sha huɗu da kuma jikoki tamanin da bakwai a yanzu haka. Ya auri mata shida a rayuwarsa, biyu sun rasu, yanzu haka kuma yana tare da huɗu. Haka nan ma ‘ya’ya, ya haifi ‘ya’ya talatin da tara, yanzu ya rage saura goma sha huɗu masu rai; takwas maza da kuma mata guda shida. Sannan kuma da jikoki tamanin da bakwai ringis.

Matarsa ta farko ita ce Hauwa, da ta haifa masa ‘ya’ya takwas; huɗu sun mutu, sannan kuma akwai rayayyu guda huɗu, biyu mata biyu maza. Baƙuwa, ita ce ta biyu, wacce ta haifa masa ‘ya’ya biyar; biyu sun rasu saura uku, biyu maza ɗaya mace. Sai kuma Maryam ta ukunsu, ta haifa masa ‘ya’ya huɗu; uku maza ɗaya mace, macen ta rasu ta bar mazan. Salamatu ita ce ta huɗu, wacce ta haifa masa ‘ya’ya goma; bakwai sun mutu saura uku kuma duk mata. Dukkan waɗannan mata guda huɗu ringis, suna nan a raye tare da shi a garin Namaran.

Jummai da ‘Yarbaka kuma sun rasu. Jummai ta haifa masa ‘ya’ya uku; biyu sun rasu saura ɗaya. Ita kuwa ‘Yarbaka, bata taɓa haihuwa ba. Waɗannan su ne mata, ‘ya’ya da kuma jikokin mai martaba sarkin Bogghom, Alhaji Shehu Sulaiman.


Alhaji Shehu Suleiman, tare da wasu jikokinsa"

Manazarta:


Shehu A.Y. (2018). Out of Mountain A Dynasty Is Born. Yaliam Press Limited (Babu adireshi).



Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub