Daura Ƙofar Kiɗi da Hauka
Shafin Farko

Ƙofar Kiɗi da Hauka


Sunan wannan ƙofa ya samo asali ne lokacin da Sarkin Daura Abdu, wanda aka fi kira da Sarkin Gwari Abdu, ya fita ta wannan ƙofa a lokacin da Fulani masu jihadi suka kawo wa garin Daura hari.

A lokacin Jahadin Shehu Ɗanfodiye na shekarar 1802 – 1806, Fulani sun kai hari masarautar Daura kamar yadda suka yi a sauran masarautun ƙasar Hausa. Da suka je wannan gari na Daura, sai suka datse dukkan ƙofofin shiga da fita garin Daura, suka hana masu shiga dan kai musu abin saye, sannan su kuma basu da damar fita. Ganin yadda lamura suka faru haka, sai shi Sarkin Daura, wato Sarkin Gwari Abdu, ya ce to tunda haka al’amari ya kasance, maimakon a zo a zubar da jinin mutanensa saboda shi, a je a sara masa wannan ƙofa. Sai kuwa aka je ana kiɗi ana sara wannan ƙofa har suka gamma sannan sarki ya fice ta wannan ƙofa. Da labari ya iske Fulani cewa sarki ya fice ta wannan ƙofa kuma ana ta kaɗe-kaɗe, sai suka ce an fita ana kiɗi da hauka. Wato an fice ana ta kaɗe-kaɗe kuma sannan a haukace. Saboda haka sai wannan suna ya bi wannan ƙofa. Kenan bisa wannan labari za mu ga cewa ita wannan ƙofa an sare ta ne a wannan tsakanin na Jahadin Shehu Ɗanfodiye wanda ya kasance kenan tsakanin 1802 – 1808.

Manazarta:


Abubakar M.S. (2007). Taƙaitaccen Tarihin Daura. Majalisar Sarkin Daura. An buga a: Ammani Printing Press.

Tattaunawa da Wakilin Tarihin na Daura da kuma Dogarin Sarkin Daura mai suna Ɗandaushe, a shekarar 2016.

Babban Shafin Tarihi
Masarautr Daura

Sarakunan Daura


Ƙofofin Daura


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub