Rijiyar Kusugu
Shafin Farko

Rijiyar Kusugu


Gabatarwa

Rjiyar Kusugu na ɗaya daga cikin ababen tarihin da ke taskace a garin Daura. Babu wani takaimaiman lokaci da za a iya cewa shi ne lokacin da aka haƙa wannan rijiya ko kuma wanda ya haƙa ta. Abin sani kawai dangane da tarihin ta shi ne cewa zuwan wani Balarabe mutumin ƙasar Bagadaza (Baghdad) wato Iraƙ a yau, mai suna Abu Yazid wanda aka fi kira da Bayajidda, ya kashe wata macijiya mai suna sarki wacce ke hana jama'a shan ruwa a wannan rijiya sai lokacin da bata da buƙata da wannan rijiya. Hoton farko na ƙasa shi ne asalin rijiyar, sannan kuma hoton da ke gefenta shi ne ɗakin da aka adana ta a cikinsa. Har yau ɗin nan wannan rijiya tana nan kuma da ruwa a cikinta. Jama'a, musamman ɗalibai manazarta Hausa, sukan je dan ziyarar gani da ido. Kalli bidiyon da ke ƙasan waɗannan hotuna.

Rijiyar Kusugu


Marubucin Wannan Shafin Tare Da Dogarin Sarkin Daura Suna Ɗebo Ruwa Daga Rijiyar Kusugu

Manazarta:


Abubakar M.S. (2007). Taƙaitaccen Tarihin Daura. Majalisar Sarkin Daura. An buga a: Ammani Printing Press.

Tattaunawa da Wakilin Tarihin na Daura da kuma Dogarin Sarkin Daura mai suna Ɗandaushe, a ranar 24 ga watan Mayu na shekarar 2016.

Ziyarar gani da ido. 25 ga watan Mayu na shekarar 2016.

Babban Shafin Tarihi
Masarautr Daura

Sarakunan Daura


Ƙofofin Daura


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub