Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hukumar Jiragen Ruwa  ta Najeriya



Hatimin Hukumar Jiragen Ruwa


Gabatarwa

Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa wadda ake rubuta ta da Nigerian Port Authority sannan kuma ake taƙaita ta da NPA a Turance. Reshe ce ta Hukumar Sufuri (Federal Ministry of Transport) a Gwamnatin Jamhuriyar Tarayyar Najeriya. Ita ke da alhakin shugabanta tare kuma da gudanar da dukkan harkokin da suka shafi sufuri ta cikin ruwa a Najeriya wanda ke da tashoshin jiragen ruwa guda shida da suka haɗa da: tashar jirgin ruwa mai matsugunni a Apapa (Lagos Port Complex) a Lagos; tashar jirgin ruwan Tsibirin Tinkan (Tin Can Island Port Complex) a Lagos; tashar jirgin ruwa ta Kalaba (Calabar Port Complex) a jahar Cross River; tashar jirgin ruwa ta Delta wadda take Warri (Delta Ports) a jahar Delta; tashar jirgin ruwa ta Rivers (Rivers Port Complex) da tashar jirgin ruwa ta Onne (Onne Port Complex) waɗanda suke a jahar Rivers.

 Babban jami’in da ke kula da wannan hukuma shi ake kira Managing Director a Turance wanda kuma ake taƙaiwa da MD. A halin yanzu (2020), Hajiya Hadiza Bala Usman ke riƙe da wannan muƙamin tun daga shekarar 2016 biyo bayan naɗa ta da shugaba Muhammadu Buhari ya yi a ranar litinin 11 ga watan Juli (July) na shekarar 2016.

Asali

Ana danganta tarihin kai-komo ta cikin ruwa da shigowar Turawa yankunan da a yanzu suka kafa ƙasar Najeriya. Amma duk da haka ana la’akari da shekerar 1909 a matsayin shekarar dasa tushen maka-makan tashoshin jiragen ruwan da ake da su yau a Najeriya.

Tun kafin wannan shekara ta 1909, Turawan Mulkin mallaka sun yi amfani da ruwan garin Badagry wanda a yanzu garin yake ƙarƙashin Jahar Lagos da ke Kudu Maso-Yammacin Najeriya a matsayin babban tashar da suke tattara bayi da sauran kayayyakin fataucin su zuwa Turai a duk faɗin Afirka ta Yamma (Mann, 2007).


Mashigar Tashar Jirgin Ruwa ta Apapa
Hoto: Port Strategy

Amma a shafinta na Intanet, Hukumar Jiragen Ruwan ta ce: “Aiwatarwa da kuma haɓakar harkokin tashar jirgin ruwa  a Najeriya ta fara a tsakiyar ƙarni na goma sha tara (19th centuary). Yunƙurin samar da kayayyakin aikin zirga-zirgar manya-manyan jiragen ruwa ya fara ne da buɗe Kogin Lagos (Lagos Lagoon) a farko shekarar 1909. An kuma tabbatar da haɓɓaka tashar jirgin ruwa ta Apapa zuwa makekiyar tashar jirgin ruwa a shekarar 1913 aikin da aka fara shi a shekarar 1921”.

Saboda haka kenan, tushen wannan harka ta sufurin jiragen ruwa a Najeriya, shi ne fitar da bayi da sauran kayayyakin da Turawa ke safarar su zuwa Turai.

Shafin Intanet

Hukumar Ilimin Najeriya tana da shafin Intanet. Latsa nan ka tsunduma cikin wannan shafi.

Manazarta


Mann K. (2007). Slavery and the Birth of an African City Lagos, 1760–1900. Indiana University Press Bloomington and Indianapolis.

Nigerian Port Authority (2020). History. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://nigerianports.gov.ng/history/


Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya

Tarihin Najeriya


Alamomi da Tambari

Hukumomi da Rasssan Gwamnati


Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub