Me ka ke nema?


Shafin Farko

'Yan Ƙasanci a Nijeriya


Gabatarwa

Kowace ƙasa a duniya, tana da wasu keɓantattun mutane waɗanda suke zama ‘ya’yan wannan ƙasa. Ƙari a akan haka kuma tana da dokoki da ƙa’idojin da ke bata damar mayar da ɗan wata ƙasar ya zama nata.

Sannan kuma dukkan wata ƙasa tana da wasu haƙƙoƙi nata da suka rataya a wuyan ‘ya’yanta kamar yadda suma dole suke da wasu haƙƙoƙin da suka rataya a wuyanta.

Wannan rubutu yana son yin magana ne game da ‘yanƙasanci, ɗan ƙasa da kuma haƙƙoƙin ƙasa da na ‘yan ƙasa a Nijeriya. Muna fata wannan rubutu ya zama jagoran buɗe idanuwan ‘yan Nijeriya su fahimci nauye-nauyen da suke wuyan su a matsayin su na ‘yan ƙasa da kuma nasu nauye-nauyen da yake wuyan ƙasar domin kowa ya kiyaye a samu zaman lafiya, lumana arziƙi da kuma kwanciyar hankali.

Ma’anar Ɗan Ƙasa

Makirosoft Encarta (2009), ya siffata ɗan ƙasa da faffaɗar ma’ana ta ɗaiɗaikun mutane da suke a matsayin mambobin wata ƙasa; wato mutumin da ya miƙa wuyansa (Ya yi wa ƙasa mubaya’a), kuma wanda yake da haƙƙin neman kariya daga gwamnatin wata ƙasa.

‘Yan Ƙasanci

‘Yan ƙasanci shi ne dangantaka tsakanin ɗaiɗaikun mutane da kuma ƙasar da mutum ya yi wa mubaya’a (Miƙa wuyansa gare ta) wanda a sakamakon yin haka shi kuma yake neman kariya daga gareta. ‘Yan ƙasanci na nufin matsayin ‘yanci wanda yake tattare da wasu ɗawainiyoyi (Britannica, 2010). Misali, dukkan ɗan ƙasa yana da wasu haƙƙoƙin da suka rataya a wuyansa na ƙasa da ya sauƙe, sannan kuma shi ma yana da nasa haƙƙoin da suka rataya a wuyan ƙasarsa da suka zama dole ta sauke masa kamar yadda za mu zayyano waɗanda suka shafi Nijeriya a nan ƙasa.

Wanenen Ɗan Nijeriya?

Nijeriya a matsayinta na ƙasa, tana da rukunan ‘yan ƙasa guda uku; haifaffen ɗan ƙasa, ɗan ƙasa ta hanyar rijista; ɗan ƙasa ta hanyar canjin asali. Ɗaya daga cikin waɗannan ukun; wato ɗan da ta haifa daga cikinta, shi ne ya fi kowane daraja. Bari mu ji daga bakin Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya:

Haifaffen Ɗan Ƙasa

Haifaffen ɗan ƙasa a Nijeriya nau’uka biyu biyu ne waɗanda kuma suka kasance ƙwaya uku; akwai ƙwaya biyu a cikin nau’in farko kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya zayyana:

  1. A rukunin farko na haifaffun ‘yan ƙasar Nijeriya akwai muta ne biyu; na farko shi ne duk mutumin da aka haifa kafin ranar ‘yancin kai (1 ga watan Oktoba, 1960), tare da sharaɗin zamowar ɗaya daga cikin mahaifansa ko kakaninsa ɗan asalin wata ƙabila daga cikin ƙabilun Nijeriya kamar yadda aka tanada a tanadi mai lamba (a) na ƙaramar doka mai lamba (1) ƙarƙashin sashe na 25 a cikin babi na III na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999. Sai kuma na biyu wanda shi ne duk wani mutumin da aka haifa a Nijeriya bayan ranar ‘yancin kai (1 ga watan Oktoba, 1960) tare da sharaɗin zamowar ɗaya daga cikin iyayensa ko kakaninsa ɗan Nijeriya kamar yadda aka tanada a tanadi mai lamba (b) na ƙaramar doka mai lamba (1) ƙarƙashin sashe na 25 a cikin babi na III na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999.
  2. Rukuni na biyu na haifaffen ɗan Nijeriya shi ne duk mutumin da aka haifa a ƙasar waje tare da sharaɗin cewa ɗaya daga cikin iyayensa ɗan Nijeriya. Kamar yadda aka tanada a tanadi mai lamba (c) na ƙaramar doka mai lamba (1) ƙarƙashin sashe na 25 a cikin babi na III na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999.

Ranar ‘Yancin Kai: Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya bayyana ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960 a matsayin ranar ‘yancin kai. Kamar yadda aka yi bayani a ƙaramar doka mai lamba (2) ƙarƙashin sashe na 25 a cikin babi na III na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999.

Ɗan Ƙasa Mai Rijista

A Nijeriya, mutum yana iya zama ɗan ƙasa ta hanyar yin rijista, bisa tanade-tanaden sashe na 28, ƙarƙashin babi na III na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 bayan cika wasu sharruɗan da suka zo a tanade-tanade masu lambobi (a), (b) da kuma (c) na ƙaramar doka mai lamba (1) ƙarƙashin sashe na 26 a cikin babi na III na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999:

  1. Ya zama mutum nagari (Mumutin kirki);
  2. Ya bayyana a fili cewa yana son zama a Nijeryia;
  3. Ya yi rantsuwar Mubaya’a kamar yadda aka bayyana ta a rataye na bakwai na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.

Mubaya’a

Ni……………………. Na rantse, na tabbata cewa tsakani da Allah zan kasance mai cikakkiyar biyayya ga Tarayyar Jamhuriyar Nijeriya, kuma zan mutunta, tsare, sannan kuma na kare Tsarin Mulkin Tarayyar Jamhuriyar Nijeriya.

Ya Allah ka taimake ni.

Mutane biyu ne za su iya cin wannan gajiyar, kamar yadda tanade-tanade masu lambobi (a) da (b) na ƙaramar doka mai lamba (2) suka zayyana a ƙarƙashin doka mai lamba 26 a babi na III na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999: Akwai matar da take aure ko taɓa aurar wani ɗan Nijeriya (Haifaffe) da kuma baligi ko baliga da aka haifa a wata ƙasa idan kakaninsa ‘yan Nijeriya ne tare da cika sharruɗa uku da aka zayyano a sama.

Ɗan Ƙasa Mai Canjin Asali

Sashe na 27, ƙaƙashin babi na III na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, ya bayar da damar cewa mutum zai iya zama ɗan Nijeriya ta hanyar canjin asali kamar yadda aka yi bayani a ƙaramar doka mai lamba (1) a wannan sashe, tare da kiyaye tanade-tanaden sashe na 28 babi na III na Kudin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999.

Ƙaramar doka mai lamba (2) ta sashen na 27 ƙaƙashin babi na III na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, ta bayyana waɗannan sharruɗa a matsayin sharruɗan da mutum zai cika kafin ya samu amincewar Shugana ƙasa a bashi takardar shedar canjin asali:

  1. Ya zamo baligi cikakke;
  2. Ya zama mutumin kirki, mai kyawawan halaye;
  3. Ya bayyana a fili cewa yana son zama a Nijeryia;
  4. Ya samu amincewar Gwamnan jahar da yake son zama a ciki bisa fahimtar cewa yana son zama a cikin jama’ar da ke yankin kuma cewa ya samu karɓuwa a wajensu sannan kuma ya saba da salon rayuwarsu;
  5. Mutum ne shi da ya bayar da ko kuma yake son bayar da gagarumar gudunmawa wajen haɓɓakawa tare kuma da bunƙasa zaman lafiya a Nijeriya;
  6. Ya yi rantsuwar Mubaya’a kamar yadda aka bayyana ta a rataye na bakwai na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya;
  7. Sannan ya kasance tun kafin ya rubuta takardar neman shedar ya:

(i). Mazaunin Nijeriya ne sama da tsawon shekaru 15 da suka gabata ba tare da yankewa ba;
(ii). Ya zauna a Nijeriya tsawon shekara guda cur ba tare da yankewa ba sannan kuma idan aka tattara zaman da ya yi a tsittsinke a Nijeriya a cikin shekaru 20 da suka gabata zai iya kaiwa adadin shekaru 15 ba tare da tsittsinkewa ba.

Zama Ɗan Ƙasashe Biyu

Sashe na 28, babi na III na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, ya bayyana cewa:

  1. Mutum yana iya rasa damarsa ta zamowa ɗan Nijeriya nan take idan ya yi rijista da wata ƙasar a matsayin ɗan waccar ƙasar matuƙar dai shi ba haifaffen ɗan Nijeriya ba ne sannan kuma ba haifaffen ɗan waccar ƙasar ba ne.
  2. Duk mai son zama ɗan Nijeriya ta hanyar rijista ko canja asali, dole ya saki damarsa ta zama ɗan wata ƙasa matuƙar dai ba ƙasarsa ce ta haihuwa ba da watanni 12 bayan ya karɓi rijista ko takardar shedar zama ɗan Nijeriya.

Watsi da Damar Zama Ɗan Ƙasa

Sashe na 29, babi na III na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya bayyana ƙananan dokoki masu labobi (1), (2) da kuma (3) wadda itama ta yi rassa (a) da (b) da za suka bai wa ɗan ƙasa damar watsi da damarsa ta zama ɗan Nijeriya. Cewa:

  1. Duk baligin da yake son watsi da damarsa ta zama ɗan Nijeriya zai iya yin hakan ta hanyar shela a kafar da ta dace;
  2. Da zarar shugaban ƙasa ya gamsu, ya kuma bayar da sanarwar watsi da wannan dama, shike nan, wanda ya yi shelar ya zama ba ɗan Nijeriya ba;
  3. Shugaban ƙasa yana da damar ƙin amincewa da wannan wannan shela ida:

(a) Idan an yi shelar ne a lokacin da Nijeriya take cikin halin yaƙi;
(b) Ya fahimci cewa shelar ta saɓa ƙa’ida.

  1. Abin da ake nufi da Baligi a Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, babi na III, sashe na 29 ƙaramin sashe na (4) shi ne: Duk mutumin da ya kai shekaru 18 zuwa sama ko kuma duk mace da aka yi wa aure.

Hana Damar Zama Ɗan Ƙasa

Sashe na 30, babi na III na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, ya bayyana wasu yanayi a ƙananan sashina na (1) da (2) wanda shima ya yake da rassa (a) da (b) da cewa shugaban ƙasa yana da damar haramtawa duk mutumin da haifaffen ɗan Nijeriya ci gaba da zama ɗan Nijeriya idan:

  1. A tsawon shekaru bakwai da ya yi a matsayin ɗan Nijeriya kotu ta ɗaure shi tsawon shekaru uku;
  2. Idan aka gano cewa: (a) Yana wasu ayyuka ko maganganun da suke nuna ƙin jinin gwamnatin Tarayya ko kuma (b) An kama shi ya yi cinikin bayan fage, ko ya shiga wata ƙasa ta abokan gaba ba bisa ƙa’ida ba domin ya yi wa Nijeriya zagon ƙasa.

Cancantar Zama Ɗan Nijeriya 

Sashe na 31, babi na III na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, ya ce ana ɗaukar zamowar ɗaya daga cikin iyaye ko kakannin mutum a matsayin haifaffen ɗan Nijeriya idan har mutumin da aka haifa ɗin (Iyaye ko kakanni) yana raye a ranar ‘yancin kai (Ranar 1 ga watan Oktoba, 1960).

Haƙƙoƙin Ƙasa a Kan Ɗan Ƙasa

A matsayinka na ɗan ƙasar Nijeriya, ƙasa tana da wasu haƙƙoƙin da suka rataya a wuyanka ka sauke mata. Sashe na 24, Babi na II na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya ce haƙƙi ne a kan kowane ɗan ƙasa ya:

  1. Ya bi dokokin Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, ya girmama tutar ƙasa, taken ƙasa tare kuma da kiyaye dukkan alƙawarun da ya yi wa ƙasa da kuma hukumomin da doka ta kafa;
  2. Ya yi dukkan iya bakin ƙoƙarinsa wajen ɗaukaka kyakkyawan sunan da Nijeriya take da shi tare kuma da kare shi, sannan kuma ya zama mai mutunta gayyatar da ƙasa ta yi masa na bayar da gudunmawa ta fannin aiki a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso;
  3. Ya zama mai kiyaye mutunci, haƙƙoƙi da kuma buƙatun halas na sauran ‘yan ƙasa da kuma zama lafiya tare da juna,
  4. Ya bai wa al’ummar da yake cikinta nagartacciyar gudunmawa tare kuma da kare lafiyarsu;
  5. Ya tallafawa dukkan hukumomin da abu ya shafa wajen ganin an tabbatar da zaman lafiya da kiyaye doka da oda;
  6. Ya bayyana haƙiƙanin samunsa tare kuma da biyan haraji ga hukumomin da abin ya shafa.

Haƙƙoƙin Ɗan Ƙasa na Wajibi

A matsayinka na ɗan Nijeriya, kana da haƙƙoƙi na wajibi a kan ƙasarka waɗanda Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa ya baka.

Babi na IV na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya bayyana wasu haƙƙoƙi na ɗan ƙasa a wuyan Gwamnatin Tarayya. Kamar irin su ‘yancin rayuwa, mutuntaka da sauran su.

‘Yancin Rayuwa

Babi na IV na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na shekarar 1999, ya fayyace wasu haƙƙoƙi da kuma damammaki da dukkan ɗan Nijeriya yake da damar cin moriyarsu a matsayin manyan haƙƙoƙinsa. Daga ciki akwai ‘yancin rayuwa, mutuntaka, walwala, faɗin albarkacin baki, damar yin addini, kiyaye sirrinsa, damar mallakar kadara kamar ƙasa da sauran su. Gasu kamar haka:

Sashe na 33 (1) da (2) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, sun yi bayanin cewa: Kowane mutum yana da ‘yancin rayuwa a Nijeriya ba tare da an raba shi da ransa bisa ganganci ba sai dai da dalili na shari’ar. Sannan kuma ba a la’akari da cewa an raba mutum da ransa da gangan idan har an yi amfani da ƙarfin da shari’a ta yarda da shi domin:

Sannan kuma idan a ƙoƙarin shari’a na amfani da ƙarfi wajen kare rayuwar wani mutum ko dukiya daga ta’addanci ko kuma ƙoƙarin kama mutumin da yake yunƙurin kuɓuta daga tsarewar da shari’a ta yi masa ko kuma a yunƙurin shari’a na daƙile wata zanga-zanga ko tarzoma ko tawaye ta kai ga an kashe mutum, to wannan ba kisan ganganci ba ne, Sashe na 33, ƙaramin sashe na (1) da (2) da kuma tanade-tanade (a), (b) da (c) na ƙaramin sashe na (2) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999.

‘Yancin Mutuntaka

Sashe na 34 na Kundin tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, ƙaramin sashe na (1) (a), (b), (c) da kuma ƙaramin sashe na (2) (a), (b), (c), (d) da (e) da kuma sauran tanade-tanaden su sun tanadi cewa:

Kowane mutum yana da haƙƙin a mutunta shi, kar a gana masa azaba, kar a wulaƙanta shi, kar a tozarta shi, kar a tsare shi cikin bauta ko aikin bauta, kar a tilasatawa mutum yin wani aiki.

Sai dai, ayyukan da kotu ta saka mai laifi ya yi, ayyukan da ake saka rundunar mayaƙa da na ta tsaro (Sojoji, ‘yan sanda da sauransu) su yi a wajen aikin su, ayyukan da ake saka waɗanda suka soki aikin soja, dukkan ayyukan da za a yi domin kare ƙasa daga wata barazana kamar yaƙi ko annoba, ayyukan gayya da jama’a ke yi domin amfanin kansu, ɗamarar rundunar sojan Nijeriya da kuma ayyukan da suka shafi bayar da ilimi duk ba a ɗaukar su a matsayin ayyukan tilas.

‘Yancin Walwala

Sashe na 35, Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, ya bayyana cewa:

  1. Kowane mutum yana da damar sakata ya wala tare kuma da watayawa ba kuma tare da an ce da shi domin ne ba. Sai dai, akwai iyakoki:
    • Idan kotu ta kama shi da laifi tare da yanke masa hukunci;
    • Idan ya ƙi bin umarnin kotu ko kuma tabbatar da wani nauyi da kotu ta ɗora masa;
    • Zargin aikata laifi, tsawatarwa game da wani laifi da ya aikata da kuma ajiya bisa umarnin kotu;
    • Domin ilimantar da shi ko kyautata rayuwarsa idan bai kai shekaru 18 ba;
    • Gudun yaɗa cuta, taɓin hankali, shan ƙwaya, shan giyar da ta wuce ƙima, mai yawon banza. Za a tsare su domin kare lafiyar sauran jama’a da kuma tasu;
    • Domin a hana mutum shigowa ko fita daga Nijeriya ko kuma a shigar da shi ko fitar da shi ta dalilin kora bisa tanadin shari’a.

    Dukkan waɗannan shari’a za ta iya hana su wancan ‘yanci na walwala. Amma duk da haka, dokar kanta ba ta da damar tsare mai zama jiran shari’a sama da wa’adin da idan aka kama shi da laifi zai yi a tsare. Misali, idan laifi yana da hukunci kwana uku a tsare, to doka ta hana a tsare wanda ya aikata wannan laifin da sunan jiran shari’a na tsawon kwanaki huɗu.
  2. Ba dole ba ne mutumin da aka kama ya yi magana ko ya amsa tambayoyi har sai ya shawarci lauyansa ko kuma duk mutumin da yake so.
  3. Dole ne a sanar da mutumin da aka tsare dalilin da ya saka aka kama shi kuma a cikin yaren da yake iya fahimta a rubuce kuma cikin awanni ashirin da huɗu.
  4. Duk mutumin da aka kama aka tsare, to dole a gurfanar da shi a gaban kuliya a kan-kari. Idan kuma ya kai tsawon watanni biyu ko uku ba tare da an bayar da belin sa ba, to dole a sake shi ba tare da sharaɗi ko gurfanar da shi gaban kotu ba idan har an kama shi ne bisa tanadi mai lamba (c) na ƙaramin shashe na (1) na babban sashe na 33 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999. Sai dai, hakan bata hana a sake kai ƙararsa.
  5. Abin da ake nufi da kan-kari a nan shi ne a kai mutumin kotun da take da damar sauraran ƙararrakin irin laifin da ake tuhumarsa da shi a cikin kwana ɗaya idan har akwai kotun a tazarar da ba ta haura kilomita arba’in ba. Idan ya haura, to cikin kwanaki biyu.
  6. Idan aka tsare mutum ba bisa haƙƙi ba, to dole a biya shi diyya tare kuma da roƙon afuwarsa daga wanda alhakin tsarewar ya rataya a wuyansa.
  7. Idan aka kama mutum bisa tanadin ƙaramin sashi na (1) (c), to wannan babu komai. Haka nan ma idan wani tsare soja ko ɗan sanda ko wani jami’in tsaro bisa laifin da ya aikata, to ba a taka doka ba.

‘Yancin Saurare da Adalci a Kotu

  1. Sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, ya bayyana cewa kowane mutum yana da haƙƙin a saurare tare kuma da yi masa adalici a kotu ko kuma wata hukumar sauraren ƙorafi, idan yana neman haƙƙinsa a hannun kowanene ciki kuma har da hukuma.
  2. Amma duk da haka wannan dama ba za ta hana wata doka yin aikinta ba domin an bai wa wata hukuma damar yanke hukunci kan wata maganar da ta shafi ‘yancin wani matuƙar dai:
  3. Shi mutumin da aka taɓa ‘yancin nasa ko za a taɓa ‘yancin nasa yana da damar shigar da ƙara;
  4. Cewa kuma hukuncin wannan hukuma ba shi ne na ƙarshe ba akwai dama ta ɗaukaka ƙara.
  5. Cewa kuma kotun ko kuma hukumar da za ta saurari ƙarar za ta bi diddigin maganar da aka ambata a ƙaramin sashe na (1) na sashe na 36 da na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ne a bainar jama’a.
  6. Duk wanda ake tuhuma yana da haƙƙi a yi masa shari’a a bainar jama’a kuma cikin lokaci sai dai idan an janye tuhumar da ake yi masa.

Amma duk da haka, kotu tana iya hana mutane shiga kallon ƙarar saboda tsaron dukiya, rayuka da kuma lafiyar jama’a. Sannan kuma idan wani minister ko kwamashinan jaha ya nuna rashin gamsuwarsa da bayyana a gaban kotu a bainar jama’a domin bayar da shaida, to kotu sai ta shirya yadda za ta karɓi shaidar tasa tare kuma da ɓoye sirrin bayanai.

  1. Idan laifi bai tabbata, to wanda ake tuhuma ya zama salihi. Sannan kuma ba zai yiwu a taka doka ba wajen neman wanda ake tuhuma ya kawo shaidu.
  2. Idan ana tuhumar mutum da laifi, to haƙƙinsa a sanar da shi irin laifin da ake zarginsa da shi; a bashi isasshen lokacin da zai kare kansa; a bashi dama ko kuma lauyansa ta yin tambayoyi ga abokan shari’asa a kotu da kuma damar kiran shaidunsa a kotu su zo su bayar da shaida a kansa; a bashi tafinta kyauta idan har baya jin yaren da kotu ko hukumar sauraren ƙararraki take amfani da shi.
  3. Wanda aka yi wa shari’a yana da ‘yancin karɓar bayanan da kotu ta adana a lokacin gudanar da shari’a a cikin kwana bakwai da yanke hukunci.
  4. Ba za a hukunta duk wanda ya aikata wani lafin da a lokacin da ya aikata babu wata doka da hana aikata wannan lafin ba, sannan kuma ba za a yi hukunci sama da horon da doka ta tanada a lokacin da aka aikata lafin ba.
  5. Idan kotu ta sallami mutum bisa wani laifi, to ita wannan kotun bata da hurumin sake kama mutum a kan wannan laifin ko kuma wani laifi da ya shafi na farkon ba sai dai bisa umarnin kotun gaba da ita.
  6. Idan aka yi wa mutum afuwa a kan wani lafi, to ba za a sake kai shi ƙara gaban kotu a kan wannan laifin ba.
  7. Ba za a tilastawa wanda ake tuhuma da laifi a gaban kotu cewa dole ya bayar da shaida a kan wannan lafin ba.
  8. Babu wata doka da za ta hukunta wani idan dai ba ta Kundin tsarin mulkin 1999 ba ko kuma dokar Majalisar Tarayya, Jaha ko Ƙaramar Hukuma ko kuma wani bayani da aka yi a ƙarƙashin ikon wata doka.

‘Yancin Kiyaye Sirri

Duk ɗan Nijeriya yana da haƙƙi a kare masa sirrinsa a cikin abubuwan da suka shafi gida, hirarraki, saƙonnin waya, wasiƙa, Imel, telegiram da sauransu, kamar yadda sashe na 37 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ya bayyana.

‘Yancin Tunani, Ra’ayi da Addini

Sashe na 38 da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, ya bayyana cewa:

  1. Duk ɗan Nijeriya yana da ‘yancin yin tunani; rugunmar wani ra’ayi ko addini; canza addini ko abin bauta; bayyana ra’ayin addini a fili shi kaɗai ko tare da jama’a; yin wa’azi; yaɗa addini ko hanyar bauta; koyar da addinin da yake bi tare kuma da aikata shi.
  2. Ba za a koyar da ɗan makaranta wani addini ko a saka shi ya halarci taron addini wanda ba nasa ba ko kuma wanda ya saɓa da ra’ayin iyayensa ko na waliyansa.
  3. Duk ɗan Nijeriya yana damar kafa makaranta tare kuma da koyar da ‘ya’yansa mazaha ko wani addinin da yake bi.
  4. Wannan sashe bai bayar da ikon kafawa, hidimtawa ko kuma shiga ƙungiyar asiri ba.

‘Yancin Faɗin Albarkacin Baki da Yaɗa Labarai

Sashe na 39 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya bai wa kowane ɗan Nijeriya:

  1. Damar faɗin albarkacin baki, karɓar ra’ayi, yaɗa ra’ayi ko fitar da sanarwa ba tare da ƙaidi ba.
  2. Kowane mutum yana da ikon mallaka, kafawa ko gudanar da wata kafar sadarwa domin yaɗa labarai, dabara, aƙida ko ra’ayi. Sai dai, gwamnatocin Tarayya da Jahohi; ƙungiya ko ɗaiɗaikun mutanen da shugaban ƙasa ya bai wa izini ƙarƙashin dokar majalisa bayan sun cika sharruɗa, su kaɗai suke da ikon kafa tashohin radiyo datalabijin domin cimma kowane irin buri ne.
  3. Duk da haka kuma sashen bai bayar da damar taka dokar hana bayyana asirtaccen labari; dokar da tabbatar da ikon kotu; tafiyar da aikin wayar tarho; radiyo; talabijin ko nuna majigi ba. Haka nan ma ƙa’idojin da aka gindaya a kan ma’ikatan Gwamnatin Tarayya ko na Jahohi; rundunar mayaƙan Nijeriya; rundunar ‘yan sanda; da kuma sauran jami’an, ko kuma wata doka da aka kafa ƙarƙashin wata doka, sashen bai bayar da damar a taka dukkan waɗannan dokoki ba.

‘Yancin Kafa Ƙungiya da Gudanar da Taro

Sashe na 40 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya bai wa duk wani ɗan Nijeriya damar kafawa da kuma shiga ƙungiya; gudanar da taro; shiga da kuma kafa jama’iyyar siyasa; shiga ƙungiyar ƙwadago da ma duk ƙungiyar da yake da ra’ayin kafawa ko shiga domin kare manufofinsa. Tare kuma da kiyaye cewa, abubuwan da sashen ya tana da basu ci karo da ikon da Kundin ya bai wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kant aba.

‘Yancin Zama

Sashe na 41 da na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya bayyana cewa:

  1. Duk ɗan Nijeriya yana damar zama da kuma yawo a duk ɓangaren da yake so. Sannan kuma babu ɗan Nijeriya da za a kora; hana shigowa ko fita daga cikinta matuƙar dai yana son yin hakan.
  2. Ƙaramin sashe na (1), sashe na 40 bai yi tanadin rushe dokar da aka gindaya game da zama ko walwalar wani mutumin da ya aikata wani laifi ba domin hana shi gudu daga ƙasa; bai hana a ingiza ƙeyar wani ɗan Nijeriya zuwa wata ƙasa ba domin fuskantar hukunci a can  matuƙar dai akwai kyakkyawar fahimtar juna a tsakanin ƙasar da Nijeriya.

Haramcin Danniya

Sashe na 42 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, ya bayyana cewa:

  1. Ya zuwa yanzu, ba a tanadi wata doka da za ta kange wata al’umma ko ƙabila aiwatar da wani abu da ba a hana ba a dokance ko kuma bisa umarnin Gwamnati aiwatar da wani abu da ya shafi addini; ƙabila; ra’ayi;  jinsi; ko kuma ra’ayin siyasa ba. Haka nan ma babu wata doka ko umarnin Gwamnati da ya tanadi cewa a fifita wani mutum; wata ƙabila; mahaifa; jinsi; jama’iyyar siyasa ko addini ba sama da saura.
  2. Doka ta hana a muzgunuwa wani ko a dannen masa haƙƙi saboda wani dalili na haihuwa.
  3. Haka nan wannan sashe bai tanadi wata dokar da ta hana aza takunkumin naɗa wani mutum da ya samu nasarar hawa karagar wani muƙamin Gwamnati ko rudunar mayaƙan ƙasa ko ta ‘yan sanda ko wani aikin hukuma da ya yake kan doron doka ba.

‘Yancin Mallakar Kadara Maras Motsi

Sashe na 43 Na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, ya bai wa kowane ɗan Nijeriya damar mallakar kadara masar mosti a ko’ina a faɗin ƙasa.

Malakkar Dukiya da Ƙarfi

Sashe na 44 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, ya tanada cewa:

  1. Ba za karɓi dukiya mai motsi da maras motsi ko ribar dukiyar bisa ƙarfi ba haka nan ma kuma mallakar dukiyar. Sai dai idan doka  ta:
  2. Buƙaci dole a biya wani diyyar dukiyarsa da aka karɓe;
  3. Bai wa mai dukiyar damar kai ƙara kotu ko kuma wata hukumar sauraren ƙararraki domin a tabbatar masa haƙƙinsa ko kuma yawan diyyar da za a biya shi.
  4. Dokar ƙaramin shashe na (1) na sashe na 44 ba ta hana aiwatar da wata doka da shafi:
  5. Ɗora haraji ko kuɗin fito tare da karɓar su ba;
  6. Kotu ta karɓe wani abu ba domin laifin karya doka wadda ka iya zama sanadiyar tabbatar da haƙƙi ne ko karya doka;
  7. Karɓar dukiyar da ta shafi izinin hayar fili, hayar gini, jiginar gini ko fili da kuma sauran haƙƙoƙin da suka shafi yarjejeniya;
  8. Karɓar dukiyar mutumin da kotu ta yadda cewa shi turu ne na bashi, ko kuma taɓaɓɓe ne, ko dukiyar gado, ko dukiyar ƙungiyoyi da kamfanonin da ake son rufe su;
  9. Karɓar dukiyar da ta shafi yanke hukunci ko wani umarnin kotu;
  10. Karɓe mallakar wata kadarar da ta taso wa lalacewa ko ta zama haɗari ga rayuwa da lafiyar jama’a ko lafiyar shuke-shuke ko dabbobi;
  11. Karɓe dukiyar da ta shafi abokan gaba; dukiyar amana da masu riƙe da ita; nuna iyakar kai wa ƙara; dukiyar da ke hannun hukumomin da doka ta kafa su a Nijeriya; karɓar wani ginin zuwa wani wa’adi domin gudanar da jarrabawa ko bincike ko bin sawu; ikon karɓar wani fili domin yin aikin da zai kare zaizayar ƙasa da kuma;
  12. Dokar da ta tanada wa hukuma ko wani mutum ikon shiga; yin safiyon fili; haƙa rami; shimfiɗa waya; kafa turakun waya; kafa waya; dasa bututu; ko kuma duk wani abu da ya shafi kafa wani abu a doron ƙasa domin a samu wutar lantarki; manfetur; ruwa; magudanar ruwa; wayar sadarwa; ayyukan amfanin jama’a matuƙar dai an biyya diyyar gine-gine, itatuwa ko kuma shuke-shuke nan-take.
  13. Gwamnatin Tarayya ce kaɗai take ikon mallakar dukiyar ma’adanai da suke a doron ƙasa, ƙarƙashin ƙasa, ƙarƙashin ruwa ko bisa ruwan gaɓar tekunan Nijeriya da gaɓoɓin tekunan Nijeriya da suka shafi albarkatun mai da iskar gas kuma Majalisar Dokoki ta ƙasa ita za ta yi dokar da za ta bayar da damar sarrafa su.

Hurumin Manyan Haƙƙoƙi

Duk da irin waɗannan damammaki, haƙƙoƙi da kuma ‘yan ci da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya bai wa ‘yan ƙasa, ya kuma iyankance cewa:

  1. Manya-manyan sashe 37, 38, 39, 40 da kuma 41, ba za su soke wata doka da aka kafa bisa manufar dimokuraɗiyya ba domin a tabbaratar da tsaron ƙasa, lafiyar jama’a, zaman lumana, kare mutuncin jama’a, ko kuma kiwo lafiya jama’a; ko kuma domin kare haƙƙi ko ‘yancin wasu mutane.
  2. Ba za a soke dokar Majalisar Tarayya ba ko kuma ɗaukar matakan da za su saɓa da sashe na 33 da 35 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 a lokacin da ƙasa ta faɗa bala’I, sai dai idan an tabbatar da cewa ɗaukar matakin zai magance halin da ake ciki.

Kuma duk da haka, babu wani batu na wannan sashe da zai soke tanade-tanaden sashe na 33 sai dai rashi da wanda yaƙi ya haddasa ko kuma wani batu da zai soke ƙaramin sashe na (8) na babban sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999.

  1. Abin da ake nufi da lokacin bala’i a nan shi ne lokacin shugaban ƙasa ya kafa dokar-ta-ɓaci bisa ikon da sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya bashi.

Dama ta Musamman

Sashe na 46 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya bai waɗ an Nijeriya wasu damammaki na musamman da cewa:

  1. Duk mutumin da yake zargin cewa an taka wata ƙa’ida ko an keta masa haddi kan wani lamari da ya shafe shi ko kuma akwai yiwuwar a keta masa haddi a babi na IV na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, kuma a kowace jaha ce daga cikin jahohin Nijeriya to zai iya garzayawa Babbar Kotu ya kai kokunasa domin a bi masa haƙƙin nasa.
  2. Babbar Kotu tana da damar sauraren ƙara tare da yanke hukunci a karon farko, ta kuma bayar da umarni, takardun umarni bisa yadda ya dace domin a aiwatar ko a tabbatar da umarnin nata game da haƙƙin mutumin da ya kai ƙasa a iya faɗin Nijeriya a kan wani batu da aka yi magana a sashe na 46 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999.
  3. Alhakin zayyana ƙa’idojin da Babbar Kotu za ta yi aiki da su wajen aiki da wannan sahshe yana wuyan Babban Alƙalin Nijeriya.
  4. Haka nan kuma Majalisar Tarayya tana iya ƙara wa Babbar Kotu ƙarfin ikon da ta ga ya dace domin aiwatar da ikon da sashe na 46 da ya bata, Sannan kuma kotun ta samu damar bai wa wanda aka tauye wa haƙƙin da Babi na IV na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya bashi  taimakon kuɗin da zai samu ya ɗauki lauyan da zai nema masa haƙƙin tare da tabbatar da cewa an tantance zargin danne haƙƙin sannan kuma an samu taimakon kuɗi tare da ɗaukar lauya.

Manazarta


Encyclopædia Britannica (2010). Citizenship. Encyclopaedia Britannica Ultimate Reference Suite, Chicago.

Microsoft Encarta (2009). Citizen. Microsoft Student 2009 [DVD]. Redmond, WA: Microsoft Corporation, 2008.



Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya

Tarihin Najeriya


Alamomi da Tambari

Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub