Alhaji Muhammad Seyoji Ahmad

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Alhaji Muhammad Seyoji Ahmad


Gabatarwa


Mai Martaba Sarkin Pindiga
Alh. Muhammad Seyoji Ahmad

Malamin makaranta, manomi kuma sarki, shi ne Alhaji Muhammadu Seyoji Ahmad, wanda ya zama sarkin yanka na farko a masarautar  Pindiga. Mutum ne shi mai sauƙin hali kuma jajirtacce wajen ganin jama’arsa sun ci gaba. Mutum ne mai kyakkyawar mu’amala tare kuma da sauƙin hali, mai karvar baƙi kuma mai son hidimtawa jama’arsa.

Ya yi karatu tun daga matakin firamare har zuwa digiri na farko. Sannan kuma ya zama malamin makaranta har zuwa matakin shugaban makaranta. Shi hakimi ne da farko kafin daga baya ya zama sarkin yanka na farko a wannan masarauta ta Pindiga.

Haihuwa

An haifi Mai martaba Sarkin Pindiga Alhaji Muhammadu Seyoji Ahmad, a garin Pindiga, a ranar 15 ga watan Agusta na shekarar 1956. Shi ɗa ne ga sarkin Pidinga Amadu Shu’aibu, wanda shi kuma Shu’aibu ɗa ne ga sarkin Pindiga Ibrahim na farko. Kenan shi ɗan sarki ne kuma jikan sarki. Sunan mahafiyarsa Hajiya A’ishatu wacce ita kuma ‘ya ce ga sarkin Kombani Isa Boɗewal; wato mahaifiyarsa bafilatana ce. sannan kuma shi Jukun ne ta vangaren mahaifi.

Karatu

Mai Martaba Sarkin Pindiga, Alhaji Muhammadu Seyoji Ahmad, ya yi makarantar firamare a santaral firamare (Pindiga Central Primary School) ta garin Pindiga daga shekarar 1963 zuwa 1969. Daga nan kuma sai ya samu nasarar shiga kwalejin Sheikh Sabbah da ke Kaduna (Sardauna Memorial College), daga shekarar 1970 zuwa 1974. Bayan kammala karatunsa na kwaleji, sai ya samu nasarar shiga babbar kwalejin horas da malamai (Advance Teacher’s College Sokoto) da ke Sakkwato wacce yanzu ta koma Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari (Shehu Shagari College of Education Sokoto), daga shekarar 1974 zuwa 1977, inda ya fita da takardar shedar karatu ta NCE. Ya kuma samu nasarar zuwa ƙasar Amurka inda ya samu digirinsa na farko a fannin ma’adanai da albarkatun ƙasa (Environmental Geology), daga shekarar 1981 zuwa 1983.


Mai Martaba Sarkin Pindiga
Alh. Muhammad Seyoji Ahmad

Gogaggayar Aiki

Bayan kammala karatunsa na NCE, Mai Martaba sarki ya fara da yiwa ƙasa hidima (NYSC), inda aka tura shi makarantar Girama ta Ise-Emure (Ise-Emure Grammar School), garin da ya kasance a cikin tsohuwar jahar Ondo wanda a yanzu kuma ya ke cikin jahar Ekiti. Ya yi wannan hidima daga 1977 – 1978.

Bayan kammala yiwa ƙasa hidima, ya samu nasarar shiga aikin koyarwa a ƙarƙashin ma’ikatar ilimi ta jahar Bauchi (Bauchi State Ministry of Education), inda aka tura shi makarantar sikandire ta Nafaɗa (GSS Nafaɗa) da ke cikin jahar Bauchi, a matsayin malamin makaranta kuma sannan mai riƙe da muƙamin mataimakin shugaban makaranta (Vice Principal). Mai martaba sarki ya yi aiki a wannan makaranta tun daga 1978 har zuwa 1981.

A shekarar 1981, mai marataba sarki ya samu nasarar zuwa ƙasar Amurka dan ƙarin karatu, inda ya samu zuwa jami’ar jahar Ohio da ke Columbus a cikin ƙasar Amurka. A wannan jami’a ya yi karatun digirinsa na farko a fannin ma’adanai da albarkatun ƙasa (Environmental Geology).

Bayan dawowarsa gida a cikin shekarar 1983, sai aka yi masa muƙamin shugaban makaranta (principal) a makarantar sikandiren Waɗe (GSS Waɗe) da ke cikin ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, ta tsohuwar jahar Bauchi.  

A shekarar 1984, ya samu gurbin ƙaro karatun digiri na biyu a jami’ar Bayero da ke Kano, a fannin albarkatun ƙasa. Amma cikin hukuncin Allah mai martaba sarki bai samu damar zuwa wannan ƙaro karatu ba saboda rasuwar mahaifinsa, rasuwar da ita ta sabauta zamowarsa sarki amma da muƙamin hakimin Pindiga.

Zamowarsa Sarki

Tun kafin zamowarsa sarkin yanka, Mai martaba sarki ya fara da riƙe muƙamin hakimin Pindiga, muƙamin da ya riƙe na tsawon shekaru goma sha shida 1984 zuwa 2000. An yi masa wannan naɗi na hakimin Pindiga a ranar Juma’a 10 ga watan Agusta na shekarar 1984 bayan rasuwar mahaifinsa.

Bayan ɗaukaka darajar wannan ƙasa ta hakimin Pindiga daga matsayin hakimi zuwa sarkin yanka, wanda aka yi a cikin watan Nuwamba na shekarar 2000, a zamanin gwamnan farar hula na farko a jahar Gombe, wato Alhaji Abubakar Habu Hashidu, sai shima mai martaba sarki matsayinsa ya ɗaukaka daga hakimi zuwa sarkin Yanka mai daraja ta biyu. Wannan naɗi shi ya saka shi ya zama sarkin yanka na farko da ya fara zama a kan kujerar sarautar Pindiga a matsayin sarki yanka.

Bayan cikar mai martaba sarki shekara guda a wannan kujera, sai aka yi bikin bashi sandar sarauta a ranar 14 ga watan Yuli na shekarar 2001.

A haka mai martaba sarki ya ci gaba da zama a kan wannan kujera har zuwa shekarar 2003, shekarar da aka sake gudanar da zaven gwamnoni, zaven da ya gusar da shi gwamna Abubakar Habu Hashidu daga kujerar gwamna ya kuma ɗora gwamna Mohammed Ɗanjuma Goje.

Bayan hawan gwamna Mohammed Ɗanjuma Goje kan kujerar gwamnan Gombe, sai savanin siyasa ya shiga tsakaninsa da mai martaba sarki, abin da ya sabauta cire mai martaba sarki daga wannan kujera da ya gada daga kakaninsa. Wannan lamari ya faru a ranar 12 ga watan Mayu na shekarar 2004. Wato a lokacin mai martaba sarki yana da shekaru ashirin kenan a kan kujerar sarautar Pindiga; wato tun daga 1984 zuwa 2004.

Bayan cire mai martaba sarki daga kan wannan kujera tasa, sai kuma aka tura shi zuwa gudun hijira a garin Tula, garin da ke cikin ƙaramar hukumar Kaltungo, duk a cikin jahar Gombe. Haka nan mai martaba sarki ya yi zaman wucin gadi, ba shi a nan-ba shi can, tsakanin Tula da Gombe, har tsawon shekara guda.

Bayan shekara guda da faruwar wannan lamari, sai mai martaba sarki ya samu cikakkiyar damar zama a gidansa da ke garin Gombe, inda ya zauna cikin haƙuri da kuma yadda da ƙaddara har tsawon shekaru tara da wata uku; wato tun daga 2004 har zuwa 2013.


Majalisar Mai Martaba Sarkin Pindiga

A lokacin wannan gudun hijira, abubuwa marasa daɗi sun faru daga ciki akwai a matakin farko da gwamnan ya ɗauka na tsare mai martaba sarki a wani gida a Gombe ba tare da yawo ba, abin da Bature ya kira ‘House arrest’; yanayin tsarewa ne da ake garƙame mutum a gida a hana shi zuwa ko’ina. A wannan mataki mai martaba sarki ya zauna a wannan gida na tsawon kwanaki saba’in da ɗaya. Sannan daga baya aka tura shi zuwa wancan gari na Tula sakamakon tsama baki da masu rajin kare haqqin (human right) xan’suka yi, ta hanyar matsawa gwamnati kan cewa dole ta xauki matakin adalci na baiwa mai martaba sarki tare da qarin wasu biyu; sarakunan Akko da Yamaltu, ‘yancin walwala.

Ana cikin wannan yanayi ne, kwatsam a ranar 13 ga watan Agusta na shekarar 2013, sai Allah cikin ikonsa ya saka gwamnatin Gombe, ƙarƙashin Dr. Ibrahim Hassan Ɗanƙwambo, Talban Gombe, ta yanke shawarar maido da mai martaba sarki gida kuma kan karagar mulkinsa, bayan ta sauke sarkin da gwamnatin Mohammed Ɗanjuma Goje ta ɗora, wato Alhaji Adamu Haruna Yakubu.

Saboda haka tun daga waccar rana ta 13 ga watan Agustan shekarar 2013, har zuwa yau ɗinan (2017), mai martaba sarki, Alhaji Muhammadu Seyoji Ahmad shi ke kan wannan kujera ta sarautar Pindiga.

Wasu Muƙaman da ya Riƙe

  1. Tun lokacin da mai martaba sarki yake kan kujerar hakimcin Pindiga, shi mamba ne a masarautar Gombe (Member, Gombe Emirate Council). Daga 1984 zuwa 2000.
  2. Darakta na kamfani roba na Arewa (Director Arewa Ceramic Industry, Misau) da ke Misau. Daga shekarar 1990 zuwa 1993.
  3. Mamba na kwamatin daraktoci (member directors committee for family support programme) na shirin tallafawa iyali na qasa, reshen jahar Bauchi, daga baya kuma ya koma na jahar Gombe. Ya riqe wannan muqami har zuwa shekarar 1994.
  4. Sannan ya tava zama Mamba na kwamitin gudanarwa (Member Governing Council University of Port-Harcout) na jami’ar Fatakwal daga 1997 zuwa 2000.
  5. Bayan zamowarsa sarkin yanka a shekarar 2000, ya zama mamba a majalisar sarakuna ta jahar Gombe.


Hatimin Mai Martaba Sarkin Pindiga

Iyali

Mai Martaba Sarki ya zuwa lokacin da aka rubuta wannan tarihi nasa yana da mata uku da ‘ya’ya goma sha bakwai.

Manazarta:


Northen Nigerian Publishing Company. (1970). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company, Zariya – Najeriya.

Okunna, E da Gausa, S. (2014). Adapting the Jukun Traditional Symbols for Textile Design and Production. Mgbakoigba: Journal of African Studies. Vol. 3. July, 2014

Tattaunawa da Mai Martaba Sarkin Pindiga, Alhaji Muhammad Sayoji Ahmad a ranar 13/02/2017 a Pindiga, Fadar Masarautar Pindiga.

Tattaunawa da Galadiman Pindiga, Alhaji Gambo Garba, a Gidansa da ke Gombe, a ranar 13/02/2017.Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub