Farfesa Yusuf M. Adam; Ganuwar Birnin Kano

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ganuwar Birnin Kano: Matsayinta a Tarihin Wayewar Kan Bahaushe


Farfesa Yusuf M. Adamu
Geography Department, Bayero University, Kano.
(yusufadamu@gmail.com)
Kano, Nigeria
© 2001


Tsakure

Ko’ina mutum ya kewaya a birnin Kano yanzu zai lura da wani abu guda da mamaye birnin a lokuna da lunguna. watau shaguna. Kano ta zama ko’ina shago. Kila a iya cewa ci-gaban harkokin kasuwanci ne suka kawo haka, tunda Kano cibiyar kasuwanci ce tun shekaru aru-aru. Ba za a ki hakan ba. Za a kuma lura da cewa a halin yanzu mafi yawancin masana’antun dake Kano a rufe suke, saboda haka a halin da muke ciki yanzu ba na kera abubuwa a Kano kamar yadda ake yi a da, amma ana ta gina shagunan sayar da kayayyakin da ake kerawa a Legas da Onicha. Akan yi wa Kano kirari iri-iri ciki har da cibiyar kasuwanci, cibiyar addinin da al’adu ko ace gari ba Kano ba dajin Allah, yaro ko da me ka zo an fika. I, babu shakka Kano gari ne mai tsawon tarihi kuma wadanda suka gina Birnin Kano shekara da shekaru ba ragwaye ba ne ba kuma mutane ne masu son zuciya da hadama da kuma rashin kishi ba. Mutane ne hazikai, masu kishin birnin Kano da son kyautata bayansu. A yadda na san mutanen Kano ‘yan shekaru kadan da suka wuce, a halin yanzu sun zama kanawawa ba kanawa ba domin kuwa Kano ba ta ransu. Abin da ke ransu abin da zuciyarsu ke so. Duk wannan shimfida ce na ke yi dangane da yadda aka sa ido ganuwar birnin Kano ta zagwanye ta lalace ake kuma kokarin shareta daga doron kasa duk da irin kimbin tarihin da ta ke da shi.Saboda haka, za a lura da wani abu guda, an kusa share Ganuwar Birnin Kano daga doron kasa. Wannan shi ya fi damuna matuka gaya.

Latsa nan ka Juyi Takarda


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub