Gudummawar Harshe - Farfesa Salisu A. Yakasai

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gudummawar Harshe da Al'ada ga Bunƙasa Tattalin Arziƙi da Zaman Lafiya da kuma Ci gaban Al'umma Mai Ɗorewa


Farfesa Salisu Ahmad Yakasai
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
syakasai2013@gmail.com
(+234) 08035073537

Maƙalar da aka gabatar a taron Al'adun Hausa na Ƙasa da Ƙasa na Burkina Faso TAHAKA (karo na biyu), a Ouagadougou – Burkina- Faso, daga ranar 7th – 11th ga watan Disamba na 2018.


Tsakure

Waiwayen tarihin irin rawar da harshe da al'ada suke takawa ga ci gaba mai ɗorewa, lamari ne da aka ayyana shekarun 1980 da kuma farkon 1990 a matsayin wani zango na baiwa mutane dama ta bayar da gudummawarsu a wajen ayyukan ci gaban al'umma. Taron duniya na Mexico a 1992 akan matsayin harshe da al'ada, ya jaddada nasarar samuwar ci gaban al'umma domin amfanin kansu. Da tafiya ta yi tafiya, sai hukumar raya ilimi da kimiyya da kuma al'adu ta Majalisar [inkin Duniya (UNESCO) ta ƙaddamar da bukin shekara goma (1988-1998) na ci gaban harshe da al'ada a duniya. Sakamakon wannan gangami ne ya haifar da tanadin wasu ma'aunai na ci gaban rayuwar al'ummar duniya. A shekara ta 1990 kuma sai hukumar raya ƙasashe ta Majalisar [inkin Duniya (UNDP) ta yi amfani da waɗancan ma'aunai ta wallafa rahoton irin ci gaban da ake samu. Haka dai lamarin ya ci gaba inda a shekarun (1992 -1996), hukumar inganta harshe da al'ada da kuma ci gaban al'umma ta Majalisar [inkin Duniya ta shirya rahoto akan yadda za a faɗaɗa ƙumshiyar al'adun al'umma.

Nan take taron ƙarawa juna ilimi na gwamnatocin ƙasashe da aka yi a Stockholm a 1998 ya amince da yalwata hurumin harshe da al'ada ga ci gaban al'umma. Daga nan kuma sai wani taron ƙarawa juna ilimi na haɗin gwiwa tsakanin hukumar UNESCO da Bankin Duniya a 1999 akan matsayin al'ada ga bunƙasa tattalin arziƙi. Sai kuma a 2001 da hukumar UNESCO ta ayyana harshe da al'ada a matsayin ƙashin bayan tattalin arziƙi da zamantakewar al'umma. Da shekara ta 2005 ta zo sai UNESCO ta tanadi matakai na kariya da na bunƙasa harshe da al'ada domin ci gaba mai ɗorewa. A wannan maƙala za mu yi tsokaci ne dangane da gudummawar harshe da al'ada ga bunƙasa tattalin arziƙi da zaman lafiya da kuma ci gaba mai ɗorewa. A sashe na farko da na ƙarshe, jawabin gabatarwa da kuma na kammalawa ne. Sashe na biyu ya kalli irin dangantakar da ke akwai ne tsakanin harshe da al'ada. Daga nan kuma sai sashe na uku inda muka kalli harshe da al'ada a matsayin madubin al'umma. A sashe na huɗu kuma muka taskace irin rawar da harshe da al'ada suke takawa wajen bunƙasa tattalin arziƙi da kuma kawo zaman lafiya mai ɗorewa ga al'umma.

Latsa nan ka Juyi Takarda


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub