Ƙasar Zamfara a Bakin Makaɗan Baka 1900-2000

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙasar Zamfara a Bakin Makaɗan ...

Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
08149388452, 08091503592
birninbagaji4040@gmail.com


Tsakure

Daula ta ƙunshi yanki na ƙasa da kuma ƙarfin mulkin da shugabannin wannan yanki suka gabatar a tsawon zamunna. Daular Zamfara ta yi tashe fiye da shekaru Ɗari uku (300) da suka shuɗe. Binciken wannan maƙala zai bi tarihin da wannan daular  ta samu daga lokaci zuwa lokaci saboda dalilai daban-daban da za a tattauna su a cikin wannan tsokaci. An bi silalen zaren tunanin makaɗan baka wajen ayyana tsawo da faɗin yanki, da kuma ƙarfin da Daular take da shi ta fuskar mulki a cikin waƙoƙinsu. Bayan saurare da taskacewa a lokacin nazarin waƙoƙin, an tattauna da tsoffin sani na tarihin daular. Ra’in Sauye-sauye na Hauhawar Ci gaba ne aka ɗora tsarin wannan aiki a kai. Fasalin wannan tsokaci zai haɗa har da ganin yadda tsarin ƙasa yake a da ta fuskar mulki da wurin zama, da kuma yadda ya kasance a yanzu. Ƙirƙirar jihohin da gwamnatoci suka yin a daga cikin dalilan da aka fahimci sun kawo sauyin da aka samu.  Bincike ya fahimtar da wannan aiki cewa canjin zamani na mulki da ƙarfin tattalin arzikin ƙasa ta fuskoki da dama, shi ne sakamakon kasancewar Daular a halin da take a yanzu. Makaɗan baka sun zama rumbu na adana wannan tarihin da maƙala ta ginu a kai.

Latsa nan ka Juyi Takarda


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub