Me ka ke nema?


Shafin Farko

Atuma Ɗan Dakauta 1452 Miladiyya


Gabatarwa

Atuma ɗan Dakauta shi ne sarki na goma sha takwas a jerin sarakunan Kano.  Shi ma kamar mahaifinsa, sarautarsa bata tsawaita ba. Bayan an naɗa shi da kwana huɗu sai Galadiman Kano na wancan lokaci ya tubure, ya tattara masu zaɓen sarki a gidansa ya raɗa musu cewa gaskiya sun yi zaɓen-tumun-dare. Dan kuwa sun zaɓo sarkin da bai san inda ya sa gaba ba, shi a nasa tunanin yana ganin kamata ya yi a ce Wamban Kano malam Yakubu ya kamata a naɗa. A nan jama’a suka rabu gida biyu. Wasu suka yarda da shi wasu kuma suka ƙi. Daga wannan rana abubuwa suka cukurkuɗe har aka yi tsawon kwana bakwai a wannan hali. Saboda haka dole ta sa aka tuɓe Sarki a Tuma.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub