Me ka ke nema?


Shafin Farko

Dawuda Abasama Ɗan Yakufu 1565 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Dawuda shi ne sarki na ishirin da huɗu a jerin sarakunan Kano. Bayan da Galadima Sarkatunya ya kashe Gwalle, sai ya naɗa Dawuda ɗan Sarki Yakufu, tunda shi Sarki Yakufu ya ƙi yarda ya koma. Shima kamar mahaifin nasa, sarautarsa bata yi tsawo ba. Ya zauna a gadon mulki na tsawon wata ɗaya da kwana ishirin kacal, aka tuɓe shi. Bayan an tuɓe shi sai ya tarkata ‘yan’uwansa ciki hard a shaƙiƙiyarsa Tabuduru, da sauransu suka rankaya zuwa Kwarmashe.  

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub