Shafin Farko

Soyaƙi Ɗan Shekarau 652 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Soyaƙi shi ne sarki na talatin da uku a jerin sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Fatsumatu kaamr yadda aka ambata. Watansa uku kacal a kan karagar mulkin Kano aka tuɓe shi. Bayan tuɓe shi wata ‘yar tarzomar yaƙi ta so ta tashi tsakanin mutanen Kano ƙarƙashin jagorancin Madawakin Kano. An ginawa Sarki Soyaƙi gida a Dukurawa ya tare a can.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.