Shafin Farko

Yakubu Ɗan Abdullahi Barja 1452 – 1463 M


Gabatarwa

Sarki Yakubu ɗan Barja shi ne sarki na goma sha tara a jerin sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Tasafe. Sarki Yakubu sarki ne managarci. Sarki Yakubu ya zauna a gidansa da ke Jujin ‘Yan Labu.

A zamanin wannan sarki ƙasar Kano ta samu gagarumin ci gaba ta fuskacin ƙaruwar arziƙi da kuma Ilimi.

A zamaninsa ne Fulani suka zo ƙasar Kano daga Malle (wato ƙasar Mali kenan a yau). Zuwan waɗannan Fulani shi ne farkon samuwar ilimin fannin Tauhidi da Lugga a Kano. Sai dai dama tun kafin zuwansu a akwai fannonin Ilimi kamar Al-Ƙur’ani, Fiƙihu, da Hadisi.

Ta fannin kasuwanci kuwa a wannan zamani nasa ne cikin shekarar 1453 wasu Larabawa daga Ƙasar Gadamas suka samu isowa Kano. Da suka iso sai suka wuce fadar Sarki, Shamaki ya yi musu iso suka bayyana cewa su fatake ne suna son yin kasuwanci a garin Kano. Da sarki ya ji haka ya yi maraba da su kuma ya sa aka nuna musu wani fili da ke unguwar Garke, wato Dandali kenan. Bayan sun gina gidaje sun zauna sai Kanawa suka riƙa ƙiran wannan guri da Dandalin Turawa saboda kasancewar fatar Larabawa Ja ce, sannan kuma jama’ar wancan lokaci ba sa iya banbacewa tsakanin Balarabe da Bature. Su kawai duk wata jar fata ko fara sunanta Bature. Wannan shi ne dalili. Duba Gwangwazo (2003).

Sarki Yakubu ya mulki Kano tsawon shekaru goma sha biyu. Ya rasu yana da shekaru hamsin da biyar a duniya. Ya rasu bayan gajeruwar jinya.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.