Me ka ke nema?


Shafin Farko

Bugayya ɗan Tsamiya (1385 – 1390 Miladiyya)


Gabatarwa

Bugayya shi ne sarki na goma sha biyu a jerin sarakunan Kano.  Sunansa na asali shi ne Muhammadu. Shi ne sarkin da ya kore sauran Maguzawa daga gidin dutsen Fanisau. Ya ce da su su watse kuma suka bi. Saboda haka ya zauna a ƙasarsa salim-alim ba wani yaƙi. Ya ci gaba da karɓar haraji a hannun jama’a. ya mulki Kano na tsawon shekaru biyar.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub