Gina Kofofin Kano

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gina Ƙofofin Kano


Ginin Ƙofofin Kano Karo na Farko

Sarkin Kano na uku Usman Gijimasu ɗan Warisi, shi ya fara wannan aiki na gina ganuwa da kuma ƙofofin Kano. Ya samu nasarar kewaye Kano da Ganuwa a tsawon shekaru goma sha takwas daga shekarar 1112 zuwa 1130. Ƙofofin da ya gina su ne:

  1. Ƙofar Kansakali (1112)
  2. Ƙofar Waika (1112)
  3. Ƙofar Ɗanƙwai/Ƙofar Dawanau (1112)
  4. Ƙofar Lunkui/Ƙofar Ruwa (1116)
  5. Ƙofar Mazugal (1118)
  6. Ƙofar Adama/Ƙofar Dagaci/Ƙofar Wambai (1118)
  7. Ƙofar Hanga (1118)
  8. Ƙofar Gyarta Wasa (1118)
  9. Ƙofar Kawaye (1118)
  10. Ƙofar Kawankari
  11. Ƙofar Barbushe/Ƙofar Bai (1124)
  12. Ƙofar Kadaɓa (1125)
  13. Ƙofar Shinkafa (1125)
  14. Ƙofar Ɓulɓula (1130)

Ginin Ƙofofin Kano Karo na Biyu

Bayan wani dogon zamani, sai aka sake samun wani sarki daga sarakunan Kano mai suna Muhammadu Rumfa, wanda shi kuma ya himmatu a cikin shekarar da ya hau mulki, ya sake faɗaɗa birnin Kano. Saboda haka dole ya rushe wannan gini na ganuwa da kuma wasu daga cikin Ƙofofin. Ya gaji Ƙofofo Goma sha huɗu, sai ya rushe takwas daga cikinsu, ya kuma gina wasu guda huɗu sababbi. Saboda haka sai adadin Ƙofofi ya koma goma daidai.

Ƙofofin da ya rushe su ne:

  1. Ƙofar Hanga (1118)
  2. Ƙofar Barbushe/Ƙofar Bai (1124)
  3. Ƙofar Gyarta Wasa (1118) 
  4. Ƙofar Kadaɓa (1125)
  5. Ƙofar Kawaye (1118) 
  6. Ƙofar Shinkafa (1125)
  7. ofar Kawankari
  8. Ƙofar Ɓulɓula (1130)

Waɗanda kuma ya bari su ne:

  1. Ƙofar Kansakali (1112)
  2. Ƙofar Waika (1112)
  3. Ƙofar Ɗanƙwai/Ƙofar Dawanau (1112)
  4. Ƙofar Lunkui/Ƙofar Ruwa (1116)
  5. Ƙofar Mazugal (1118)
  6. Ƙofar Adama/Ƙofar Dagaci/Ƙofar Wambai (1118)

Ya kuma gina waɗannan:

  1. Ƙofar Fagge/ Ƙofar Mata (1463)
  2. Ƙofar Kudu/Ƙofar Ɗan’agundi (1472)
  3. Ƙofar Kawaye/Ƙofar Nasarawa (1466)
  4. Ƙofar Dogo/Ƙofar Na’isa  

Ginin Ganuwa da Ƙofofin Kano Karo na Uku

Sarki Muhammadu Nazaki Ɗan Zaki shi ya yi wannan aiki. Ya kuma yi hakan ne dan ya sake faɗaɗa ƙwaryar birnin Kano. Ya yi wannan aiki ne kuma a tsawon shekaru uku. Ya kammala aikin a cikin shekarar 1621. Ya gina ƙofofi guda uku kamar haka:

  1. Ƙofar Gadon Ƙaya.
  2. Ƙofar Dukawuya.
  3. Ƙofar Kabuga.

Ginin Ƙofofi karo na Huɗu

Haka nan bayan wani dogon zamani sai aka samu wani sarki mai suna Abdullahi Bayero. Shi ma ya sake bada tasa gudunmawa wajen ƙara yawan waɗannan ƙofofi, sakamakon buƙatar yin haka da ke akwai. Ya ƙara ƙofofi uku kamar haka:

  1. Ƙofar Famfo (1934).
  2. Sabuwar Ƙofar Rumafa (1935).
  3. Sabuwar Ƙofar Alasan (1937).

Saboda haka kenan Kano tana da ƙofofi goma shida a jimillance kamar haka:

  1. Ƙofar Kansakali (1112)
  2. Ƙofar Waika (1112)
  3. Ƙofar Ɗanƙwai/Ƙofar Dawanau (1112)
  4. Ƙofar Lunkui/Ƙofar Ruwa (1116)
  5. Ƙofar Mazugal (1118)
  6. Ƙofar Adama/Ƙofar Dagaci/Ƙofar Wambai (1118)
  7. Ƙofar Fagge/ Ƙofar Mata (1463)
  8. Ƙofar Kudu/Ƙofar Ɗan’agundi (1472)
  9. Ƙofar Kawaye/Ƙofar Nasarawa (1466)
  10. Ƙofar Dogo/Ƙofar Na’isa  (1470)
  11. Ƙofar Gadon Ƙaya (1619).
  12. Ƙofar Dukawuya (1916).
  13. Ƙofar Kabuga (1621).
  14. Ƙofar Famfo (1934).
  15. Sabuwar Ƙofar Rumafa/Sabuwar Ƙofa(1935).
  16. Sabuwar Ƙofar Alasan (1937).
  17. /ol>

    Manazarta:


    Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

    Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Savannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

    Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Eɗecutive Governor, Government House, Kano.

    Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

    Ɗanyaro M.M. (1997). Kano State 30 Years of Statehood (1967 – 1997).

    Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

    Gwadabe M.M. (2008). Land, Labour and Taɗation in Kano Native Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

    Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

    Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

    Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.

    Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.

    Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

    Northern Nigerian Publishing Company Ltd. (1979). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Gaskiya Corporation, Zaria.

    Obii-Mbta R.A. (1994). Alhaji Ado Bayero and the Rorayl Court of Kano. Carpricorn 25 Limited. Kano-Nigeria.

    Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Coy, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

    William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub