Me ka ke nema?


Shafin Farko

Guguwa Ɗan Gijimasu 1247 – 1290 Miladiyya


Gabatarwa

Wannan shi ne sarki na bakwai a jerin sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Munsada. Sarki Guguwa ɗa ne ga sarkin Kano Gijimasu, shi kuma ɗan sarkin Kano Warisi, shi kuma ɗan Sarki Bagauda.

Sarki Guguwa mutum ne mai karimci. Ya kasance mai kyautatawa ga talakawansa. Shi ne sarkin da ya samu lalura ta makanta a lokacin da ya ke kan kujerar mulki. Ya mulki Kano na tsawon shekaru arba’in da huɗu. Shekaru ishirin da biyu yana gani, ishirin da biyu kuma yana makance. Daga baya aka cire shi aka maye gurbinsa da waninsa.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub