Daular Damagaran

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Daular Damagaran


Gabatarwa

Daular Damagaran, wata ƙaƙƙarfar tsohuwar daula ce kafin zuwan Turawa wadda ke da helikwata a garin Zindar wadda a yanzu ta ke kudancin ƙasar Nijar. An kafa wannan daula a shekarar 1731 a ruwayar Wikipedia (2017).

Daular ta taɓa zama a matsayin gudunma a ƙarƙashin makekeyiar daular Barno. Amma daga baya ta ɓalle tare kuma da ƙwace sauran gudunmomin da ke Yammacin daular waɗanda suke maƙwabtaka da ita.

Malam Yunusa, wanda aka fi sani da Sarki Malam, shi ne ya taso daga Yamen, wanda kuma asali daga Makka yake, kuma an turo shi ne ya zo ya yaɗa Musulunci. Da ya iso daular Barno, sai ya je gurin Shehun Barno na wancan lokacin ya sanar da shi. Sai shi Shehun ya nuna masa cewa ai tuni addinin Musulunci ya kafu a wannann daula, sai dai ya ƙara gaba yammaci.

Daga nan sai malam Yunus ya gangaro yamma yana ta tafiya har sai da ya iso garin Difa. Sannan ya ɗora tafiya zuwa Kulum-Farda. Sai ya yada zangon farko a Damagaran ta ƙaya, inda ya zauna a garin Geza, ya kafa makaranta. Ya kasance yana karantar da yara da rana, da daddare kuma ya yi wa’azi.

Manazarta


Wikipedia (2017). Zinder. An ciro a shekarar 2017 daga shafin, https://en.wikipedia.org/wiki/Zinder

Wikipedia (2017). Sultanate of Damagaram. An ciro a shekarar 2017 daga shafin, https://en.wikipedia.org/wiki/Sultanate_of_Damagaram

Tattaunawa da Alhaji Laminu, Magajin Gari (Kwatankwacin shugaban ƙaramar hukuma a Najeriya) Shiyyar Birnin Zinder a ranar 24/07/2017 a ofishinsa da ke garin Zinder a Nijar.

Tattaunaw da Wakilin Tarihi na fadar masarautar Damagaran a ranakun 24-30/07/2017 a fadar Masarautar Damagaran da ke birnin Zinder a Nijar.



Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub