Shafin Farko

Muhammadu Abbas 1903 – 1919 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Muhammadu Abbas shi ne sarki na 51 a jerin sarakunan Kano, sannan kuma sarki na 9 a jerin sarakunan Fulani, har wayau kuma shi ne sarki na farko da Turawa suka fara naɗawa.
Sarki Muhammadu Abbas mutum ne jarumi, kuma mai faɗa ba fasawa ko kuma ana iya cewa mutum ne kaifi ɗaya. Ya kasance sarki mai haƙuri da jama’arsa.

Sarki Abbas ya yi mulki tare da Turawa, saboda haka hakimansa suka samu dama ta dalilin haƙurinsa da kawaicinsa suna iya yin magana kai tsaye da Turawa, har sai da ta kai jallin munafurci ya fara gudana a tsakanin Turawannan da wasu daga cikin hakiman sarki Abbas. Irin wannan lamari na tsaka da faruwa sai Allah ya kawo wani Bature mai suna Mr. Temple., shi ya takawa wannan al’ada burki. Ya samar da kyakkyawan tsari, ya yankawa sarakuna da sauran ma’aika albashi.

A zamanin sarki Abbas ne aka yi wani gagarumin taron sarakuna, gabas da yamma, kudu da arewa a cikin shekarar 1912. A zamanin sarki Abbas ne aka gina wasu kasuwanni a Kano. Sannan kuma a zamaninsa ne a ciki shekarar 1910 aka gina wata makaranta a cikin Nassarawa wacce a yanzu ta koma gidan Ɗanhausa.

Sarki Muhammadu Abbas ya yi sarautar Kano ta tsawon shekara goma sha shida. Ya rasu a shekarar 1919. An binne shi a gidansa da ke Nassarawa.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.