Sarkin Katsina Muhammadu Kabir Usman

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Alhaji Muhammadu Kabir Usman


Gabatarwa

Alhaji Muhammadu Kabir Usman, shi ne sarki na arba’in da tara a jerin sarakunan Katsina, sannan kuma sarki na goma a jerin sarakunan Fulani, kuma sarki na uku a gidan Sulluɓawa.

Shi Alhaji Muhammadu Kabir Usman mutum ne masanin Al-ƙur’ani da kuma ilimin zamani. An ruwaito cewa Alhaji Muhammadu Kabir ya rubuta Al-ƙur’ani da hannunsa. Haka na iya tabbatuwa daga kirarin da ake yi masa na “Limamin Sarakuna ɗan Shehu”.

Haihuwa

An haifi Alhaji Muhammadu Kabir Usman a watan Janairun shekarar 1928. Shi ɗa ne ga sarkin Katsina Usman Nagogo, wanda shi kuma ɗa ne ga sarkin Katsina Muhammadu Dikko. Kenan, Alhaji Muhammadu Kabir Usman ya zama ɗan sarki jikan sarki. Sunan mahaifiyarsa Aminatu.

Karatu

Alhaji Muhammadu Kabir Usman ya fara karatun Al-ƙur’ani tun yana ƙarami a hannun malaminsa malam Muhammadu Abdullahi a cikin fadar Katsina. Daga baya, Alhaji Muhammadu Kabir ya shiga wata makarantar Al-ƙur’ani da ke unguwar Tsamiya, wacce ke daf da fadar ta Katsina.

Bayan ya kai shekaru goma sha huɗu a duniya, an saka Alhaji Muhammadu Kabir Usman a makarantar ‘Katsina Middle School’. Sannan kuma ya samu shiga makarantar ‘yansanda ta Kaduna (Nigeria Police College, Kaduna) inda ya samu horo na shekara guda bayan zamowarsa ɗansanda a Hukumar Gargajiya ta Katsina (Katsina Native uthority).

Sannan kuma a shekarar 1953 ya je Legas dan yin kwas ɗin , ‘Criminal Investigation’ haka nan kuma ya je ‘Police College, London’ dan faɗaɗa iliminsa a wannan fanni na binciken manyan laifuffuka.

Gogayyar Aiki

Alhaji Muhammad Kabir Usman. A shekarar 1947 ya samu shiga Rundunar ‘Yansadan Hukumar Gargajiya ta Katsina (Katsina Native Authority Police), sannan kuma an ɗaukaka darajarsa daga baya zuwa Wakilin Doka na Katsina. Haka nan kuma a shekarar 1957,  aka yi masa muƙamin ‘Native Authority Councilor in Charge of Police, prison and the department of urban water supply’.

A shekarar 1957 aka yi masa muƙamin Magajin Gari amma na riƙon ƙwarya. Wannan muƙamin nasa na Magajin Gari sannan kuma Hakimin Birni da Kewaye an tabbatar masa da shi a shekarar 1963. A dai wannan shekarar ta 1963 aka zaɓe shi a matsayin ‘member of the House of Assembly, Kaduna’. A shekarar 1965 ya zama ‘parliamentary secretary’ na firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello.

Zamowarsa Sarki

A watan mayu na shekarar 1981, masu zaɓen sarkin Katsina suka zaɓi Alhaji Muhammadu Kabir Usman a matsayin sarkin Katsina wanda zai gaji Mahaifinsa Alhaji Usman Nagogo. Amma wannan zaɓe nasu ya sadu da tangarɗa da ofishin zaɓaɓɓen gwamnan Kaduna na wannan Lokacin Alhaji Abdulƙadir Balarabe Musa wanda yaƙi amincewa da naɗin har sai da ‘yanmajalisarsa suka tsige shi aka tabbatar da Alhaji Abba Musa Rimi a matsayin gwamnan Kaduna shi kuma ya amincen da naɗin nasa aka kuma yi bikin naɗin sarautarsa a filin Kangiwa da ke garin Katsina.

Gudunmawar da ya Bada

Alhaji Muhammad Kabir Usman ya bada gagarumar gudunmawa a lokacin mulkinsa a matsayin sarkin Katsina. Shi ne mutumin da saboda kyakkyawar mu’amalarsa da jama’a ake yi masa kallon mutumin talakawa.

A zamaninsa aka ƙirƙiri wasu sababbin hakimai a masarautar Katsina. Sannan kuma a zamaninsa aka yi Jahar Katsina.

Sannan Alhaji Muhammadu Kabir Usman shi ne ya rushe masallacin Dutsi, sannan kuma ya gina babban masallacin Juma’a na Katsina, wanda har yanzu da shi ake amfani a matsayin babban masallacin Juma’a na Katsina.

Rasuwarsa

Alhaji Muhammadu Kabir Usman ya rasu a ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2008 bayan doguwar rashin lafiyar da ya daɗe yana fama da ita. Wannan rashin lafiya har ta kai shi da fita ƙasashen waje neman maganin tun kafin rasuwar tasa. Ya yi sarautar Katsina ta tsawon shekaru 27.

Manazarta:


Ingawa T.L. (2006). Katsina a History of an Ancient City. Hamdala Prinitng and Publishing.

Lugga S.A. (2004). Katsina College. Lugga Press, Katsina

Mamman M. (2015). Tarihin Unguwannin Birnin Kastina. Ahmadu Bello Uniɓeristy Press Ltd, Samaru, Zaria-Nigeria.

Michael D. (2008). HRH, Alhaji (Dr) Muhammadu Kabir Usman, Emir of Katsina. A ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://naijapositive.myfastforum.org/viewtopic.php ?t=2867&start=0

Wikipedia (2016). Muhammadu Kabir Usman. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Muhammadu_Kabir_ Usman


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub